Thursday, 10 May 2007

GWAMNA SHEKARAU YA MAMAYI YAN ADAWA YA KAFA TARIHI A SIYASAR KANO!

GWAMNA SHEKARAU YA MAMAYI YAN ADAWA YA KAFA TARIHI A SIYASAR KANO!

Malam Ibrahim Shekarau Gwamnan Jihar Kano sabanin harsashen masana harkokin siyasa da yan adawa ya lashe zaben da aka gudanar ranar 14 ga watan Afrilu inda zai zama mutum na farko a tarihin siyasar Kano da zai maimaita wa'adin mulki bisa kujerar gwamnan jihar .

Ga dukkan alamu Gwamna Shekarau ya karantu bisa yanda ake siyasa a kasashe masu tasowa musamman Nijeriya. Ya kasance gwamnan dake fuskantar adawa ta fannoni da dama. A cikin jam'iyyar sa ta ANPP Gwamna Shekarau na fuskantar adawa daga bangaren su Alhaji Haruna Ahmadu Danzago bisa taimakon Mataimakin Gwamna Injiniya Magaji Abdullahi da T.B.O.

Jam'iyyun PDP da AC da sauran jam'iyyun suma sun kasa dakatar da hankoron Gwamna Shekarau na sake komawa bisa mulki. Anyi zaton jam'iyyar PDP bisa jagorancin tsohon gwamna Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso ko kuma jam'iyyar AC bisa jagorancin Dakta Muhammadu Abubakar Rimi zasu taka rawar da daya daga cikin jam'iyyun su zasu lashe zabe domin samar da magajin Gwamna Shekarau daga cikin Alhaji Ahmed Garba Bichi na jam'iyyar PDP ko kuma Alhaji Usman Sule Ruruwai na jam'iyyar AC.

Akwai bukatar masana harkokin siyasa suyi nazari kan dalilan da suka sa Gwamna Shekarau ya tsallake tsirasin da tsofaffin gwamnonin jihar Kano daga Dakta Abubakar Rimi zuwa Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso suka kasa tsallakewa. Musamman tsohon gwamna Kwankwaso da a lokacin sa duk da yana cikin jam'iyyar dake da mulki a tsakiya ya kasa komawa.

Kuma akwai bukatar sake nazarin tuhume-tuhumen da yan adawa suke yi masa domin sanin gaskiyar lamari, duk da yake jam'iyyun adawa a jihar Kano sunyi zargin magudi amma ta yaya Gwamna Shekarau ya sami goyon baya matuka sabanin su Gwamna Attahiru Bafarawa da Adamu Mu'azu da jama'arsu suka juya masu baya duk da karfin mulkin dake hannun su.

Koda yake Gwamna Shekarau ba zai rika barci da idanun sa biyu a rufe ba sanin cewa jam'iyyun adawa musamman jam'iyyar PDP zata garzaya kotu dan kalubalantar zaben sa , har yanzu za'ace tsugune bata kare ba sai har ranar da kotu ta yanke hukunci bisa karar .
Gwamna Ibrahim Shekarau na bukatar sake salon tafiyar da mulkin sa sabanin wa'adin sa na farko . Yana da bukatar aiwatar da ayyukan raya kasa tunda a baya ya shafe shekaru hudu yana gyaran zukatan jama'ar jihar. Sannan ya san irin mutanen da zai basu mukamai a gwamnatin sa domin a baya mutane nayi wa Kwaminisoshin sa da sauran manyan jami'an gwamnatin sa kallon wasu mutane da suka fi son kan su. Akwai bukatar gwamnatin sa a zango na biyu ya tafi da dukkan jama'ar jihar sabanin wasu mutane su kadai da sukayi wa gwamnatin kaka gida suka zama cimma zaune.

Kuma a matsayin sa na shugaban jiha sai ya mika hannu ga dukkan yan adawa domin su zo a tafi dasu domin ciyar da jihar Kano gaba. Duk dai kan abu daya ake hankoro wato ganin cewa jihar Kano ta cigaba ta kowane fanni ta kuma yi zarra ga sauran jihohin kasar nan. Saboda haka Gwamna Shekarau ya san cewa yan adawa ba suna yi bane dan basu kaunar sa ko kuma dan sun tsane shi bane a'a suna adawa ne bisa hangen su na an kasa daura jihar bisa tafarkin cigaba.

Ga kuma yan adawa kada jikin su yayi sanyi domin dimokaradiyya babu adawa kamar shayi ne babu siga. Su cigaba da adawa mai tsafta bisa dokokin kasa domin ganin cewa Gwamna Shekarau ya cika alkawarukkan da ya dauka. In yan adawa suka mike kafa gwiwar su tayi sanyi to a gaskiya basu yiwa Gwamna Shekarau adalci ba saboda ganin ya sami damar da wani bai taba samu ba yayi zaton zai yi abinda ya gan dama . Dole su cigaba da sa ido in zai karkace su dawo dashi kan hanya.

Talakawan Jihar Kano na bukatar ayyukan cigaba musamman ta fannin samar da wutan lantarki . Ya zama wajibi ga Gwamna Shekarau ya samo hanyar da jihar Kano zata rika dogaro da kanta wajen samun isashen wutan lantarki wanda ta haka masana'antun jihar zasu farfado dubban jama'a su sami aikin yi . Sannan talakawa kada su koma gida su kwanta bayan sun kasa sun tsare har aka tabbatar masu da abunda suka zaba. Ya zama tilas ga talakawa su cigaba da sa ido sosai kan yadda ake tafiyar da mulkin jihar su musamman dukiyar da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya da kudin shiga.

Ya kamata gwamnatin jihar Kano ta fito da hanyar kwance damarar yan bangar siyasa da masu sana'ar siyasa. Yayin da ake kamfe zaka tarar da dubban matasa masu jini a jika suna jefa rayukan su cikin hadari a matsayin yan bangar siyasa , ba dan komai ba sai dan abunda zasu samu su kai bakin salati. Akwai bukatar gwamnati ta sake fadada abunda take yi kan koya wa matasa sana'a.

Koda Gwamna Shekarau yayi nasara a shari'ar da yan adawa zasu kaishi gaban manta sabo ya kwana da shirrin cewa jiga-jigan yan siyasa a jam'iyyun adawa dama na cikin jam'iyyar sa ta ANPP kamar su Dakta Muhammadu Abubakar Rimi da Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso da Janar Bashir Magashi da Alhaji Haruna Ahmadu Danzago da Injiniya Magaji Abdullahi da Dakta Bala Salisu Kosawa da Alhaji Aminu Wali da Alhaji Musa Gwadabe da Hajiya Naja'atu Mohammed da sauran su zasu jira dan dawo da martabar su a siyasance a zabe na gaba yayin da zaiyi kokarin dora wanda gaje shi yayin da wa'adin sa na biyu zai kare.

Ya kuma kwana da sanin cewa a katsa a tsare ya zama al'ada a siyasar Kano inda zai gani a kwayar cin tuwon sa bisa yadda zai tafiyar da mulkin jihar a shekaru hudu masu zuwa in talakawa sun sake gamsuwa su amince da wanda zai nuna a zaba in kuma basu gamsu ba su saka masa kamar jama'ar jihar Sakkwato ga Bafarawa da jihar Bauchi ga Mu'azu.

Fatan mu Kano ta kara cigaba ta fannonin kasuwanci da ilimi da siyasa ta cigaba da bada jagoranci ga jihohin Arewa da Nijeriya gabaki daya da rike kambun koda me kazo an fika!

Hazawassalam
Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com

No comments:

Post a Comment