Friday, 11 May 2007

Nuna Wa Talakawa Banbanci a Nijeriyarmu ta yau

Nijeriya kasa ce data kunshi al'umma jinsi iri guda wato bakar fata mai mutane miliyan 140 . Kuma Nijeriya kasa ce da Allah ya albarkace ta da dinbin ma'adinai wanda itace ma kasa ta shida a sahun kasashen da suke da albarkatun man fetur a duk duniya . Amma abin takaici da bakin ciki shine talauci da fatara yayi wa al'umma katutu . Akwai tsagoron banbanci a rayuwar talakawa da masu mulki da yan barandar su .

Nuna banbanci da wariya a kasar mu yau sai dada karuwa da habaka yake yi a inda a al'amurran da suka shafi kiwon lafiya da zaman takewa da tattalin arziki da siyasa da ilimi da sauran su akwai rashin daidaito tsakanin talakawa da masu mulki da yan boko .
Talakawan a Nijeriya basa samun ingantattcen asibitoci da magani a inda ma aka same su zaka tarar da asibitocin a matsayin dakunan rubuta magunguna a inda in aiki za'ayi wa mutum in baida kudi to matsalar sa ce . Yayin da a bangare guda masu mulki da iyalen su kan fita kasar waje kawai dan a duba lafiyar su . Ta bangaren ilimi kuma ya'yan talakawa na hallartar makarantun da basu da kujeru ko tebura wasu ma a karkashin bishiyoyi saboda wasu makarantun ajujuwan su sun rushe . Malaman su basu da kayayyakin da suke bukata na koyar wa kuma sukan yi watanni kafin a biya su albashin su da bai taka kara ya karya ba . Inda a bangare guda zaka tarar da ya'yan masu mulki da yan boko a makarantu masu zaman kan su da ajujuwan dake dauke da na'urar sanyaya daki .

Ta bangaren muhalli kuma zaka tarar da talakawa a zaune ne a unguwannin yaku bayi ko ihun ka banza a inda babu tsabtattacen ruwan sha da wutan lantarki akan kari gashi kuma yanayin unguwannin basu ma kamaci dan'adam ya zauna ba saboda rashin tsabta da kulawa yayin da zaka tarar da masu mulki da yan boko suna zaune a unguwanni masu tsari da abubuwan more rayuwa .

Babban birnin tarayyar Nijeriya wato Abuja an fake da sunan tsara birnin an kori talakawa daga garin a inda aka rushe masu gidaje da wuraren sana'aoin su . Abuja ta kasan ce ta masu mulki da yan boko su kadai ! Kai a hatta wuraren bauta ana nuna wa talakawa banbanci da wariya a inda ake ware sahun farko da kujerun gaba ga masu mulki dake zuwa da jibga-jibgan masu tsaron lafiyar su suna zazzarewa talakawa ido. Haka kuma ta fannin sufuri talakawa har gobe suna amfani ne da jakuna da kekuna da manyan motocin daukan kaya da tsofaffin motoci da Achaba domin zirga-zirgan yau da kullum . Su kuma masu mulki da yan barandar su suna hawan motoci masu tsadar gaske ko su hau jirgin sama in tafiya ta kama su .

In talaka ya kukuta ya sami ilimin zamani da kyar zai sami aikin yi koda yake ma wadanda suke aiki a hukumomin gwamnati a yanzu ma ana ta rage su . Su kuma ya'yan masu mulki da mutanen su na zama manyan manajoji da daraktoci a manyan kamfanoni da iyayen su suka kafa da dukiyar haram da suka same ta ta hanyar cin amanar dukiyar kasa dake hannun su. Wadannan kadan ne daga irin banbance - banbancen da wariyar da ake nuna wa talakawa a wannan kasar mai dinbin arziki . Da ace masu mulki suna kwatanta adalci da akalla ba za'a yi fama da fatara da rashin daidaiton da ake ciki a yau ba .

A yaushe yan Nijeriya zasu farka su tashi domin kawo karshen wannan wariya da banbanci a kasar mu ta haihuwa? A kuma yaushe guguwar canji da sauyi zata kada wanda zai zama sanadiyar samun yanci da daidaito da mutumci da talakawan Nijeriya zamu sami daidaituwa suma a mutumta su kamar yan kasa masu cikakken yanci ? A yaushe talakawan wannan kasar zasu sami jagoran da zai zo masu da kyawawan manufofin da zai samar da cigaba da kawo karshen zalunci da danniya da kama karya?

Talakawan Nijeriya tsawon shekaru suke ta fata da addu'ar Allah ya basu shugabanni na gari masu tausayi da hangen nesa da rikon amana da gaskiya. Amma koda yaushe in kamar hakar su zata cimma ruwa sai a kawo karshen irin wadannan shugabannin ta hanyar juyin mulki ko murkushe duk wani yunkurin neman yanci da karfin mulki da dauri da karfin Naira ko ta hanyar magudin zabe ko bada cin hanci da mukaman siyasa.

Tarihin gwagwarmayan neman yanci da daidaituwa dan neman wa talakawan Nijeriya canjin ga samun nagartattcen rayuwa ba zai taba mantawa da gwarazan mazaje da sukayi tsayin daka ga ceto talakawa ba. Fittatu daga cikin su akwai kamar su Marigayi Malam Aminu Kano da ya jagoranci samar wa talakawa yanci a hannun masu mulki na kama karya da Cif Gani Fawehinmi wanda yayi fice a sahun gaba wajen yaki da zalunci da danniya wanda ya jawo masa dauri sau da dama musamman a zamanin mulkin sojoji . Haka kuma tarihi ba zai manta da Marigayi Malam Sa'adu Zungur da Dakta Tai Solarin da Alhaji Abubakar Rimi da Kanar Abubakar Dangiwa Umar da Alhaji Balarabe Musa da Kamred Adams Oshimole da Fasto Olubunmi Okogie da Dakta Yusuf Bala Usman ba domin sunyi fice a tsawun gaba wajen kokarin kwato ma talakawa yanci a Nijeriya.

Tabbas wata rana talakawan Nijeriya suma zasu dara a daina nuna masu banbanci da wariya a kasar su ta haihuwa inda za'a sami wadattacen abinci ga kowa da hanyoyin sufuri na gari da kyawawan muhalli da samun ruwa sha mai tsabta da wutan lantarki akan kari da aikin yi da zabe ba tare da magudi ba .

HazaWassalam

Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com

No comments:

Post a Comment