Friday 11 May 2007

KO YAR'ADUA ZAI HAU DOKIN GIRMA?

Alhaji Umaru Musa Yar'adua shine mutumin da hukumar zabe ta kasa ta sanar da cewa ya lashe zaben zama shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP da aka gudanar ranar 21 ga wata ga watan Afrilu ,wanda a yanzu shine shugaban kasa mai jiran gado har zuwa ranar 29 ga watan Mayu yayin da Shugaba Olusegun Obasanjo zai mika masa ragamar mulkin tafiyar da kasa.

Zaben na Mutawallen Katsina na fuskantar korafe-korafe da zargin tafka magudi daga hadin gwiwar jam'iyyun adawa da rahotannin kungiyoyin masu sanya idanu akan zabe daga na cikin gida da kasahen waje. Kuma akan haka hadin gwiwar jam'iyyun adawa sukayi kira da a rushe zabubbukan gaba daya a kuma shirya sabon zabe karkashin gwamnatin wucin gadi . Haka ma wasu daga cikin kungiyoyin masu sanya idanu na cikin gida da wasu fittatun yan siyasa da wasu masu fada aji sunyi kiran soke zabe tare da gudanar da sabon zabe.

Domin nuna cewa da gaske suke, hadin gwiwar jam'iyyun adawa da kungiyoyin kare dimokaradiyya sunyi kiran yan Nijeriya su fito zanga-zanga domin nuna rashin amincewar su da zaben . Haka kuma suna ta kira ga kasashen duniya da kada su amince da gwamnatin da Yar'adua zai wa jagoranci.

Ta bangaren jam'iyyar PDP su suna ganin an gudanar da zabe na gaskiya kuma korafi kawai yan adawa sukeyi dan kin yarda da kaddara . Shima Shugaba Obasanjo ya amince da cewa an sami kurakure a zaben amma wannan bai isa ya hana ingancin zaben ba tare da kira ga yan adawa su garzaya kotu dan bin hakkin zargin da suke yi.

Shugaba mai jiran gado Yar'adua , shi kuma kira yayi ga yan adawa dasu zo a hada hannu domin cida kasa gaba.Sannan kuma wasu kungiyoyi da jam'iyyun adawa duk sunyi masa mubaya'a. Hakama kasashen Afrika ta Kudu da Amerika da Ingila sunyi masa barka tare da fatan aiki tare da gwamnatin sa.

Anya hadin gwiwar jam'iyyun adawa zasuyi nasara wajen kiran da suke yi na sake sabon zabe?Shin al'ummar Nijeriya zasu amsa kiran su na bijirewa sakamakon daya bayar da Yar'adua? Shin kasashen duniya zasu amsa kiran na yan adawa domin nisantar gwamnatin Yar'adua?Shin za'a rantsar da Alhaji Umaru Musa Yar'adua ranar 29 ga watan Mayu?Samun amsoshin wannan tambayoyin na iya samuwa kafin ko bayan 29 ga watan Mayu.

Lallai Shugaba Obasanjo zai sakar wa Shugaba mai jiran gado Yar'adua kan maciji , ya kuma rage agareshi yasan yadda zai yi da ita. Domin da farko masana harkokin siyasa na ganin cewa zai zama shugaban kasa ba tare da amincerwar mafi yawan yan Nijeriya ba saboda suna ganin cewa zaben da ake ikirarin ya lashe bata da
inganci.Na biyu, suna ganin cewa akwai matsaloli da dama dake addaban mutanen Nijeriya daga rashin aikin yi da rashin tsaro da rashin wutan lantarki da sauran su.Na uku,suna ganin cewa zai yi fama da korafe -korafen gwamnatin sa ta gudanar da bincike kan kashe-kashen da akayi na fitattun yan Nijeriya kamar su Marigayi Cif Bola Ige da Cif Harry Marshall da Hajiya Sa'adatu Rimi da sauran su.Na hudu ,gwamnatin sa zata fuskanci kira daga yan Nijeriya kan gudanar da bincike kan yadda aka sayar da kaddarorin gwamnati da kudaden da sukayi batan sawu a hukumomin gwamnati musamman hukumar NNPC da sauran su.Na biyar, tsoma bakin wadanda suke ganin cewa su suka dora shi bisa mulki a harkokin mulkin sa.

