Thursday 28 June 2007

SARAKUNA DA MALAMAN ADDINI SUNA TARE DA TALAKAWA KUWA?

A jerin shugabannin al’umma a kasar mu Nijeriya ,Sarakuna da Malaman Addini nada matsayi da martaba na musamman kasantuwar su iyayen al’umma.Sun kasance fitilu masu haskakawa al’umma hanya kan yadda zasu tafi da rayuwar su bisa tsari da tarbiya kan tafarkin da sukayi imani dashi.Kuma sun kasance masu umarni ga al’umma kan aikata kyawawan aiyuka da gujewa munanan aiyuka.

Talakawa na matukar girmama su da amsar umarnin su saboda imanin da suke dashi na cewa baza su so duk wani abin da zai cutar da su ba.Amma sabanin irin rawar da sarakuna da malaman addini suka saba takawa, a yau mun wayi gari wasu daga cikin su sun sake salon tafiyar su ta wajen kasancewa tare da masu mulki da masu hannu da shuni.A yau a bayyane yake wasun su sun raba gari da talaka ,sun shiga tawagar masu mulki da masu hannu da shunin da suka dora kasar nan bisa tafarkin jari hujja da tsarin su talaka shine makiyi abin ki,saboda tsare tsaren su da manufofin su a kullum sai kara jefa talaka cikin halin kakani kani da bakar wahala suke kara tsunduma talaka.

Malaman addini a ko’ina cikin duniya an shaide su da a kullum da kasance tare da gaskiya kuma kira ga mabiyan su kan kamanta gaskiya da rikon amana .Basa tsoron fadin gaskiya komai dacinta .Sannan kuma basa hada kai da azzalumai da yan handama da masu halin fataken dare.Littatafan tarihin addini a cike yake da gwarazan malaman da sukayi kira da a daina zalunci,har ma wasun sun jagoranci al’umma ga kawar da zalunci da kama karya.A zamanin nan da muke ciki a idanun mu mun gan ko jin labaran malaman addinin da suka murkushe zalunci da azzalumai,dama malaman da aka daure su,ko aka tilasta masu gudun hijira ,koma aka raba su da rayukan su ba dan komai ba sai dan suna hani ga zalunci da danniya da wasu kalilan mutane suke yiwa mafi rinjayen mutane dan kawai tsarin tursasa al’umma na hannun su.

An wayi gari wasu malaman addini suna fassara littafan addinan su bisa tafarkin da zasu da’da’da wa masu mulki rai dan su sami abin duniya.Mun wayi gari in kayi fashin mulki ko magudin zabe zasu ce Allah ne ya baka! In ka saci dukiyar al’umma zasu ce Allah ne ya azurta ka!! In ka tursasa al’umma da karfin tsiya kan abinda sukayi intifakin basa so zasu ce Allah yace a bika!!! Kuma a yau mun wayi gari wasu malaman addini sune a kullum kan hanyar gidajen gwamnatocin jiha da tarrayya da gidajen wadanda kowa yasan ta hanyar da suka tara dukiyar su.

Ba wai ina cewa laifi bane ga sarakuna da malaman addini suyi mu’amala da masu mulki da masu hannu da shuni bane a’a matsalar shine na basa iya fada masu hakikanin gaskiyar halin da talakawa da kasa ke ciki.Talakawa na shan bakar wahalan da basu taba sha ba tun kafuwar kasar nan Nijeriya.Babu aikin yi da rashin magunguna a asibitoci da rashin wutar lantarki da rashin da babun suna da yawa.Amma wasu sarakuna da malaman addini sun tsuke bakunan su ,sun wayan ce kamar komai na tafiya dai dai! Kullum suka buda bakunan su sai kan talaka,sarakuna su fadawa talakawa su zauna lafiya ba tare da fadawa masu mulki suyi adalci ba, malaman addini kuma wa’azin su a kan talaka sukeyi kan ya daina kaza babu kyau ba tare da fadawa masu mulki su daina jefa talaka cikin matsi ba.
Babu ja kan cewa sarakuna da malaman addini suna da matsayi da martaba na musamman a al’ummar kasar nan.Shin matsayin da martaban bai ishe su bane suke tarewa a gindin masu mulki?Sannan akwai wani abin duniya da suka rasa shi yasa suka zama maroka ga masu mulki?Suna tsammanin kan mutane bai waye bane har yanzu suke fadin son zuciyar su a matsayin umarnin addini?Suna zaton cewa bin son zuciyan masu mulki shi zai kare masu kujerun su?Kuma sai a yaushe zasu samar wa kansu yanci a daina kiran su yan amshin shatan gwamnati?

A shugabannin al’umma a yanzu sarakuna da malaman addini ne kawai suka rage da talakawa kewa kallon da kyakyawan zato saboda imanin da suke dashi na cewa zasu yi masu jagoranci na gari da kare masu hakkokin su da samar masu kyakyawan yanayin da rayuwar su zata kasance cikin sauki da walwala.Shin ba babbar cin amana bane a ce a yau a matsayin su na jagorori sufi damuwa da samun biyan bukatun kan su kan na mabiyan su?Basa tunanin cewa talakawa na kallon su ,suna kuma iya yi masu irin nasu fassaran ,kuma masu iya magana na cewa mutumci madara ne in ya zube baya kwasuwa duka.

Tarihin kasashen turai da wasu a Asiya ya nuna irin rawar da sarakuna da malaman addini suka taka a baya. Me ya kawo karshen tasirun su a yau?amsa a bayyane yake ,saboda dasu aka hada kai da baki ana zaluntar talaka ,sun hada baki da masu mulki da kuma guguwar juyin juya hali yazo sai yayi awon gaba dasu gabaki daya.Shi yasa a wasu kasashen ma gabaki daya babu burbushin tsarin mulkin sarautar gargajiya,su kuma malaman addini suka rasa tasiri a rayuwar al’umma kan umartan su da kyakyawan aiki da hani ga mumunan aiki.

Ina sarakunan da suka tsayawa ,tare da daurewa masu magudin zabe gindi kan su zauna daram a kujerun su na mulki a kasar nan suke?Abinda yaci doma ba zai bar awai ba!Kuma tarihin kasar nan tun jamhuriya ta farko zuwa yau,sarakunan da suka bada hadin kai wajen dorawa talaka wanda bashi ya zaba ba na karewa da murabus!Haka ma duk malamin addinin daya hada baki da masu mulki na rasa girma da kima a idon jama’a dan suna ganin sa a matsayin malamin gwamnati.

Martaban sarakuna da malaman addini na iya karuwa sosai in suka martaba bukatun talaka da kare hakkokin sa.Su sami manufar fadawa masu mulki gaskiya koda a gaban sune,tare da basu shawarwarin da rayuwan talaka zata inganta da kuma kiran su dasu daina cigaba da duk manufofin dake kara jefa talaka cikin matsi.In kuma suka ziyarci gidajen gwamnati daga kananan hukumomi zuwa na tarayya ya kasance bukatun al’umma ne ya kaisu bawai samar wa kamfanonin su da ya’yan su kwangiloli da mukaman gwamnati ba .Yanda suke iya fadawa talaka gaskiya ,su iya fadawa masu mulki gaskiya.Kuma ya kamata a koda yaushe su kasance cikin sahun farko na kira ga gwamnati su canza duk wata manufa da al’umma ke kukan zai matsa masu,ba wai wasu daban su kasance a sahun gaba ba wajen kwatowa talaka yanci.

Shugabani na gari abin koyi ne ga talakawan su .Duk shugaban da ya sace dukiyar al’umma ko a baya ko a yanzu ya zama wajibi ga sarakuna da malaman addini su san irin mu’amalar da zasu yi dasu ,saboda rungumar su a jiki ke bada kwarin gwiwa ga yan’baya kan cewa suma za’a rungume su idan suka bada kudi aka gina wuraren ibadu da kuma kai gaisuwa fada ayi masu sarauta.Talakawa na tare da sarakuna da malaman addini ,da fatan suma kamar yanda ake martaba su,zasu cigaba da kasantuwa da talakawa,domin sabanin haka na iya janyowa talakawa su daina ganin kimar su wanda ka iya zama barazana ga al’umma gabaki daya domin in babba ya tsawatar aka ki sauraran sa to wa ke iya wannan babban aiki na dora al’umma bisa tafarkin shiriya?


Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com

Saturday 2 June 2007

SAMAR DA SABUWAR TASWIYAR HANYA GA MATAN HAUSAWA

Mata a kasar Hausa sun kasance cikin matan da akafi kulawa da su da kokarin ganin sun sami nagartattacen rayuwa kan sauran mata na wasu bangarorin Nijeriya.Hukumomi ma basu yi kasa a gwiwa ba wajen taimakawa mata a inda a jihohi da dama ana basu ilimi kyauta da kulawa ta musamman in suna da juna biyu a asibitoci har zuwa haihuwa. A wannan makalar in mukayi zancen matan Hausawa sun kunshi dukkan matan dake zaune a Arewacin Nijeriya.Kan batun ma wanene Bahaushe ? Zamu barshi dan tattaunawa a wani lokacin .
Duk da a bayyane za'a ga kamar rayuwar matan Hausawa na tafiya ba tare da wata matsala ba, amma a hakikanin gaskiya akwai matsaloli da dama da al'umma suka tsuke bakunan su akai , kuma ba'a wani kokari na ganin an samar da mafita ga wadannan matsalolin .Bisa fahimtar addini da al'ada , da ci da sha da muhalli da tufafarwa duk sun ta'allaka akan miji ,amma kuma sai mazaje da mataye suka yiwa wannan umarnin addini da kuma al'ada wata fahimta ta daban .Wato ta bangaren maza suka noke da fahimtar samun wata dama da zasu dankwafar da mata ta hanyar kin basu damar da zasu inganta rayuwar su su kuma bada nasu gudunmawar ga cigaban ungwanin su da garin su da kasa gabaki daya .Su kuma mata sai suka fake da samun wannan damar na samun bukatun rayuwa bisa tsarin addini da al'ada ,sai yasa suka zauna suka mike kafa basa wani kokari ko yunkurin ganin rayuwar su ta inganta.
Kafin wasu su yi mani kartattacen fahimta , ina magana ne akan yadda rayuwar mata a kasar Hausa ta ta'allaka kan maza ba tare da yin wani yunkurin da rayuwar matan zata inganta su tsaya da kafafun su ba. Duk da cewa matsalolin tattalin arziki a yau ya tilasta wasu mazajen da mata su samar wa kan su mafita ta hanyar koyon sana'oi da kasuwanci da karatu mai zurfi ta fannin addini da boko dan samun ayyukan yi.Amma har yanzu akwai mazan da burin su shine yiwa matan su na aure mulkin mallaka ta wajen toshe duk wata hanyar da zasu sami kudin shiga.Wasu mazan kuma koda sunyi wa budurwa ko matan da zasu aura alkawarin cigaba da makaranta ko aiki,da zaran sun aure su sai suyi mirsisi su ki cika alkawarin da suka dauka.
Saboda hana mata samun kudin shiga ta hanyar aikin yi ko kasuwanci ko sana'a shike zafafa kishi yayin da mazajen su zasu kara aure domin suna ganin duk abinda mijin nasu ya mallaka wata cima zaune zata zo a raba da ita.Haka kuma so dayawa in mijin talaka ne wanda bai mallaki abin duniya ba ,da zarar ya mutu ko wata lalurar rashin lafiya ya sami mijin sai iyalen su shiga halin kakani kani. Ta kan kai da an bar matan da ya'ya, ya rage gare ta tasan yadda zata yi dasu.
Wai ma shin mun taba tambayar kawunan mu me yasa matan Hausawa ke daukan maganan gado da muhimmanci?Sannan kuma me kesa mai mata fiye da guda matan nasa zasu yi ta gasar haihuwa?Shin me ke kawo takun saka tsakanin matan marigayi da yan'uwan sa wajen rabon gado? Kuma me ke yawan kawo rabon gado a kotuna tsabanin shekarun baya da ake rabawa a gida?
Tun ranar gini tun ranar zane ,mafi yawan maza in suka je neman aure zancen da suka fi yiwa mata shine na basu aljannar duniya wanda ke jawo wasu yan'matan ma in makaranta ko aiki suke sai su daina domin kakar su ta yanke saka.Zai fi kyau tun ana neman auren a rika karfafa wa mata gwiwa domin su fuskanci rayuwa ,su kasance suna da manufa da burin da suke so su cimma a rayuwa.So dayawa irin wannan baiwar kan bayyana ga wasu matan yayin da mutuwa ta raba su da mazajen su ko rabuwan auren.Da dama sun shahara ta fannoni da dama da suka zabar wa kan su.
