Tun a shekarar 1914 da turawan mulkin mallaka suka hada kudancin da arewacin wannan kasa da suka rada wa suna Nijeriya talakawa ke bada gudunmawa mafi tsoka wajen cigaban wannan kasar. Gudunmawar su ta kasance ta hanyoyin biyan harajai ,aiki kusan na bauta da kuma rayuwar su a lokacin da Nijeriya ta fuskanci barazanar wargajewa.
A lokacin mulkin mallaka turawan Ingila sun bautar da talaka ta hanyar samar da amfanin gona kamar dalar gyada ta Kano,noman auduga ,koko ,manja ,rogo da sauran su. Turawan mulkin mallaka suke sawa albarkatun gonar da talakawa suka noma farashi maimakon wanda ya noma ya sawa kayan sa farashi domin jigila zuwa kasar Birtaniya.Talakawa su suka yi aikin gina titin dogo domin samar da sifirin da za’ayi dakon kaya zuwa bakin teku. Sukan biya haraji kan komai daga kawunan su, iyalan su da abubuwan da suka mallaka kamar dabbobi ,gonaki da kayayyakin da suka mallaka . Wannan zalunci ya samu tabbata ne tare da hadin kan masarautun gargajiya da yan koren turawa da sunan mulkin cin gashin kai.
Lokacin da Nijeriya ta samu yancin mulkin kai a shekarar 1960 , talakawa na ta murnan cewa al’amura zasu canza tunda yan’uwan su bakake zasu kasance masu gudanar da harkokin mulkin wannan kasa. Amma mai talakawa suka samu sakamako game da wahalar da zalunci da suka fuskanta a hannun turawan mulkin mallaka ? Sabbin shugabanni da aka samu maimakon su maida hankali su ga hada kan kasa domin cin gajiyar dinbin arzikin albarkatun kasa da Allah yayi wa wannan kasar baiwa da ita sai ya kasance sun maida hankalin su gun kokuwar dafe madafan iko da samun girma wanda ya kaisu da fara haza harsashin kabilanci , son kai , bangaranci da nuna banbancin addini.
Kabilanci da bangaranci ya kai matuka a shekarar 1966 da wasu sojojin kabilar Ibo suka gagoraci juyin mulkin da ya hambarar da gwamnatin jamhuriya ta farko wanda sakamakon haka ya kai Nijeriya da fadawa cikin yakin basasa wanda ya janyo halakar dubban talakawa daga kowane bangare na Nijeriya. Jagororin wannan yaki da suka fuskanci shan kasa suka tsere zuwa kasashen waje suka bar talakawan da suka ingiza kuma a yau suna raye suna holewar su.
Talakawan Nijeriya basu da abokane, masoya , mataimaka da masu tausaya masu na hakika. Masu mulki sojojin su da farar hula sun kasance masu hada kai da masarautun gargajiya , malaman addini da manyan yan kasuwa domin kara jefa talaka cikin wahala ta hanyoyin mara wa manufofin gwamnati daka gallazawa talaka kamar janye tallafin gwamnati a abubuwan more rayuwa da karin kudin man fetur da gangoginsa .An bar talaka cikin bakar wahala da kuncin rayuwa kuma duk yayin da suka so su motsa domin neman wa kansu yaci sai masarautu da maluman addini su shiga dakufar da talakawar da cewa Allah ya la’anci mai tada fitina. Basa sanar da gwamnati cewa lallai talakawa na cikin wahala dan haka gwamnati ta taimaka ta janye manufofin ta da zai jefa talaka cikin karin wahala da kunci .
Koda yaushe yan siyasa da maluman addini sun kasance cikin ingiza talakawa suyi ta rikici a tsakanin su da sunan addini. Dubban talakawa sun rasa rayuwar su a sakamakon fadace-fadace da sunan addini a jihohi da dama na kasar nan. Yan siyasa da malaman addini dake ingiza talakawa rikici a tsakanin su basa taba tura yayan su su kasance a sawun gaba yayin irin wadanan tashe-tashen hankula.
