Friday, 11 May 2007

JANAR BUHARI DA ZABEN 2007

Mafi yawan yan-Nijeriya nada yakinin cewa da an gudanar da zaben 2003 ba tare da magudi ba da Janar Muhammadu Buhari na dab da kare wa'adin zango na farko a matsayin sa na shugaban kasa mai cikakken iko a ranar 29 ga watan Mayu .Janar Buhari ya kabulanci zaben shugaba Obasanjo har zuwa kotun koli ta kasa da ta tabbatar da cewa Cif Olusegun Obasanjo ne ya lashe zaben 2003.

Duk da kasantuwar abubuwan da suka faru a zaben 2003 , maimakon gwiwar Buhari tayi sanyi sai ya kara hazama da nitsewa cikin harkokin siyasa da kokarin ganin an samar da shugabanci na gari a tsarin dimokaradiya . Janar Buhari a yanzu yana ta shirye-shiryen sake fitowa takarar shugaban kasa a zaben 2007 kuma yana cikin wadanda ake ganin cewa suna sahun gaba-gaba wajen maye Shugaba Obasanjo a 2007 .

Zaben 2007 zai fi ta 2003 zafi da wahala ganin cewa mafi yawan yan takarar daga arewa suke wanda shine yankin da Janar Buhari ya fito , kuma gashi har yanzu yana son sake tsayawa takara a jam'iyyar hamayya ta ANPP.

Janar Buhari nada jan aiki a gaban sa kafin ma ya sami damar tsai dashi a matsayin dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar ta ANPP .Gwamna Ahmed Sani da Bukar Abba wadanda a shekarar 2003 suna cikin masu goyon bayan Buhari suma sun fito dan neman shugabancin kasa karkashin jam'iyyar ANPP .Ga kuma Alhaji Bashir Tofa da yan takara da zasu yi ta kunno kai kafin taron fidda gwani na jam'iyyar a watan disamba . Ko yaya zata kaya tsakanin Janar Buhari da gwamnonin jam'iyyar sa masu neman takarar suma a tsayar dasu da ragowar yan takarar a karkashin jam'iyyar sa ?

Taron fidda shugabanin jam'iyyar ANPP da akayi kwanan nan ya nuna a zahiri cewa Janar Buhari bashi da tasiri a jam'iyyar ANPP inda yan takara goma sha takwas da yake mara masu baya sun sha kasa . Koda yake Janar Buhari yayi zargin cewa gwamnonin jam'iyyar ANPP sun tafka magudi domin ganin cewa yan koren sune kadai suka kai labari .Masu nazari kan harkokin siyasa suna ganin cewa gwamnonin sunyi haka ne domin hana Janar Buhari ya kwace jam'iyya su kuma samu damar tsaida daya daga cikin su dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar ANPP.

Jama'a dama musamman masu nazarin harkokin siyasa sun zaci cewa Janar Buhari zai fice daga jam'iyyar ANPP zuwa wata jam'iyya ko kuma shima ya kafa nasa jam'iyyar .Amma shi Janar Buhari ya fito ya bayyana cewa babu gudu babu ja da baya zai kasance cikin jam'iyyar ANPP kuma karkashin jam'iyyar zai nemi takarar neman shugaban kasa a shekarar 2007 .

Ruhi da goyon bayan da jam'iyyar ANPP take samu ya ta'allaka ne da so da kauna da jama'a musamman ma talakawa kewa Janar Buhari. Wannan kauna ce zata ba Janar Buhari damar zarce duk yan takara masu neman kujerar shugaban kasa a jam'iyyar . Ko shakka babu jam'iyyar ANPP bata da dan takara mai aminci da kwarjiji kamar Janar Buhari . In sukayi kumbiya-kumbiya har basu tsai da Janar Buhari a matsayin dan takarar shugaban kasa ba to lallai jam'iyyar ANPP zata shiga wani hali.

Janar Buhari na fuskantar kalubale masu yawa a inda a mahaifarsa ta Daura jama'a da dama sun fice daga jam'iyyar ANPP zuwa wasu jam'iyyu . Ko Sanata Kanti Bello wanda yana daya daga cikin mutanen da suka shawo kan Buhari ya shiga harkokin siyasa sunyi hannun riga . Haka ma wasu daga cikin magoya bayan sa na gani kashe ni a zaben 2003 suma sun kaurace masa zuwa wasu jam'iyyu .

