Friday 11 May 2007

Samar Da Ingantaccen Tsarin Dimokaradiya

Tarihin kafuwar tsarin dimokaradiya a Nijeriya wacce ta fara tun lokacin mulkin mallaka a kullum kan zama cikin tsarkakiya. Kabilanci da addini suna taka muhimmiyar rawa a siyasar nan kasar sai dai abun takaici masu fada aji suna amfani dasu wajen cimma burikansu na dauwama kan mulki.

A jamhuriyan farko jam'iyyun da yan siyasa suka kafa sun kasance jam'iyyun yanki da kabila . Manyan jam'iyyun siyasar lokacin kamar Northern People's Congress(N.P.C) jam'iyya ce da tasirinta da karfinta ya takaita ga Arewa kuma Hausawa da Fulani ne mafi yawan membobin ta. Ita kuma jam'iyyar Action Group (A.G) kabilar Yarbawa ne daga sashen Kudu maso Yamma suka kafa ta tare da mamaye ta. Sannan jam'iyyar National Council of Nigeria (N.C.N.C) ita kuma ta kasance ta kabilar Ibo daga yankin Kudu maso Gabas.

Rigingimun siyasar da ya kai ga rushewar jamhuriya ta farko ya ta'allaka ne ga kabilanci wanda shine hujjar da wasu sojoji daga kabilar Ibo suka fake dashi wajen hanbare gwamnatin jamhuriyya ta farko wanda ya zama sanadin da sojoji suka kutsa kai cikin harkokin mulki da siyasa .

Haka ma aka sake kwata tsarin jam'iyyun jamhuriyan farko a jamhuriyya ta biyu a inda jam'iyyun National Party of Nigeria(NPN) da People's Redemtion Party (PRP) da Great Nigeria People's Party(GNPP) keda tasiri da karfi a Arewa . Jam'iyyar Unity Party of Nigeria (UPN) nada karfi da tasiri a yankin Kudu maso Yamma yayin da ita kuma jam'iyyar Nigeria Peoples Party(NPP) nada karfi da tasiri a yankin Kudu maso Gabas.

Zaben da jam'iyyar NPN ta lashe a zaben 1983 wanda ya hada har da wasu jihohi a yankin Kudu maso Yamma yasa jam'iyyar UPN ta tada kayar baya domin tace sam bazata sabbuba bindiga a ruwa wai ace wata jam'iyya daga Arewa taci zabe a yankin da take da tasiri . Tashin hankalin da ya biyo baya na daga cikin dallilan da sojoji suka sake kwace mulki a hannun yan siyasa wanda ya sake maida Nijeriya baya game da cigaba da bunkasar tattalin arziki.

Da Janar Ibrahim Babangida bai soke zaben June 12 ba da jamhuriyya ta uku ta zama mafi inganci a tarihin siyasar Nijeriya . Jam'iyyun Social Democratic Party(SDP) da National Republican Convention (NRC) wanda dan takarar jam'iyyar SDP marigayi Cif Moshood Abiola da ya zama dan Nijeriya na farko da mafi yawan masu jefa kuri'a suka zaba wanda ba daga yankin su ya fito ba a matsayin dan takarar shugaban kasa .

A zaben 1999 wanda Cif Olusegun Obasanjo ya lashe shima ya fuskanci matsalar kabilanci inda yankin da ya fito na Kudu maso Yamma suka kyamace shi suka ki zaben sa badan komai ba sai dan Yan Arewa suka tsaida shi suke mara masa baya .Haka ma jam'iyyun da suka tsaya zabe in banda jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) jam'iyyar All Nigeria People's Party (APP a lokacin )nada tasiri da karfi ne a Arewa ita kuma jam'iyyar Alliance for Democracy (AD) nada gindin zama a yankin Kudu maso Yamma.

