Gwamnatin shugaba Olusegun Obasanjo wacce it ace gwamnati mafi dadewa a tarihin Demokradiyya a Najeriya,za ta kawo karshe a ranar 29 ga watan Mayu 2007. Mutuwar tazarce da ya kawo karshen neman tsawaita lokacin mulkin shugaba Olusegun Obasanjo na nufin bullowar wani zababben sabon shugaba ta hanyar demokradiyya.
Kamfen din siyasa ya fara ne da neman wanda zai ja ragamar kasa da kuma wadanda za su rike suaran mukaman siyasa.Kamar yadda ya zama ala’ada a siyasance tuni an fara batun yankin kasa da zai samar da shugaban kasa.Sai dai abin tambaya anan shine ko a wannan karon ma yan Najeriya za su bari azarbabi ya kwashesu wajen neman wanda zai zama shugaban kasarmu na gaba maimakon cancanta da dacewa?
Yan siyasa masu neman garabasa da kuma yan siyasa da suka kasance kaska rabi mai jini suna fakewa bayan bangaranci da kuma maida shi a matsayin ma’aunin da shugaban kasa na gaba zai fito.
Shugaban da talakawan Najeriya ke bukata shine wanda tunainsa ya ke na al’umma ne,wanda kuma zai zama tamkar uba ga dukkan mutanen kasa ba tare da la’akari da kabilarsu ba ko yankin da suka fito ko kuma addininsu.Cikakken mai kishin kasa wanda mahanarsa ta wuce ta azarbabi-na bangaranci da addini- da kuma ba zai gabatar da kansa a matsayin shugaba mai wakiltar wata kabila ba ko wani yanki. Rikici a kan karba karbar mulki zuwa arewa ko kudu maso kudu ko kuma kudu maso gabas an lullubeshi da addini maimakon dacewa da cancanta a matsayin ma’auni.
Tuni wasu mutane sun fara nuna kawunansu a mastayin masu sha’awar gadar shugaba Obasanjo a 2007.Daga cikinsu akwai mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da Janar Muhammadu Buhari da Janar Ibrahim Babangida da Janar Aliyu Gusau da Birgediya janar Buba Marwa da Farfesa Jerry Gana da Alhaji Bashir Tofa da gwamnoni irin su Kalu Odili Udenwa da Makrfi da Ahmad Sani da Adamu Mu’azu da Adamu Abdullahi.Kawo ya zuwa yanzu an cike gurbin kowane yanki da yan takarar da suke wakiltarsa domin shiga fadar Aso Rock.
Kamata ya yi a ce yan takarar da sunayensu ya gabata da wadanda za zu bayyana anan gaba su nemi a zabesu akan manufofinsu maimakon maida hankali akan yankunan da suka fito dad a kabila ko kuma addini a matsayin ma’aunin da za’a zabesu akansu.Kamata ya yi su kutsa cikin kowane yanki na kasa domin su sami karbuwa a kuma zabesu kamar yadda marigayi Cif M.K.O Abiola ya yi wanda ta kai ga ya rinjayi Alhaji Bashir Tofa ba acikin jahar kano kawai har ma da mazabarsa ta Gandun Albasa.
Ya kamata yan Najeriya su kara zama wayayyu a 2007 su zabo shugabannin da su cika alkawalullan da suka yi a yayin kamfen.Ya kamata a aje azarbabi na bangaranci gefe daya saboda kada a zabi wanda bai cancanta ba domin kawai yana “nawa”.Ya kamata ace shekaru bakwai da suka gabata sun zamarwa yan Najeriya abin lura ta yadda yan siyasa ke aje sabanin da ke tsakaninsu na bangaranci da yanki da addini su hade wuri daya idan suna da manufar da ta hadasu.Bai kamata su bari yan siyasar da ke son yin amfani da hanya mafi sauki ta kabilanci da yanki da addini domin zama shugaban kasa su yaudaresu ba.
Ya kamata yan Najeriya su bude idanunsu kada su bari a yi amfani da su ta hanyar kabilanci da bangaranci da kungiyoyin yanki ba, wadanda ba abinda ya damesu idan ba idan basu gabatar da wanda ajhihunsa yafi nauyi ba a cikinsu a matsayin wanda suka amince ya zama shugaban kasa.Saboda son kansu da kuma kare manufofin kashin kansu yana da wuya su gabatar da dantakarar shugaban kasar da ya fi dacewa daga cikin kabilarsu ko yankinsu.
Har ilayau ya kamata yan Najeriya su sa ido akan ayyukan kungiyoyin addini saboda za su kasance masu yin kira da a zabi “Mutumin da hada akida daya da shi.” Ba tare da la’akari da cewa ya dace ba. Ba su taba kai hangensu nesa da mutanensu ba wajen neman wanda za’a zaba alhali kuwa da akwai yantakara da suka dace masu himma.
Nauyi ne da ya hau kan dukkan yan Najeriya domin tabbatar da anyi tsaftataccen zabe ba tare da hatsaniya ba a zabukan 2007.Bai kamata ace mun bari abinda ya faru a zaben 2003 ba sake faruwa a 2007 ta yadda masu rike da mukami a yanzu za su yi kokarin dora mutanesu da yaransu akan mu ba.
Ya zama wajibi gay an Najeriya su goyi bayan muanen da suka cancanta a zaben 2007.Mutanen da suke da kishin kasa da kyakkyawar manufa da gaskiya,wadanda suke san inda suka dosa suke kuma wadanda suka dauke da manufofin talakawa a zukatansu. Irin mutanen da suke da kishin kai kasa ga kololuwar ci gaba da cin hanci da rashawa ko yunwa ko rashin aikin yi ko rashin tsaro ko dora dangi da na kusa akan mukamai za su zama bas u da muhalli acikinta.
Jam’iyyun siyasa suna da gagarumar rawar da za su taka wajen gabatar da yantakar da suka dace a zabukan 2007.Dole ne su tabbatar da cewa an yi tsafataccen zaben share fage a cikin jam’iyyunsu.Yan Najeria za su bijerewa dukka wani lusarin dantakarar da aka gabatar musu a wata jam’iyya wanda ya shiga gaban wani dantakarar da ya fi cancanta da dacewa.
Koma dai ya zata yantakarar shugaban kasa da za su fi yin tasiri a zabukan 2007 sune Janar Muhammadu Buhari da mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da Janar Ibrahim Babangida.Ya zama wajibi ga yan Najeriya su fara dora ayyukansu da cancantarsu da dacewarsu akan mizani domin su zabi mutumin da ya dace ya jagoranci kasa a zaben 2007.
Yan Najeriya suna bukatar mutanen da suka cancanta su rike makaman gwanmatin tarayya da jaha da kaamar hukuma da kansiloli da majalisun tarayya domin bude sabon shafi a 2007. Dole ne al’umar wannan kasa su ki amincewa da siyasar amfani da kudi da ubangida da yaro da magudin zabe.Cancanta da nagarta da kwarewa da tsayin daka da kishin kasa ne ya kamata su zama ma’aunin mutane a zabukan 2007.
Shehu Mustapha Chaji.
Friday, 11 May 2007
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment