Tuesday 1 January 2008

Zaben Kasar Kenya: Wani Koma Baya ga Tsarin Dimokaradiya a Afrika

Zaben da aka gudanar a kasar Kenya ranar 27 ga watan Disambar 2007 ya bar baya da kura da tambayoyi da dama kan cewa shin kasashen Afrika a shirke suke subi sahun kasashen duniya wajen gudanar da zabe na gaskiya da gujewa magudin zabe wajen baiwa talakawan su abinda suka zaba?Hukumar zaben kasar ta Kenya ta bayyana cewa Shugaba Mwai Kibaki ne ya lashe zaben sabanin harsashen farko dake nuni ga Mista Raila Odinga na kan hanyar lashe zaben.

Kasar Kenya ta kasance kasa mafi karfin tattalin arzikin a gabashin Afrika,kuma arzikin ta ya dauru ne akan yan yawon bude ido,inda kasar ke samun kudin shiga na miliyoyin daloli a kowane shekara.Zargin da jama'ar kasar keyi na an basu shugaban da basu suka zaba ba ya jefa kasar cikin tashe-tashe hankulan da daruruwan mutane suka rasarayukan su.

Kamar mafi yawan kasashen Afrika da kabilanci ke taka muhimmiyar rawa wajen cigaba da danne talakawa da tauye cigaba,inda shugabanni ke shigewa cikin rigar kabilanci su cigaba da mulki,kasar Kenya ta sami kanta a cikin wannan matsalar .Shugaban kasa mai ci Mwai Kibaki ya fito ne daga kabilar Kikuyu(mafi rijaye a kasar),inda shi kuma jagoran yan'adawa Raila Odinga dan kabilar Lous ne. Adawa da sakamakon zaben ya juye zuwa fadan
kabilanci tsakanin yan kabilun biyu.

Jagoran yan adawa Raila Odinga wanda jam'iyyun adawa karkashin lemar Orange Democratic Movement (ODM) suka tsayar shahararen dan siyasa ne a kasar kuma da'ne ga tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Jaramogi Oginga Odinga.Ya kuma fara takarar shugaban kasane a shekarar 1997 inda yazo na uku lokacin tsohon shugaban kasa Daniel Arap Moi wanda shi ya lashe zaben sannan shugaban kasar na yanzu Mwai Kibaki yazo na biyu. Odinga dan siyasa ne da yake da gagarumin goyon bayan talakawan kasar ,kuma yana da kyakyawan tsarin gudanarwa wajen iya cin zabe.An kuma ganin sa a matsayin dan siyasa dake da yawan canza sheka.

Shugaba Mwai Kibaki wanda yayi saurin rantsar da kansa awa guda bayan fadin sakamakon zaben ya aiwatar da ayyukan cigaba musamman ta fannin tattalin arziki inda arzikin kasar ya bunkasa. Kibaki ya karbi mulkin kasar bayan shekaru masu yawa da kasar ta kasance karkashin mulkin jam'iyya daya tilo wato Kenya African National Union(KANU). Shugabanni biyu ne suka shugabanci kasar ta Kenya bayan samun mulkinkai daga kasar Birtaniya a shekarar 1963 wato tsakanin Shugaba Jomo Kenyatta da Daniel Arap Moi kafin shekarar a shekarar 2002 Shugaba Mwai Kibaki ya jagoranci jam'iyyun adawa suka kada jam'iyyar KANU a zaben da aka gudanar a shekarar.

Zaben na kasar Kenya na fuskantar suka daga cikin kasar da wajen kasar .Kungiyoyin sa ido sun shaida cewa an tafka magudi a zaben.Kuma wani abinda ke karfafa wa yan'adawar kasar gwiwa shine na cewa kuri'o 230,000 kawai ne rata tsakanin Kibaki da Odinga kuma jam'iyyar Odinga ita ta lashe mafi yawan kujerun majalisun kasar ,wannan shi yasa suke zargin cewa da anyi kidayan gaskiya da sun lashe zaben da gagarumin rijaye.Ko kungiyar sa ido na tarrayyar Turai sun shedi cewa anyi aringizon kuri'o saboda a cewar shugaban nasu Mista Alexander Graf Lambsdorff , yace "an hana mu shiga wuraren da ake tattara tare da kidaya kuri;o kuma sakamakon da hukumar zaben kasar ke bayar wa ya sha ban-ban da sakamakon dake fitowa daga inda akayi zabubbukan".

Abubuwan da suka faru a kasar Kenya bayan zaben abin takaici ne da kunya ga kasar Kenya .Kamar Nijeriya , itama ta kasa gudanar da zaben gaskiya .Kuma kasar Kenya kamar Nijeriya tana da mutumci da tasiri a yankin gabashin Afrika dama Afrika gabaki daya.Shugaba Mwai Kibaki dan shekara 76 a duniya bai yi halalci ba, bai kuma sa bukatun kasar kan bukatun sa ba.Da anyi zaben son zuciya kamar yadda yayi a yanzu da bai hau kan kujerar mulkin kasar ba .A yau ya jefa kasar sa cikin kashe-kashe da fadan kabilanci wanda zai raba kan jama'ar kasar da maida ita baya a fannonin cigaba.Boren da jama'ar kasar keyi ya nuna a fili bashi suka zaba ba kuma sun gaji da salon mulkin sa.

Matsalar magudin zabe nada illar gaske ga kuma sa duk shugaban da yazo ta hanyar rashin samun kwarin gwiwa ya bugi kirji ya aiwatar da ayyukan cigaba saboda rashin halarci da jin linzamin wadanda suka daura shi. A karshe sukan koma wajen Amerika da Turawan Yamma dan samin yarda a madadin aiwatar da bukatu da manufofin su. Gubar magudin zabe na kara yaduwa in kasashen da ya kamata su zama abin koyi ga wasu kasashe a Afrika suma suka tsinci kansu a matsalar magudin zabe kamar Nijeriya . Ga kasar Kenya tabi sahu,wacce abar koyi ce ga kasashen gabashin Afrika.

Kasar Kenya ta tsinci kanta a wani hali na ban takaici da kunya saboda son zuciya na wasu shugabannin ta , inda a yanzu sun bude gabar kiyayya a tsakanin kabilun kasar su, inda talakawa da basu ji ba basu gani ba ake ta karkashe wa da kwasar ganima da kone dukiyoyin su. Shugabannnin kasashen Afrika nada bukatar canza takun su game da yanda ya kamata a gudanar da zabe domin cigaba da bunkasar tsarin dimokaradiya a nahiyar mu.


Haza Wassalam

Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com