Ana kuma amfani da kabilanci wajen ingiza talakawa su kashe junan su . Duk yayin da wasu masu fada aji suka rasa madafen iko sai su fake da zancen kabilanci da bangaran ci wajen kokarin samu damar fada aji . Rigin-gimun kabilanci yayi sanadiyar dubban talakawa sun rasa rayukan su tare da maida wasu dubbai sun zama masu gudun hijira a cikin kasar su ta haihuwa.
Masu mulki da yan koren su sun kasance masu fahimtar juna a kamfanonin su na hadin gwiwa inda zaka same su tare ba tare da banbancin kabila, bangare ko addini ba . Sun kasance masu manufa daya na tara dukiya ta kowace hanya . Basa korafi sai yayin da suka kasa cimma manufar su na juya da sarrafa dukiyar kasa ko ta jiha.
A bangar siyasa , magudi da murda-murdan zabe da talakawa ake amfani dasu ana basu dan abunda ba zai ishe su kashewa ba tun kafin a rantsar da wadanda suka ci gajiyar magudin zabe.
A yaushe talakawan Nijeriya zasu fahimci cewa suna da makiya guda? A yaushe talakawa zasu fahimci cewa ana amfani da su ne dan biyan bukatar wani ko wasu mutane dake kokarin cimma burin su suna fakewa da sunan kabilanci , bangaranci da addini? A yaushe zasu fahimci cewa yayin da wadannan mutane ke farfajiyar mulki basa zancen an danne kabilarsu , yankin su ko addinin su. Sai yayin da suka rasa madafan iko sai su shiga gwagwarmayar an danne yankin su, kabilarsu ko addinin su .
Yayin da yan’arewa ke mulkin wannan kasar wacce dama ta musamman talaka dan arewa yake samu daga gwamnati?A yanzu da dan kudu kuma bayarbe ke mulki wane dama ta musamman yan kudu da yarbawa ke samu daga gwamnati? Wane bangare ne na Nijeriya ba’a fama da talauci, rashin aikin yi, rashin ruwa , wuta , tituna masu kyau , rashin tsaro, kyawawan muhalli da sace dukiyoyin su?
Masu mulki da yan koren su a gidajen sarautu da maluman addini sun kasance da kamanni guda inda zaka same su suna zaune a kebabun unguwanni da manyan gidaje masu jan rufi , suna tafiya a jerin gwanon motoci masu tsada tare da jibga-jibgan masu gadin su. Wasu cikin su har sun yi kiba da tumbi kamar mace mai cikin wata tara.
Lokaci yayi da talakawan Nijeriya zasu hada kansu ba tare da kyamar juna ba saboda banbancin addini , yanki da kabila domin samar wa kansu rayuwa mafi kyau da ingaci . In suka yarda aka cigaba da amfani dasu wajen raba kansu kan kan banbancin kabila , yanki da addini masu mulki da yan koren su zasu cigaba da azabtar da talaka da sace masu dukiyar kasa.
Fahimtar juna , girmama juna da ganin mutuncin juna shine abubuwan da talakawan Nijeriya suke bukata wajen cigaba da dorewar kasar mu Nijeriya. Kaddara ta riga ta hada mu mun zama yan kasa daya kuma wata kabila, ko yanki ko addini ba zata iya dorewa ita kadai ba ba tare da chudanya da yar’uwarta ba.
Hadin kai ke kawo karfi in kuma talakawan Nijeriya suka bari aka cigaba da raba kan su to wahalar yau kamar ta jiya zata tarar da yayan mu da zasu zo nan gaba, Fahimtar hadin kai da girmama juna shine zai ciyar da kasar mu gaba a cikin kasashen duniya.
Haza wassalam nine
Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com
Thursday, 17 May 2007
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment