Thursday, 10 May 2007

TUNAWA DA MARIGAYI MALAM AMINU KANO

TUNAWA DA MARIGAYI MALAM AMINU KANO

Mallam Aminu Kano jagoran gwagwarmayar kwato hakki da yancin talakawa a bana ya cika shekaru ashirin da hudu da rasuwa. Shi ya kafa tare da shugabantan jam’iyyun NEPU (Northern Elements Progressive Union) a jamhuriya ta farko da PRP (People’s Redemption Party) a jamhuriya ta biyu.

Al’ummar yankin Arewa a kasar mu Nijeriya lokacin mulkin mallaka da bayan bada mulkin kai sun kasance a wani yanayi da Sarakunan Gargajiya da masu fada aji suka danne talaka da azabtar dashi tamkar bawa a wasu lokutan ma gara bawa kan irin kamakaryan da ake yiwa talaka. Zamanin ya kasance cikin yanayi na danniya da kamakarya da handama da babakere da nauyuka iri-iri na zalunci da aka dankara wa talakawa. Talakawa a lokacin na biyan kudin haraji da jangali da nomau a gonakin masu mulki a kyauta. Wasu lokutan ma in masu mulkin lokacin suka kai rangadi a yankunan dake karkashin su akan tilasta wa magidanci ya bar gidansa da dukkan abunda ya mallaka harma da iyalansa domin saukar dasu da tawagar su!

Malam Aminu Kano ya bayyana ne a tsakiyar lokacin da ake irin wannan zalunci da danne hakkin talaka . Yayi kira ga al’umma dasu bijire tare da kin amincewa da zalunci da kama karyan da akeyi masu tare da mutumta su kamar yan adam masu yanci da martaba. Kafuwar NEPU ke da wuya talakawa suka shiga jam’iyyar babu kama hannun yaro wanda ya jawo tsoro da fargaba ga turawan mulkin mallaka da Sarakunan gargajiya domin akidun NEPU na kira ne ga kawo karshen yadda suke tafiyar da mulkin su na son rai .

Talakawa a lokacin sun amsa kiran NEPU na samun yanci wanda hukumomi su kuma a lokacin suka dauki tsauraran matakai a kansu inda yayi sanadiyar daure tare da azabtar da magoya bayan NEPU. Wasu yan NEPU suka tafi gudun hijira wasu kuma akama sheka dasu barzahu . NEPU karkashin jagorancin Mallam itace jam’iyyar farko a tarihin kafuwar Nijeriya a kasa daya na yunkurin yanto talaka daga mulkin zalunci fir’aunanci.

Siyasar Mallam Aminu Kano ba siyasar tara dukiya bane. Kwato yancin talaka shine manufar sa . Yanci da daidaituwa da martaba kowa shine abinda Mallam ya tsaya kai da fata har ya koma ga Allah .Mallam baiyi mulkin Nijeriya ba to abin tambaya anan itace wane nasarori ya samu a gwagwarmayar sa ? Lallai Mallam ya sami gagarumin nasara a gwagwarmayar sa na kawo karshen zalunci . Gwagwarmayan Mallam ya tilasta wa Sarakunan gargajiya su sake salon mulkin su tare da kawo karshen nomau kyauta a gonakin masu mulki a kyauta . Ya kuma kawo karshen haraji da jangali . Sannan tsayuwar dakan da Mallam yayi ya baiwa ya’yan talakawa damar samun ilimi zuwa kowane mataki sannan da rike mukaman siyasa da gwamnati wanda a da ya takaita ne kawai ga gidajen mulki..

A yau a ko’ina a Arewacin Nijeriya mutane na kokarin sanin tare da kare hakkokin su da kundin tsarin mulkin kasa ya basu. Suna kuma shiga cikin harkokin bunkasar dimokaradiya domin cigaban kasar su. A yau akwai yancin fadin ra’ayi ka da walwala wanda masu mulkin mulukiya suka hana al’ummar su a wancan zamanin .Mallam Aminu Kano shi ya jagoranci dubban yan gwagwarmayan kwato yanci da wadanda muka sami labarin su da wadanda ma ba’a taba jin su ba muka sami yancin da muke morewa a yanzu. Wasu yan NEPU ma tsire su akayi har suka mutu kamar sannanen labarin Malam Audu Angale . Shi dai an tsire shine a bainar jama’a bias zargin da akeyi masa na batanci ga Iyayen masu mulki ba tare da gurfanar dashi a gaban Shara’a ba . Haka ma an daura daruruwan yan NEPU ba tare da yi musu Shari’a ba in ma an kaisu gaban Shari’a ba’a basu damar kare kansu kan tuhumar da akeyi masu .Irin wannan zalunci da fin karfi shi yasa wasu yan NEPU in aka kaisu gaban alkali sai suce su yan mishan ne domin kotunan basu da hurumin yiwa wanda ba Musulmi ba Shari’a sai a kaisu kotun Nasara inda za’a sake su domin babu shaidun da zasu tabbatar da zargin da akeyi musu.

