Thursday 17 May 2007

Janar Babangida na cikin tsaka mai wuya

A shekara mai zuwa waton 2007 Nijeriya zata sami sabon shugaban kasa mai cikakken iko yayin da wa'adin shugaba Obasanjo zai kare. Cikin tsahun gaba -gaba na masu neman shugabancin Nijeriya a shekara ta 2007 shine tsohon shugaban mulkin soja Janar Ibrahim Babangida.
Tun lokacin da Babangida ya furta cewa zai tsaya takarar shugabancin wannan kasar masoyan sa da masu adawa dashi suke kai gwauro su kai mari kan dacewar sa ko a'a kan ya sake dawowa bisa kujerar mulkin wannan kasar.Ta bangaren gwamnati mai ci a yanzu manazartan harkokin siyasa suna ganin cewa bashi da goyon bayan shugaba Obasanjo saboda yadda gwamnatin sa take ta kokarin ganin tayi wa Babangida kofar raggo ta hanyar kama dan sa Mohammed Babangida kan tuhumar mallakar kashi ashirin da hudu na kamfanin wayar sadarwan globacom, da bincike kan shari'ar kashe marigayi Janar Mamman Vatsa , da bayyana rahoton Okigbo kan yadda kudade fiye da dala biliyan goma sha-biyu sukayi batan kai na raran man-fetur da aka samu lokacin yakin tekun fasha.
Masu goyon bayan Janar Babangida suna ganin cewa a lokacin sa ya samar da cigaba ta fannoni da dama kamar su hukumar samar da aikin yi (N.D.E),Bankin talakawa (People's Bank),hukumar kare haddura(FRSC),hukumar raya karkara (DEFRI),hukumar wayar da kan matasa (MAMSA)gina tagwayen hanyoyi kamar na Kaduna zuwa Kano,kafa jam'iyyu da basu kudaden tafiyar dasu,hukumar wayar da kan mata (Better Life) da sauran su .Suna ganin cewa in har Babangida ya sake dawowa bisa kujerar mulki to za'a sami cigaba fiye da wanda aka samu a lokacin da yake mulki irin na kama karya ta soja.Kuma suna ganin cewa inshi ya bata to a bashi dama yazo ya gyara.
Akwai masu ganin cewa kafin ma Babangida ya fito dan tsayawa takara ana da bukatar yayi wa Yan-Nijeriya cikakken bayanai game da irin rawar da gwamnatin sa ta taka wajen soke zaben June 12 , yadda akayi da sama da dala biliyan goma sha-biyu na rarar man fetur , kashe Dele Giwa ,hatsarin jirgin saman hakulas dauke da sojoji a legas, gaskiyar zancen yunkurin juyin mulkin marigayi Mamman Vatsa da kashe shi , shigar Nijeriya kungiyar O.I.C da maida huldan jakadanci da kasar Isra'ila, da kuma uwa uba karbo bashi daga bankin duniya wato I.M.F da daura Nijeriya bisa tafarkin S.A.P da ake ganin shi ya karya darajar naira ta kuma jefa Nijeriya a halin kakani-kanin da take ciki a yanzu.
Amma babban abun tambaya gashi Babangida da magoya bayan sa shine a yaushe shi janar din ya amince da kuma yarda da tsarin dimokaradiya?Domin a lokacin sa ya kawo tsare-tsaren da yayi wa dimokaradiya targade ko kuma ace ya karyata. A lokacinsa ne jam'iyyun N.R.C da S.D.P suka gudanar da zaben fidda gwani wanda Malam Adamu Ciroma a jam'iyyar N.R.C da marigayi Janar Shehu Musa Yar'aduwa ya lashe a jam'iyyar S.D.P sai kawai ba tare da wani muhimmin bayani ba ya rushe zaben nasu.
Haka ma Babangida yasa yan-siyasa da al'ummar kasa sake shiryawa da fitowa sabon zaben da aka tsara na shugaban kasa a inda Alhaji Bashir Tofa na jam'iyyar N.R.C da marigayi Cif M.K.O Abiola na jam'iyyar S.D.P suka tsaya takara . Ana cikin bada rahotannin sakamakon zaben kwatsam sai Babangida ya soke zaben ba tare da wani kwakwaran dalili ba. Rigingimun da suka biyo baya shi ya tilasta masa sauka kan mulki bada shiri ba bayan shekara takwas yana mulki.
Soke zaben June 12 ya jefa Nijeriya cikin wani yanayin rikici da tashin hankalin siyasar da tun yakin basasar Nijeriya ba'a taba fuskantar irin wannan yanayi ba. Tirjewan da kabilar Yar'bawa sukayi na an soke zaben da dan'uwan su ya dauki hanyar lashewa yasa a zaben 1999 aka barwa Yar'bawa su kadai suka tsaya takara waton Cif Olu Falae da Cif Olusegun Obasanjo. Sanin kowa ne yadda Janar Babangida ya taka rawa wajen ganin cewa Cif Obasanjo shi ya lashe zaben.
A shekara bakwai da Shugaba Obasanjo yayi yana mulki sau nawa Janar Babangida ya fito domin kare talakawa daga manufofin gwamnatin da suke takura talaka da jefa talakawa cikin halin ni yasu? Shin da yan-arewa suke ta koken cewa wannan gwamnatin na danne su Babangida ya fito ya samar masu sauki?
