Friday 11 May 2007

KALUBALEN DAKE GABAN BAFARAWA DA JAM'IYYAR SA TA DPP

Dantakarar Shugaban Kasa karkashin jam'iyyar DPP kuma gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya kasance cikin fitattun yan takarar da suka fito daga Arewa domin maye Shugaba Olusegun Obasanjo yayin da wa'adin mulkin sa zai kare ranar 29 ga Watan Mayu na wannan shekarar.
Gwamna Bafara ya kasance cikin yan siyasar da sukayi fice suka shahara tun bayan da sojoji suka mika mulki a shekarar 1999. Ya kasance cikin sahun gaba a kokarin ganin cewa mulki ya komo Arewa tare da kokarin yin hakan a aikace a zaben fidda gwani na jam'iyyar ANPP a shekarar 2003 inda Janar Muhammadu Buhari ya sami damar tsayawa takara.
Jihar Sakkwato da Gwamna Bafarawa ke mulki a yanzu ta kasance mahaifar manyan yan siyasa da suka taka rawa ta musammman a siyasun kasar nan . A jamhuriyya ta farko Marigayi Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkkwato daya zama Firaminista na farko kasancewar sa shugaban jam'iyyar NPC amma saboda wasu dalilai sai ya tura Marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa zuwa Ikko ya zama Firaminista inda shi Sardauna ya zauna a Kaduna a matsayin Firamiyan Jihar Arewa . A jamhuriyya ta biyu Alhaji Shehu Shagari shi ya zama Shugaban Kasa karkashin jam'iyyar NPN . Wadannan shugabanni biyu tarihin siyasar Nijeriya ba zai taba kammaluwa ba sai an kawo su dan sun bada nasu gudumawa ga cigaban Nijeriya .
Takarar da Gwamna Bafarawa keyi a yanzu shin zai sake kafa tarihi a matsayin wanda zai sake zama Shugaban Kasa daga jihar Sakkwato? Tasirin Gwamna Bafarawa a siyasa zai zarce koya gaza na Sir Ahmadu Bello da Alhaji Shehu Shagari ?Yanayin da Sardauna da Shagari suka sami kansu a lokutan su daidai yake da wanda Bafarawa ya sami kansa a yau?
A zancen gaskiya ba tare da son zuciya ba Gwamna Bafarawa ya aiwatar da aiyukan cigaba ta fannoni da dama a jihar sa. Kuma ya kasance cikin kalilan gwamnonin da suka rike amanar da aka basu . Kuma hukumar EFCC bata sanya sunan sa cikin wadanda sukayi handama da satar dukiyar jihar su ba .Ya kuma kasance cikin shugabanni masu fadin gaskiya komai dacin ta da iyakar kokarinsa ga kare martabar Arewa.
Kamar Gwamna Yar'adua babu zato ba tsammani Gwamna Bafarawa ya fito takarar neman Shugaban Kasa . Wasu masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa jam'iyyar DPP na tsammmanin tsohon shugaban kasa na mulkin soja Janar Ibrahim Babangida zai shigo jam'iyyar yayi mata takara yayin da hakar sa ta kasa cimma ruwa a jam'iyyar PDP amma sai sukaji shiru. Ganin cewa jam'iyyar tazo taron fidda wanda zaiyi mata takarar shugaban kasa amma babu yan takarar shugaban kasa sai shugabannin jam'iyyar suka yanke shawarar tsaida Gwamna Bafarawa yayi mata takarar shugaban kasa. Amma abun tambaya a nan shine Bafarawa da gaske yake yin takarar? Ko kuwa so yake ya sami wata farfajiyar da zai nemi a dama dashi in zaben ya kusa ya janye a biya masa wasu bukatun sa?
