Friday, 11 May 2007

Shugabannin da ya dace Yan'Arewa su zaba a 2007

Tun shekarar 1914 da turawan mulkin mallaka suka hada yakin kudu da arewa suka rada wa suna Nijeriya arewa ta shige gaban kudu ta fannoni da dama .Zuwan turawan mulkin mallaka suka tadda arewa da tsarin gwamnati da ilimi da cinikayya da tsimi da tanadi ga yawan jama’a . Wadannan fannonin da area ke dashi ya bayyana cigaban ta kan yankin kudu . Da aka zo bada mulkin kai arewa ce ta karbi ragamar tafi da kasar .

Mulki ya zauna a hannun yan arewa tsawon kusan shekaru talatin da biyar wala na farar hula ko na soja . Musamman in dimokaradiya za’a yi tsantsa to ko shakka babu arewa ce zata lashe zaben ko ace dan takarar shugaban kasa daga arewa ne zai lashe zaben .Tsawon shekaru yan kudancin kasan nan sun koka da wannan babakeren da suke ganin cewa yan arewa suna yi masu ba dan komai ba sai dan sufi su yawan jama’a.

Matsalar da aka samu a lokacin mulkin Janar Ibrahim Babangida na rushe zaben June 12 wanda ake zaton cewa Cif Mashood Abiola daga sashen kudu maso yamma ne zai lashe ya kara sa yan kudancin kasar nan musamman yan yankin marigayi Abiola suka lashi takobin dole mulki ya koma kudu suma su dana . Zaben 1999 sai ya zama wata dama da yan bokon arewa da yan siyasa da tsofin janar-janar na sojoji suka yanke shawarar cewa su mika mulki ga kudancin kasannan ko a’a ce ga yankin kudu maso yamma . Wannan matsayin da yan arewa suka dauka na a yar da mangoro a huta da kuda na neman zama dana sani ga wadanda sukayi gaba –gaba wajen ganin hakan ya tabbata.

Ga alamu dai bayan shekaru takwas chir da barin mulkin daga arewa alamu na nuna cewa mulkin zai sake dawowa .Amma abin tambaya a nan shine tsawon shekarun da mulki yayi a hannun yan arewa a baya shin sunyi amfani da damar wajen inganta rayuwar al’ummar su? Shin tsawon shekarun da mulkin ya bar arewa shin da banbanci tsakanin rayuwar mutanen arewa da lokacin da mulkin ke hannun yan arewa ? Shin yan arewa sun koyi wani darasi da in suka sake samun damar tafiyar da ragamar kasar zasu yi amfani da damar su ? Cikin masu neman takarar shugabancin kasa daga arewa waye jama’a suke ganin cewa lallai zai fidda su kunya in ya sami lashe zaben domin kada a ce gara jiya da yau ?

Yakin arewa da alamu da gaske suke dan mulki ya dawo arewa domin duk manyan jam'iyyu sun tsaida yan arewa a matsayin yan takarar su . Jam'iyyar PDP dake kan mulki sun tsaida Alhaji Umaru Musa Yar'adua gwamnan Jihar Katsina a matsayin dan takarar Shugaban kasa yayin da jam'iyyar adawa ta ANPP suka tsayar da Janar Muhammadu Buhari su kuma sabuwar jam'iyyar AC suka tsaida Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar. Itama sabuwar jam'iyyar DPP sun tsayar da Alhaji Dalhatu Bafarawa Gwamnan Jihar Sokoto a matsayin dan takarar shugaban kasa.

Amma abun tambaya a nan shine shin yawan yan takarar shugabacin kasa daga arewa ba zai iya zama cikas ga dawowar mulki arewa ba ? A tsarin dimokaradiya kowa nada yancin fitowa ya nemi takara in har ya cika sharuddan da aka shimfida na wanda ya cancanta ya tsaya zabe . Ba adalci bane a tilasta wa wani ko wasu kan kada su tsaya takara . Hakkin jam’iyu ne su tsayar da yan takara na gari ta hanyar yin zaben fidda gwani na gaskiya .

Wata dama ta musamman da yan arewa zasu samu a zaben 2007 shine ta yadda manyan Yan siyasa daga Arewa suka sami damar tsayawa takara a inuwowin jam'iyyun su saura dame sai su bayyanawa al'umma me zasu gudanar dan a mara masu baya su ci zabe.
Ya kamata jama'ar Nijeriya musamman yan arewa su tantance su darge kan waye yafi cancanta bisa la'akari da haleyensa da rikon amana da gaskiya da sadaukar da kai da karbuwa a kowane sashi na Nijeriya .Kuma zaiyi kyau a lura da manufofin da kowannen su zai aiyana domin kada a rude mutane da kudi ko ayi masu shigar burtu azo ana dana sani .

Kungiyoyin dake wakiltar jama'a arewa musamman A.C.F dake karkashin jagorancin Cif Sunday Awoniyi da Northern Union karkashin jagorancin Dakta Olusola Saraki nada muhimmiyar rawan da zasu taka wajen ganin cewa an sami daidaituwa a tsakanin yan takara . Zai zama kuskura babba in aka fahimce su suna mara wani ko wasu yan takarar shugaban kasa da basu jama'ar arewa ke so ba .

Shugabannin al'umma a rewa musamman Yan siyasa da Sarakuna da Malaman Addini nada rawar da zasu taka wajen cire son rai da girman kai su ilmantar da jama'ar Arewa kan yan takarar shugaban kasa daga Arewa . Talakawan Arewa na kallon su kuma suna fatan ba za'a kara hada kai dasu ba dan hana su wanda suke so kamar yadda aka hada kai aka hana su Shugabanin da suka zaba a zaben 2003 .

Jama'ar Arewa ya kamata su lura da yan takara musamman yan takarar shugaban kasa wadanda suka mara wa tazarce baya. Yan goyon bayan tazarce basu da wani dalilin da zai sa su fito a yanzu suna neman takara saboda da sunyi nasara da babu batun takarar da suke yi a yanzu .

Fatan talakawan Nijeriya musamman na Arewa shine in mulki ya komo Arewa su sami damar cin moriyar tsarin dimokaradiya ta hanyoyin bunkasa aikin gona da makamashi da masana'antu da samar da ingantattcen ilmi da aiyukan yi da sauran su . Burin talakawan Arewa shine in mulki ya komo Arewa su gani a kas na Kare an ce ana buki a gidan ku yace in gani a kasa .

Haza Wassalam

Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com

No comments:

Post a Comment