Matan Hausawa na bukatar sabon tsarin rayuwa da zasu taimakawa kan su da mazajen su da ya'yan su da iyayen su da yan'uwan su.Suna bukatar tallafi da karfafa gwiwa kan abinda suka zabar wa kan su a rayuwa.In sana'a take sha'awa ,to a tallafa mata wajen koyon sana'ar da kuma girmama su in akazo harkar cinikayya . Sannan in makaranta take sha'awa to a tallafa mata da taimaka mata har ta cimma wannan burin nata . Haka kuma in aiki zata yi a taimake ta dayi mata kyayawan zato.Ta wannan hanyar lallai mata zasu bada babban gudunmawa ga bunkasar tattalin arzikin kasa.
A zamanin nan da muke ciki da mafi yawan yaran da ake haihuwa mata ne ,akwai bukatar dora su bisa tafarkin da zasu zama masu dogaro da kan su saboda in suka sami kan su a halin mutuwan iyayen su ko mazan su na aure ,ko in auren su ya mutu ko kuma rashin samun mijin aure da wuri , ba zasu kasance cikin wani mumunan hali ba,su kasance suna masu iya dogaro da kan su dama taimakawa wasu.Kuma a wannan zamanin na jari hujja da gwamnati ta janye kusan dukkan tallafi kan abubuwan more rayuwa,magidanta da dama na shan bakar wahala wajen baiwa iyalen su abubuwan jin dadin rayuwa.Shin ba abu mai kyau bane iyalen sa suma su bada nasu gudunmawa ga tafiyar da gida?
Domin a zamanin da muke ciki a yanzu in magidanci na bukatar ya'yan sa su sami nagartattcen ilimi sai ya kai su makarantu masu zaman kan su .Haka ma batun kiwon lafiya da sauran al'amurran tafi da rayuwa na yau da kullum. Ga halin rasa aiki ko sana'a da dubban magidanta suka sami kan su bisa sauye sauye a manufofin gwamnati ,shi ke nan in maigida ya sami kansa cikin tsaka mai wuya sai iyalen sa gaba daya su tagayyara?A kullum muna cin karo da gungun mata da ya'yan su masu tsaida mutane a kan hanya suna neman taimako ko in ce bara,da dubban kananan yara (musamman mata )da ake turo su daga kauyuka domin a'ikatau a gidaje a birane.
Sannan wani babban matsalar da ake fama da ita da kusan kowa ya tsuke bakin sa shine na matsalar yawan Zaurawa .Kusan yadda ake yawan aure ,haka ake yawan sakin matan ,ko kuma mazajen su gudu su bar matan! Me ke kawo yawan sakin mata a yanzu?Koma menene dalilan akwai bukatar samin bakin warware wannan matsalar na yawaitan Zaurawa.
Kungiyoyin mata da kungiyoyin mutunta hakkin yan'adam da matan shugabanni a kowane mataki bisa jagorancin Shugabanin addini ya kamata suyi kokarin ganin ana martaba mata tare da bi masu hakkin su yayin da mazajen su zasu sake su .A wannan lokacin na tsarin dimokaradiyya akwai bukatar neman majalisun dokoki daga jiha har tarayya su yi dokokin da dole in magidanci zai saki matar sa sai a kotu da biyan ta wasu makudan kudade da zai ishe ta tafi da rayuwar ta har ta sake aure. Mafi yawan masu sakin matan su nada ketar ganin matan su tagayyara su kuma rasa tudun dafawa .Haka kuma sau dayawa akan sha wahala da mata ana zaman aure ,amma da zarar walwala tazo sai mazajen su, su hura masu wutar kiyayya har sai an rabu,kiri kiri suna ji suna gani dadi yazo za'a ci babu su. Sannan ga maza marasa tausayi da suke sakin matan su in wata laluran rashin lafiya ta same su dan kawai kada su kashe kudin su wajen neman magani.Wasu mazan kuma dan hannun su da shuni sai su auri mata su sake su in suka cimma burin su !
Lokaci yayi da matan Hausawa zasu hada kafada da sauran matan kasashen da suka cigaba musamman na kasashen Musulmi inda suke da dama kamar kowa ta wajen samun ilimi mai zurfi da damawa asha dasu a harkokin kasuwanci da kimiyya da siyasa.Amma wannan damar ba zata samu ba sai sun yinkuro da kan su domin ganin cewa ana basu damar da addinin su ya basu ,tare da juya baya ga duk wata al'ada da zai tauye cigaban su a rayuwar zamanin mu na yau domin su bada tasu gudunmawar ga bunkasar tattalin arziki da cigaban Arewa da Nijeriya.

Hazawassalam

Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com
http://shehuchaji.blogspot.com/