Mallam ba kamar yan siyasar mu na yanzu bane da suka shiga siyasa domin arzurta kansu da Iyalan su da yan lelen su domin har ya bar duniya abunda ya mallaka shine gida daya da gona. Sabanin yan siyasar yanzu wanda zaka gan an zabi mutum ko motar hawa bashi da ita wasu kan baburan Achaba ma sukaje inda za’a rantsar dasu cikin rigunan aro. Amma a yau sune suka mallaki tarin motoci masu tsadan gaske da manyan gidaje da asusun ajiya a kasashen waje da rukunin kamfanoni duk mallakar su. A takaice sun zama masu hannu da shuni cikin takaitattcen lokaci sannan, wani abin takaici da ban haushi shine duk shekarun da sukayi bias mulki ba wani abin azo again a kasa da sukayi wa al’ummar da suka zabe su.

Da'ace Mallam zai dawo a yau da yayi matukar bakin ciki domin masu ikirarin su mabiyan sa ne da daliban sa a fagen siyasa suma ba'a barsu a baya ba wajen kokarin satar dukiyar al'umma a yau. Zai gan yan siyasar dake amfani da sunan sa domin yaudaran talakawa domin su manufar su da akidun su bana yanto talaka bane ta hanyar samar masa da cigaba da kyautata rayuwar sa bane a'a burin su shine su sami dukiya da mulki.

Arewar yau ba Arewa ce da Mallam ya sani a zamanin sa ba. Wadanda a yau suke tinkaho wai sune shugabanin da dattawan Arewa ba wasu mutane bane face wadanda suke cinikin al'ummar Arewa dan samun bukatun kansu wanda a irin hakan har ya kaisu da nisantar dafe mukaman iko. Sun sami damar inganta tare da kyautata rayuwar al'ummar su lokacin da suke tafiyar da mulkin kasa amma wannan ba akidun su bane illa tara dukiya ta kowace hanya har idon su ya rufe a yau suka sami kansu a tsaka mai wuya.

Mallam Aminu Kano baiyi kasa a gwiwa ba wajen kwato yancin mata tare da ganin cewa ana girmama su da basu hakkokin su. Mallam yayi fafatukar ganin cewa ana baiwa mata gado yadda addinin Musulunci ya tsara domin a lokacin a wurare da dama a Arewacin Nijeriya ba'a baiwa mata gado.Haka kuma ya tsaya kai da fata wajen ganin ana baiwa mata ilimi tare da wayar masu da kai su kasance suna bada nasu gudunmawar ta fannonin zaman takewa da bunkasa tattalin arziki da siyasa domin cigaban su da kasa baki daya.

Masu mulki da yan siyasa ya kamata suyi koyi da Mallam Aminiu Kano ta wajen sanya bukatun talaka a gaba . Gwagwarmayar da yan siyasa a yau suke yi mafi yawa na samun biyan bukatun kan su ne ba wai dan samar da cigaba da kyautata rayuwan talakawa ba. Lallai ya kamata masu mulki da yan siyasa su kyautata dabi'un su saboda in aka tashi bada tarihin kasar mu Nijeriya za'a ambace su a matsayin gwaraza kuma amintattun mutane .

Tabbas tarihi zai cigaba da tunawa da Malam Aminu Kano a matsayin gwarzo kuma jagoran talakawa wanda a rayuwar sa har ya koma ga Allah yayi iyakan kokarin sa wajen gwagwarmayan kwato yancin talakawa tare da samun daidaituwa da mutumci da martaba daga hannun masu mulkin da suka hada kai da turawan mulkin mallaka suka bautar da talaka. Allah ya jikan sa yasa ya huta amin suma amin .

Haza Wassalam

Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com

1 comment:

  1. malam aminu kano Allah yajikasa yayimsa rahama amenn.

    ReplyDelete