Janar Babangida ya shedawa Yan-Nijeriya cewa babu gudu babu ja da baya zai fito takarar neman Shugabacin kasa a zaben 2007 . Masu nazari kan harkokin siyasa nata tsokaci kan rawar da Janar din zai taka wanda zai iya kai shi ga samun nasara ko faduwar sa a zabe. Tun zangon farko na wa'adin Shugaba Obasanjo masoya da magoya bayan Babangida suke ta kira gareshi ya fito amma Janar din yayi bayanin cewa shi ba zaiyi takara da Shugaba Obasanjo ba. To yanzu da Shugaba Obasanjo ba zai tsaya zabe ba a shekarar 2007 kuma a yadda Yan-Nijeriya suke tsammani na cewa Shugaba Obasanjo zai rama wa kura aniyar ta sai gashi alamu suna ta nunawa cewa Obasanjo ba zai goya wa Babangida baya ba.
A wannan yanayin da Janar Babangida bashi da goyon bayan Shugaba Obasanjo ga yan takara biyu masu karfi da tasiri wato mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da Janar Muhammadu Buhari lallai Janar Babangida nada jan aiki wajen lashe zaben 2007 .
Ba shakka Janar Babangida nada tasirin gaske a siyasar wannan kasar da kuma masoya da mogoya baya masu yawa. Ya rage ga shi Janar din ya san yadda zai tallata kansa ga Yan-Nijeriya su mara masa baya domin sake samun damar dawowa ya mulki Nijeriya a tsarin dimokaradiya. Manufofin sa da zai aiwatar na iya sa Yan-Nijeriya su amince dashi ya kaiga ya lashe zaben 2007 .
Masoya da magoya bayan Janar Babangida har ila yau na bukatar cikakken bayani kan lallai zai fito takara ko a'a domin ga dukkanin alamu har yanzu yana jan kafa wajen tsunduma cikin harkokin siyasa da zai kaishi ga tsayawa takara. Kuma ga fitowar Janar Aliyu Gusau takarar shugaban kasa shima wanda ake ganin tare suke kuma in har da gaske Babangida zai fito to Janar Gusau ba zai tsaya takara ba.
Batun jam'iyyar da Janar Babangida zai tsaya ma har yanzu bai bayyana ba duk da cewa shi sannan dan jam'iyyar P.D.P ne. Takarar sai da gwani na jam'iyyar tasa da alamun tana yi masa kwarjini wanda yasa ya raba kafafuwansa a jam'iyyu masu dama. Koda yake jam'iyyar N.D.P ta rigaya ta bashi damar tsayawa a matsayin dan takaranta na shugaban kasa , amma ko jam'iyyar zata karbu har ta kaishi ga cimma burinsa to al'amurran siyasa kafin zaben 2007 kadai zai iya tabbatar da haka.
Wani abin murna da farin ciki shine cewa fitowar ire-iren su Janar Babangida na tabbatar da daurewar tsarin dimokaradiya a wannan kasa wanda mulkin soja ya ja mata tsaiko ga cigaba ta fanin siyasa , zamantakewa da bunkasar tattalin arzikin kasa .
Zaben 2007 ya zama kalubale ga Janar Babangida domin ya rigaya ya furta cewa lallai zai fito . Dole cikin abubuwa uku a sami daya , kodai yaki fitowa takara wanda zai tabbatar da zancen manazartan harkokin siyasa cewa Janar Babangida matsoraci ne a fagen siyasa na gwagwarmayan neman al'umma ta mara masa baya ya kaiga darewa kan kujerar mulkin Nijeriya a tsarin dimokaradiya. Nabiyu, in har ya fito takara aka kada shi a zaben to alkadarinsa ta karye a yadda al'umma suke ganin sa a wani dodon bango mai bada tsoro. Na uku , in ya fito takara har ya kaiga lashe zaben 2007 to ya tabbatar wa al'ummar Nijeriya da duniya gabaki daya cewa shine mutumin da yafi tasiri a siyasar wannan karni ba'a Nijeriya kadai ba har ga Afrika gabaki daya . Kuma wannan shi zai bashi babbar dama na gyara sunan sa a tarihin siyasar Nijeriya domin mutanen Nijeriya da dama suna ganin shine ya jefa Nijeriya a halin da ta tsinci kanta a ciki har yanzu.
Ina mai kira ga Janar Ibrahim Babangida da ya tsuduma cikin harkokin siyasar zama shugaban kasa a 2007 ba dan komai ba , dan wannan wata dama ce da zai fito yayi wa jama'ar Nijeriya kwararen bayanai da zasu gamsu kan cewa wasu abubuwan da auka faru yayin da yake kan mulkin Nijeriya alheri ne ga kasan.Kaman yadda Janar din yayi bayani da kansa a wata hira da sashen hausa na B.B.C lokacin yaki da tazarce cewa yan-majalisa su sani suna da ya'ya wanda in sukayi abunda jama'a basa so to zasu barwa ya'yan su abun fadi . Lallai tun Janar din nada rai da lafiyar sa to ya fito karara ya fadi dalilan da yasa ya aiwatar da wasu manufofi wanda a yau shi kadai akasa a gaba sanin cewa akwai majalisar koli ta kasa (A.F.R.C) a lokacinsa wanda dukkan matsayin da ya dauka sai da amincewa da yardan su .
Dabara ta rage game shiga rijiya , mu talakawa fatan mu shine Allah ya bamu shugaba nagari wanda zai fidda talaka daga halin kakani-kanin da ya sami kansa a ciki . Gashi Janar Babangida in har yana da kyakyawan manufa da buri na inganta da cigaban talaka da Nijeriya sai muce Allah ya bashi sa'a.

Haza wassalam Nine

Shehu Mustapha Chaji

shehuchaji@yahoo.com

No comments:

Post a Comment