Jam'iyyar DPP da Bafarawa kewa takara ta samo asali ne daga jam'iyyar ANPP a inda wadanda ake ta kokuwar jan ragamar jam'iyyar dasu wato bangarorin Mista Don Etiebet da Janar Jeremiah Useni . Bangaren Janar Useni dake samun goyon bayan Gwamna Bafarawa suka balle daga jam'iyyar ANPP suka kafa tasu jam'iyyar ta DPP. Jam'iyyar tayi hobbasa wajen tsaida yan takara daga Shugaban Ksa da gwamnoni zuwa yan majalisar jiha amma sanin karbuwar jam'iyyar ko akasinsa sai anga irin rawar da jam'iyyar zata taka wajen lashe zabe a zabubbukan watan Afrilu. Domin ko a jihar Sakwatto jam'iyyar DPP na fuskantar barazana daga jam'iyyun PDP da ANPP musamman da tsohon Mataimakin Gwamna Bafarawa wato Alhaji Aliyu Magatakarda Wammako wanda ya buga tsalle daga dan takarar gwamna na jam'iyyar ANPP ya koma na PDP.
Gwamna Bafarawa nada jan aiki a gaban sa na zama shugaban kasar Nijeriya domin takara dasu Janar Buhari da Gwamna Yar'aua na manyan jam'iyyun ANPP da PDP ba wasan yara bane. Kuma gasu duk yan Arewa bugu da kari Janar Buhari da Gwamna Yar'adua duk sun fito ne daga yankin Arewa maso Kudu wato yankin dashi ma Gwamna Bafara ya fito.Kuma ko a tsohuwar jihar Sakkwato wanda a yanzu ya kunshi jihar Kebbi da Zamfara sai yayi da gaske domin samin na gashi domin jam'iyyun ANPP da PDP duk sun kama kasa daram karkashin jagorancin gwamnonin su wato Gwamna Ahmed Sani na ANPP da Gwamna Aliero na PDP .
Wasu matsalolin da Gwamna Bafarawa zai fuskanta sun hada da ganin da wasu suke yi masa a matsayin "yaron Babangida" da kuma ganin da wasu suke yi masa na zama kafar ungulu ga Janar Buhari domin dashi kansa da jam'iyyar tasa DPP da ba'a sami matsala ba da duk suna cikin tawagar Janar Buhari a jam'iyyar ANPP. A hirar da gidan rediyon BBC sashen Hausa tayi dashi kwanakin baya da akayi masa tambayar ko zai iya janye wa Janar Buhari ? Sai ya amsa da cewa shi Janar Buhari ne ya kamata ya janye masa a matsayin kanin sa.
Wasu masu fashin bakin siyasa na ganin cewa duk da cewa kundin tsarin mulkin Nijeriya ya baiwa Gwamna Bafarawa ikon tsayawa takara suna ganin cewa yana da karancin ilimin zamani wanda ka iya zama matsala a gareshi gun tinkarar tafiyar da kasa irin Nijeriya a karni na ashirin daya . kuma suna ganin cewa bashi da goyon bayan manyan yan boko da yan siyasa da yan kasuwa wanda suna taka muhimmiyar rawa gun lashe zaben shugaban kasa.
Game da kawancen da jam'iyyun adawa sukeyi na hada karfi gu guda domin kayar da jam'iyyar PDP a zabe a shirye Gwamna Bafarawa da jam'iyyar sa suke domin shiga wannan kawancen?In kuma yaki amincewa da shiga kawancen jam'iyyar sa ta DPP na iya kayar da jam'iyyar PDP a kasa gaba daya?
In har Gwamna Bafarawa ya amince da kiraye kirayen da ake yi masa na janyewa ya mara wa wani dantakarar shugaban kasa daga Arewa baya wa zai marawa baya tsakanin Janar Buhari da Gwamna Yar'adua?
Marigayi Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da Alhaji Shehu Shagari sun tinkari zabubbukan lokacin su duk da rashin goyon bayan wasu daga Arewa kuma sun lashe zabubbukan lokutan su ko zata kasance haka da Gwamna Bafarawa a zaben watan Afrilu? Matsoraci bashi zama gwani kuma a rashin tayi akan bar araha.
Kalubalen dake fuskantar Gwamna Bafarawa nada yawan gaske wanda mafita itace koya maimaita tarihi kamar Sir ahmadu Bello da Alhaji Shehu Shagari ya lashe zabe a rantsar dashi ranar 29 ga watan Mayu a matsayin Shugaban Kasa ko kuma har a kammala zabe ba'a zarge shi da zama dutse a ruwa ba.

Hazawassalam
Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com

No comments:

Post a Comment