A kwana a tashi rananar 29 ga watan mayu na wannan shekarar Shugaba Olusegun Aremu Obasanjo zai kamala mulkin sa na tsawon takwas a karagar mulkin Nijeriya , wanda a wannan ranar ne zai mikawa Alhaji Umaru Musa Yar’adua mulki a matsayin zababbaben shugaban kasa.
Yan Nijeriya zasu yi kewar Shugaba Obasanjo bias mahangar da suke kallon sa.Ya kasance hadari sa gaban ka inda kake so , domin duk abinda ransa ya biya masa ko ana ha maza ha mata sai ya aiwatar dashi.
An sami cigaba ta fannoni da dama a shekarun da yayi bias mulki .A lokacin mulkin sa ne wayar tafi da gidan ka ya zama ruwan dare ,sabanin shekarun baya da wayar sadarwa sai masu hannu da shuni. An aiwatar da manufofin sauye-sauye daban daban musamman a fanning tattalin arzikin. Sabbin manufofin sun karfafa bankuna da sabon tsarin fansho da Karin albashi da biyan basusukan da suka yi ma Nijjeriya katutu. Shugaba Obasanjo ya kuma kafa hukumomin yaki da cin hanci da almudahana ta hanyoyin kirkiro hukumomin EFCC da ICPC wanda a lokacin mulkin sa ne manya jami’an gwamnati har da babban sufetun yan’sandan Nijeriya Tafa Balogun suka fuskanci shari’a bias tara dukiya ta hanyar haram. An kuma sake fasalin babban birnin tarayya Abuja domin ta kasance cikin manyan biranen duniya da gina tashoshin bada wutar lantarki da kuma bada kwangilar gina tagwayen hanyoyi da sabon tashoshi da jiragen kasa da sauran su.
Shugaba Obasanjo ya kuma kasance wanda a lokacin mulkin sa duk da dai shi ba Musulmi bane, jihohi da dama suka sami damar aiwatar da Shari’ar Musulunci ba tare da fuskantar wata tsangwama ba daga gwamnatin tarayya. Ya kuma kasance shugaba mai girmama addinan talakawan sa inda a watan azumi ,dashi ake azumi. Bai kuma mika wuya ga kasashen da suke yaki da ta’addanci ba wajen shirya makircin da za’a yi farautar Musulmi ba da sunan yan’atadda bane .
Amma ga talakawan Nijeriya da yan ‘adawa suna ganin cewa ba’a taba samin gwamnatin da ta jefa talakawa cikin halin kakanikayi ba kamar lokacin mulkin Obasanjo. Kamar yadda Janar Muhammadu Buhari ya sha fadin cewa tun lokacin aka samar da Nijeriya a shekarar 1914 babu gwamnatin da ta sami kudin shiga kamar gwamnatin Obasanjo , sannan babu lokacin da talauci da fatara yayi wa al’umma katutu kamar lokacin gwamnatin Obasanjo.Sannan kasar bata taba shiga halin rashin tsaro ba kamar a wannan lokacin inda dubban jama’a suka rasa rayukan su a tashe tashen hankulan addini da kabilanci da fashi da makami da kisan gillar da akayi wa fitattun mutane.
Duk da makudan kudaden da gwamnatin sa ke fadin ta kasha kan samar da wutan lantarki , kasar ta kasance cikin duhu har ta kai ga kamfanoni da masana’antu da dama sun durkushe. Haka ma babu ingantattun hanyoyi da tsaftatacen ruwan sha , ga rashin aikin yi da Koran dubban ma’aikata daga aiki wanda ya jefa dubban mutane majiya karfi zaman kasha wando. Karin kudin man fetur da dangogin sa babu kaukautawa ya haddasa tsadan rayuwa da kara jefa talaka cikin halin matsi da da gwamnatin Obasanjo keyi kusan kowane shekara.
Kan batun yaki da cin hanci da rashawa wasu masu nazarin harkokin yau da kullum na ganin cewa a baki kawai gwamnatin Obasanjo ke yaki da cin hanci da rashawa. Saboda suna ganin akwai wadanda suka zama yan lele sa ,duk da korafin da ake na a bincike su amma ya toshe kunnen sa ,amma sai wanda suka kasance yan bora kadai ake tursasawa kan batun cin hanci da rashawa. Sannan masu sharhi kan harkokin siyasa na kuma yiwa gwamnatin Obasanjo yar’amshin shatar turawan yamma da Amerika da bankin duniya ,domin manufofin da gwamnatin sa ke gudanawar daga su ya karbo.