Hajiya Naja'atu Mohammed , Suleiman Hunkuyi Adamu Modibbo , Sergent Awuse , Mohammed Kumalia , Khairat Gwadabe , Gbenga Aluko , Bashir Magashi , Jeremiah Useni , Paul Unango , Don Etiebet , Gwamna Bafarawa da Saminu Turaki , yan majalisar dattijai da wakilai d.s duk suna cikin wadanda suka ko fice daga jam'iyyar ANPP ko suka rabu da Janar Buhari saboda wasu dalilai . Hakama shi Janar Buhari ya kasa warware dambarwan siyasar ANPP ta jihar Kano wanda ya kai jam'iyyar darewa gida biyu wato bangaren magoya bayan Janar Buhari karkashin jagorancin Alhaji Ahmadu Haruna Dan-Zago da bangaren Alhaji Sani Hashim Hotoro wanda Gwamna Ibrahim Shekarau ke mara wa baya .

Da alamun samun nasara ga Janar Buhari a zaben 2007 in har yayi amfani da damar sa nacin gajiyar dambarwan siyasar da kasar ke ciki a yanzu. Biyu daga cikin yan takara masu tasirin gaske wato Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar da Janar Ibrahim Babangida na fama da rigin-gimun da suka shafi rikon amana . Atiku Abubakar na fuskantar zargin amfani da kudade na hukumar PTDF dan amfanin kansa ga kuma dakatarwan da jam'iyyar sa ta PDP tayi masa . Shi kuma Janar Babangida kamfen dinsa zai raja'a ne ga yiwa yan Nijeriya bayanai kan tambayoyi da dama da suke son yi masa don ya basu amsa .

Game da gwamnonin jam'iyyar ANPP Janar Buhari na iya tsira daga makircin su albarkacin hukumar EFCC wanda ta lashi takobin binciken duk wani dan siyasa da ya fito neman takarar wani mukami . Ga alamu takarar shugabanin kasa a shekara mai zuwa na iya kasancewa tsakanin Janar Buhari da yan bana bakwai a siyasar Nijeriya musamman ma yan'fadanci da karnukan farauta wanda ke kai gwauro su kai mari wai suma yan takaran shugabana kasa ne!

Buhari na iya amfani da rashin fitowar takarar shugaban kasa da yankin kudu maso yamma wajen daukar mataimakin shugaban kasa . Domin al'adar siyasar Yarbawa basa juya wa nasu baya , kuma lallai Janar Buhari na bukatar dunkulellen kuri'u daga wannan yankin domin ya kai labari musamman in har ya dauki mai farin jini da mutunci a cikin su . Domin yadda siyasar take nunawa yankin kudu maso kudu suma sun fito neman kujerar shugabancin kasa wanda saboda haka ba za'a san yadda zasu kada ba . Su kuma kudu maso gabas ba yanki ne da za'a amince masu ba a batun takarar neman kuri'a daga yankin.

Zaben 2007 na iya kasan cewa rawar karshe da Janar Buhari zai taka a fagen siyasa ta takara . Ya zama wajibi da kalubale a gareshi ya gan cewa lallai ya lashe zaben 2007 . In har ya samar da tsari mai kyau tare da sassautawa a fagen siyasa to yana iya samun biyan bukatar sa na komawa kan kujerar mulki domin ya sami damar aiwatar da manufofin sa a kan Nijeriya.

Kan mage ya waye , talakawa zasu duba su darge kafin su zabi dan takara . Ganin cewa Janar Buhari yana cikin jam'iyyar ANPP bashi ne zai sa kawai talakawa su zabi duk dan jam'iyyar ba . Da dama daga yan siyasar da suka ci gajiyar so da kauna da talakawa kewa Janar Buhari sun juya masu baya . Mafi yawa daga cikin yan siyasa sun ci amanar talakawan da suka zabe su dashi kansa Janar Buhari da suka dafa kafadar sa suka haye kan kujerar mulki.

Janar Buhari ya kasance gwarzo abin so da kauna gun talakawa a zaben 2003 , shin yana iya samun irin wancan damar a zaben 2007 ? Lokaci ne kawai zai nuna in har talakawa zasu sake fitowa kwansu da kwarkwatansu domin jefa wa Janar Buhari kuri'un su a ranar zabe.

Hazawassalam

Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com

No comments:

Post a Comment