A wannan lokacin na mulkin Shugaba Obasanjo an sami yaduwar da kafuwan kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayuka game da addini da kabila . Wadannan kungiyoyi da suke fakewa da addini da kabilanci sun kasance masu isar da sakonnin kiyayya da kyama da gaba a tsakanin al'umomin Nijeriya . Wadannan kungiyoyi sun kasance cikin abubuwan dake zama barazana ga dorewar dimokaradiya da hadin kan Nijeriya a matsayin kasa daya .

A lokacin zaben 2003 al'ummar Kudu maso Yamma kamar yadda al'addar su a siyasar Nijeriya ta kasance na mara wa nasu baya . Wani daga cikin manyan yakin cewa yayi " duk wani da ya zabi Buhari to tabbas shege ne"(Ma'ana duk wanda ya zabi wanda ba Bayarbe ba akan dan'uwansa Bayarbe to shege ne).Al'amurra sun sake kazanta inda kungiyoyi kusan na ta'adda masu ikirarin kare kabilar su kamar OPC da NDPVP da MOSSOB da MOSSOP sun tsunduma cikin harkokin zabe inda suke jaddada zaben dan takarar daya fito daga cikin kabilar su.

Dimokaradiya a Nijeriya na fuskantar barazanar kungiyoyi kabila da yanki kamar su kungiyar Yarbawa ta Afenifere da YCF (kungiyar dattawan kabilar Yarbawa ) da NU(Northern Union) da Ohanaze Ndigbo da ACF(Arewa Consultative Forum) da Middle Belt Forum da sauran su . Wadannan kungiyoyi ne da aka kafa su domin kare kabila ko yanki wanda maimakon su maida hankali kan abubuwan da suka shafi kasa gabaki daya sun fi maida hankali ne kan abunda ya shafi al'ummar su.

Aikace-aikacen kungiyoyin addini basa taimakawa tsarin dimokaradiya inda a bayyanai suke kira da a zabi dan takara da ake da addini daya dashi ba tare da la'akari da cancantarsa ba. Suna isar da jawabai da wa'azuzukan da kan kawo rabuwan kai da rashin mutunta juna a wuraren ibadun su musamman kan harkokin da suka shafi siyasa.

Har yaushe dimokaradiya zata karkafa a rin wannan yanayi a kasar mu Nijeriya?A yaushe jama'a zasu fara zaben shugabannin na gari ba tare da la'akari da kabila da yanki ko addinin suba? A yaushe yan siyasa zasu daina amfani da bangaranci da yanki ko addini wajen neman kuri'u ba? Wadannan suna cikin matsalolin da yan Nijeriya suke da bukatar shawo kan su kafin zaben 2007 . A yanzu mafi yawa daga cikin masu neman kujerar shugabancin kasa suna fakewa ne da batun yanki domin zaben su . Akwai kira'i kira'i da dama na cewa mulki ya dawo Arewa ko yankin Kudu maso Gabas dake kukan cewa su sau daya suka taba mulki ko kudu maso Kudu da suke cewa babu wani daga yankin su da ya taba shugabancin kasa . Duk an jingine batun cancanta da sadaukar da kai da rikon amana da shugabanci na gari kan neman shugabancin kasa bisa kabilanci da yanki.

Lallai zai dauki lokaci mai tsawo in har ana bukatar shugabanci na gari da ingantatcen tsarin dimokaradiya alhalin ana kauda kai ana son rai wajen zaben shugabani bisa yanki da kabila. In har da gaske muke kan samun shugabanci na gari to ya zama wajibi sikelin da zamu auna yan siyasa dake neman shugabanci ya kasance bisa sanin makamar aiki da sadaukar da kai da rikon amana da cancanta domin kasar mu Nijeriya ta kaima cigaba ta fannonin tattalin arziki da zaman takewa da siyasa .

Haza Wassalam

Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com

1 comment:

  1. Salam. Allah ya saka malam kuma allah ya ganar damu.

    ReplyDelete