Amma me yasa yan Nijeriya ke ganin laifin Shugaba Obasanjo musamman mutanen Arewa? Wasu suna zargin sa da cewa da gangan ya taimaka wajen ganin cewaq Arewa bata sami cigaba ba kamar mutanen kudancin Nijeriya musamman a fanning tattalin arzikin kasa inda yan kuddancin Nijeriya su suka fi cin gajiyar manufofin gwamnatin sa a bangaren sauye sauyen bankuna da sayar da kaddarorin gwamnati . Haka kuma wasu na zargin sa da baiwa mafi yawan mukaman gwamnati ga yan bangaren sa. Amma abin tambaya anan shine kudaden da gwamnatin tarayya ke baiwa jihohi da kananan hukumomi a matsayin kudin rabon kasa, shin gwamnoni da shugabannin kananan hukumomi sunyi ayyukan raya kasa ga jama’ar su? Sannan kuma yan Arewan da suka rike mukamai a gwamnatin sa sun kawo wa al’ummar da suke wakilta abubuwan more yaruwa?
Kowa ya tuna bara bai ji dadin bana ba, domin yan Nijeriya su sani koda sun manta cewa da Janar Ibrahim Babangida ya mika wa wanda ya lashe zaben 12 ga watan juni na shekarar 1993 da bamu sami kan mu a halin da muke ciki ba. Sannan hadin gwiwar su Janar Babangida da yan G-34 su suka tsaya kai da fata Obasanjo ya sake dawowa bias mulkin Nijeriya. Inda kuma a zaben 2003 bisa jagorancin Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar aka sake dankarawa yan Nijeriya Obasanjo.
Yakamata yan Nijeriya su yi karatun ta natsu su daina daura wa Shugaba Obasanjo duk laifufukan tabarbarewan al’amurra shi kadai! Ta bangaren sa ya lura da cewa masu kaiwa da komowa a matsayin shugabannin al’umma mutane ne masu tsananin son kan su, su kadai. Saboda haka ko wanne daga cikin su na da farashin sa da in aka taya zai sallama. Ya kuma fahimci cewa talakawan Nijeriya suma ta bangaren su , basu ma san inda aka sa gaba ba da rashin sanin hakkokin su .Wannan ko a bayyane yake kan yadda aka gudanar da zaben wannan shekarar inda duk da korafai korafai da ake maluman addini sune kan gaba wajen halasta sakamakon zaben.
Da masu cewa mulki ya komo Arewa ko kuma ya komo hannun Musulmi lokaci ne kawai zai tabbatar in da gaske suke yayin da kida ya canza.Domin wasu daga cikin su har zalamar su tafara fitowa fili bias mubaya’ar da suka yi wa Shugaba mai jiran gado Alhaji Umaru Musa Yar’adua .Yayin da hakar su ta kasa cimma ruwa muna sauraron me zasu fito su fadawa yan Nijeriya.
Shugaba Obasanjo dai tasa ta kare a bias jagorancin da yayi wa yan Nijeriya , tarihi a sannu zai bayyana matsayin sa kan yayi abin kirki ko akasin sa. Yan jari hujja da masu hannu da shuni ba shakka sun ci gajiyar mulkin Obasanjo , a yayin da talakawa musamman wadanda yan’uwan su suka rasa rayukan su a rigingimun kabilanci da addini ko kuma dubban talakawan da aka raba su da aiyukan su ko muhallin su da sana’ar su musamman a birnin tarayya Abuja zasu yi takaicin mulkin Obasanjo. Haka kuma tarihi zai bayyana irin gudumawar da Shugaba Obasanjo ya bayar ga bunkasar dimokaradiyya ko wanin sa . Da fatan in ya koma gonar sa ta Ota zai kyale sabon shugaban kasa ya gudanar da ayyukan mulkin sa ba tare da fuskantar katsalandar saba cikin harkokin mulkin sa.
Hazawassalam
Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com
Saturday, 12 May 2007
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment