Thursday 17 May 2007

KO GWAMNA SHEKARAU ZAI MAIMAITA?

Jam’iyyar PDP ita ta lashe zaben 1999 lokacin da sojoji suka mika mulki ga gwamnatin dimokaradiya a jihar Kano . Amma sai reshe ya juya da mujiya a zaben 2003 inda Malam Ibrahim Shekarau karkashin inuwar jam’iyyar ANPP mai adawa ta karbe mulki a hannun Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso na jam’iyyar PDP.

Gwamna Ibrahim Shekarau ya sha fama da gwagwarmaya kafin ya zama dan takarar jam’iyyar ANPP a jihar Kano . Saboda wanda jam’iyyar ta tsayar da farko Alhaji Ibrahim Al-Amin Little bai sami amincewar tsofin yan jam’iyyar ba inda sai da sukayi kullin da aka maye shi da Malam Shekarau a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar ANPP. Kuma faduwa tazo daidai da zama inda yaci gajiyar umarnin da Janar Muhammadu Buhari ya bayar ga magoya bayan sa na a zabi “ANPP SAK”.

A shekaru kusan hudu da yayi kan kujerar mulki Gwamna Shekarau ya aiwatar da aiyuka daban daban kamar samar da aikin yi a ma’ikatun gwamnati , koyar wa matasa sana’oi , kafa hukumomin da zasu kula da Shari’a kamar zakka da kumusi, Hisba ,A daidaita sahu da hukumar Shari’a, ya kuma gina sababbin ajujuwa da makarantu , bawa yaya mata ilimi kyauta,kari kudin tallafi ga dalibai a manya makarantu , karin albashi ga ma’ikata, bayar da abun buda baki kyauta da watan azumi, samar da motocin haya daban daban ga mata da maza ,d.s .

Daga bangaren yan’adawa suna ganin cewa bawani abun azo a gani da Gwamna Shekarau ya aiwatar na cigaba da bunkasar jihar Kano . Sunce gwamnatin sa ta karbi biliyoyin nairori daga gwamnatin tarayya a matsayin kason ta amma babu aiyuka da zaka iya nunawa a kasa cewa ga inda akayi aiyuka da kudaden . Sannan kuma sunce yana shekara biyu bias karagar mulki karbi fiye da dukkan kudin kason kasa da Gwamna Kwankwaso ya samu a shekara hudu.

Magoya baya da masoyan Gwamna Shekarau tun a bara suka yi ta kira a gareshi da ya sake neman komawa bias karagar mulki a wa’adi na biyu sanin cewa shi Gwamna Shekarau da kansa ya shedawa Kanawa cewa shi wa’adi guda kawai zai yi domin shi a kamus dinsa ta siyasa babu tazarce . Gwamna Ibrahim Shekarau dai ya fito ya amsa kirasa na sake neman komawa gidan gwamnati a karo na biyu da magoya bayansa kewa lakabi da “tamaimaita” sabanin kalmar tazarce da aka fi sani.

Shin Gwamna Shekarau zai cimma burin sa na sake maimaitawa?Shin Shekarau zai zama mutum na farko a tarihin siyasar Kano wanda zai yi mulki har wa’adi biyu?Shin yanayin siyasa a shekarar 2003 dai dai yake da na yanzu? Samun amsoshin wannan tamboyoyin kadai shi zai iya nuna ko Gwamna Shekarau zai maimaita ko a’a .

Ta bangaren jam’iyyun adawa kamar su PDP, AC, PSP wanda masu nazari kan harkokin siyasa suna ganin cewa zasu taka muhimmiyar rawa wajen kokarin gadar da wanda zai maye Gwamna Shekarau a zabe mai zuwa . Jam’iyyar PDP da aka karbe mulki a hannun ta a 2003 ta cika ta batse day an takara masu son karbe wa PDP mulkin ta a hannun ANPP. Fittatu daga cikin su sune Arc. Aminu Dabo , Alhaji Ibrahim Al-amin Little , Alhaji Salisu Buhari tsohon kakakin majalisar wakilai , Dr.Abdullahi Ganduje , sai shi tsohon gwamna wato Engr Rabi’u Musa Kwankwaso da magoya bayansa suka saya masa form na takara d.s . Daidaituwa da zaben gaskiya gun fidda gwani na iya samara wa jam’iyyar PDP dan takarar gwamna na gari da za’a kai ruwa rana dashi a zaben na 2007 a jihar Kano .