Bayan ziyarar mubaya'a da kungiyar Northern Union bisa jagorancin Dakta Oluola Saraki ta kaiwa Mutawalle sun kuma aika wa Janar Muhammadu Buhari da Aljaji Atiku Abubakar wasikun su hakura su kuma goya wa Yar'adua baya, domin a fadin su a'i mulki ya komo Arewa .Irin wadannan ra'ayoyin na kungiyar Northern Union shine manufar da za'a yada kafin ranar 29 ga watan Mayu wanda ta haka ake son Buhari da Atiku dole su hakura. Malaman adddini da Sarakuna ma ba'a barsu a baya ba wajen samar wa Yar'adua goyon baya ba.Wani babban malamin addinin Kirista ,shi kira yayi ga yan adawa in zasu fito zanga-zanga , to su fito da Matan su da Ya'yan su a gaba ba wai su ingiza ya'yan talakawa aje a hallaka su ba.Haka ma wani babban malamin addinin Musulunci da a watannin baya yake cewa shi da kansa zai jagoranci zanga-zanga in akayi magudin zabe ,amma sai gashi yana fadawa al'ummar Musulmi su hakura in akayi zabe duk wanda aka basu su karba sannan a'i mulki ya komo Arewa kuma a hannun Musulmi.Kazalika ma Sarakuna har sun fara kaiwa Shugaba mai jiran gado ziyarar ban girma da mubaya'a.

Ta bangaren yan adawa kuma da alamun cewa bakunan su basu hadu ba.Akwai yan adawar dasu adawar su ta samun miya tayi ja ce,in akayi masu alkawarin samun mukamai ko kwangila to adawa ta kare a wajen su.Kuma akwai yan adawar dasu tasu adawar na an ki biya masu wasu bukatun su ne.Shi yasa wasu suke ganin cewa cikakken dan adawa a siyasar Nijeriyar mu ta yau shine Janar Buhari wanda rawar da ya taka tun siyasar 2003 zuwa yau ya kara tabbatar da mutumcin sa da gaskiyar sa da rashin kwadayi.

Saboda wasu masana harkokin siyasa na ganin cewa in aka kwatanta Janar Buhari da Alhaji Atiku Abubakar za'a gan cewa da shi Mataimakin Shugaban Kasa Atiku aka dama aka sha a zaben 2003,kuma dashi ne ya sami kansa a matsayin Shugaba mai jiran gado da shima ya tsuke bakin sa.Ko Gwamna Bafarawa da yace Buhari ba dan siyasa bane bayan ya koka a zaben 2003 inda ya shawarce shi yaje kotu .Sannan an ya wadanda suka lashe zabe a majalisun jihohi da tarayya da Gwamnoni a jam'iyyun adawa zasu amince da zancen cewa a rushe zaben gaba daya?Wannan halin na yan adawa shi yasa ma wasu masana harkokin siyasa suke ganin cewa za'a rantsar da Alhaji Umaru Musa Yar'adua a matsayin Shugaban kasa ranar 29 ga watan mayu .

Shugaba mai jiran gado Yar'adua nada jan aiki in aka rantsar dashi domin da farko yana bukatar samun goyon bayan al'umma dan gwamnatin sa ta sami gindin zama ,kuma sanin kowa ne cewa lallai gwamnatin sa zata karbu in ya watsar da manufofin gwamnatin Obasanjo na bin sahun kasashen jari-hujja da bankin duniya.Sannan kuma yaki tafiya da mutanen da sune a sahun gaba a gwamnatin Obasanjo ta hanyar hana su mukamaia gwamnatin sa.Tauraron sa zai yi sama in ya sakar wa hukumar EFCC mara su binciki duk wanda ya rike mukami daga gwamnoni da ministoci da sauran su a lokacin gwamnatin Obasanjo in aka kuma same su da laifi to a hukunta su .Sannan ya kwana da shirin cewa wasu da suke ganin cewa su suka dora shi bisa mulki in basu sami biyan bukatun su ba ,su zasu fara sa kafan wando daya da gwamnatin sa.

Tsakanin Shugaba Obasanjo da Yar'adua da jam'iyyar PDP da hadin gwiwar jam'iyyun adawa bisa jagorancin Janar Buhari da Mataimakin Shugaban kasa Atiku ba'a san maci tuwo ba har sai ranar 29 ga watan mayu.

Hazawassalam

Shehu Mustapha Chaji

No comments:

Post a Comment