Jam’iyyar A.C wanda mafi yawa daga cikin ya’yanta da shugabanin ta kaura sukayi daga jam’iyyar PDP da ANPP a jihar Kano . Jam’iyyar nada jiga-jigan yan siyasa irin su tsohon gwamnan jihar Kano Dakta Abubakar Rimi , tsohon minister Alhaji Musa Gwadabe , tsohon kakakin majalisar wakilai Alhaji Ghali Umar Na’abba da Hajiya Naja’atu Bala Mohammed d.s . Fittatun yan takarar gwamna a jam’iyyar ta A.C sune Alhaji Sule Ruruwai da Alhaji Ghali Umar Na’abba da magoya bayansa ke matsawa ya fito takara shima . Duk wanda jam’iyyar ta tsayar ana ganin cewa lallai zai taka muhimmiyar rawa a zaben 2007 saboda sanin makaman aiki da suka yi .

Ta bangaren jam’iyyar PSP kuma wanda badan Janar Buhari yayi umarnin da’a zabi ANPP SAK ba to da ana tsammanin jam’iyyar ita zata kafa gwamnati a shekarar 2003 a jihar Kano . Dr. Yakubu Danhassan tsohon akanta janar a gwamnatin Gwamna Kwankwaso kuma na hannun daman sa sun raba gari saboda bukatar shi Danhassan din na shima ya gaje kujerar Gwamna Kwankwaso a zaben 2003 . Yayi matukar farin-jini da samun karbuwa kafin guguwar ANPP SAK ta dushe tauraron sa . Shima yana ta shirye-shiryen tallata kansa ga Kanawa su bashi dama ya zama gwamnan su karkashin jam’iyyar sat a PSP.

Lallai Gwamna Shekarau nada jan aiki inda gasket yake na yunkurinsa na komawa a karo na biyu. Ga rigin-gimun cikin gida ta jam’iyyar sat a ANPP inda ta dare gida biyu ko wace bangaren na ikirarin cewa itace ta halas . Ga zarge-zargen da akeyi wa Gwamna Shekarau na cewa sun riga sunyi hannun riga da Janar Buhari musamman rawan da ake zargi shi Shekarau ya taka wajen ganin cewa yan takara masu goyon bayan Janar Buhari basu kai labari ba a zaben fidda shugabannin jam’iyyar ta ANPP a Abuja kwanakin baya.

Yan siyasar jihar Kano suna da wani canfi na cewa ba’a mulkin Kano sau biyu . Suna cewa a tarihin siyasar Kano ba’a taba samun wanda yayi mulki ya sake nema ya samu ba. Suna kawo misalai da tsohon Gwamna Abubakar Rimi wanda duk da farin-jinin sa Marigayi Alhaji Sabo Bakin-Zuwo ya kada shi , Arc. Kabiru Gaya tunda ya bar mulki yake ta yunkurin sai ya koma amma har yanzu burin sa bai cika ba . Haka ma tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso hakansa bata cimma ruwa ba. Ko Gwamna Shekarau zai karya wannan canfi da ake fada na kasa samun wa’adi na biyu ?Abun da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa .

A shekarar 2003 rundunar da ta hada kai takai Shekarau ga gidan gwamnatin jihar Kano ta daddare .Gwamna Shekarau ya rigaya ya raba rana da yan’jam’iyyar tasa da suka mara masa baya a zaben 2003 kamar Alhaji Haruna Ahmadu Dan-Zago da a yanzu ya farraka da nashi bangaren na jam’iyyar a jihar Kano.Hajiya Naja’atu Bala Mohammed wanda itace ta samara da kalmar ANPP SAK ta fice daga jam’iyyar zuwa AC ,Janarorin da suka mara masa baya irinsu Janar Bashir Magashi shima ya kama gaban sa , shi kuma Birgediya Janar Halliru Akilu zai mara wa uban gidansa wato Janar Babangida baya wanda a yanzu yana cikin jam’iyyar PDP . Malaman da suka mara masa baya domin ya aiwatar da Shari’ar Musulunci suma sun zarge shi da kasa aiwatar da Shari’a yadda ya kamata har sun ajiye mukamman su a gwamnatin sun fice .

Uwa uba Gwamna Shekarau da Janar Buhari sunyi kalamai masu banbanci da juna a hirar da akayi dasu a gidan rediyon BBC inda Janar Buhari yace anyi magudi a zaben fidda shugabannin jam’iyyar ta kasa shi kuma Gwamna Shekarau y ace anyi zabe na gaskiya . Amma masu nazari kan harkokin siyasa na ganin cewa kowannen su na bukatar juna don cimma burikan su wato Janar Buhari dan lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa a jam’iyyar ANPP shi kuma Gwamna Shekarau dan samun goyon bayan sa dan sake komawa karagar mulki .

Rana dai bata karya sai dai uwar diya taji kunya , Ko Gwamna Shekarau zai maimaita ?Lamari ne da Kanawa zasu tantance a zaben 2007 in sun gamsu da aiyukan sa . Lallai in Gwamna Shekarau ya lashe zaben 2007 ya maimaita to lallai ya kafa tarihi da ba masu adawa dashi kunya a fagen siyasa .

Haza wassalam

Shehu Mustapha Chaji

No comments:

Post a Comment