Monday, 16 December 2013
Yadda taron ‘Dandalin Siyasa A Intanet’ ya gudana a Jihar Zamfara
A ranakun Juma’a da Asabar da suka gabata ne aka gudanar da gagarumin taron ‘Dandalin Siyasa A Intanet.’
Taron, wanda ake gudanarwa duk shekara, shi ne karo na biyar a bana kuma an gudanar da shi ne a zauren taro na Jibrin Bala Yakubu da ke birinin Gusau, Jihar Zamfara.
Tun a daren Juma’ar da ta gabata, bayan mahalarta sun gama sauka masaukinsu, sai aka taru a dakin taro na King’s City Hotel Gusau, inda aka gabatar da kwarya-kwaryan bikin maraba. Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Wakkala, ya halarci bikin da kansa. A nan ne ’yan wasan kwaikwayo na Hukumar Al’adu ta Jihar Zamfara suka gabatar da wasan kwaikwayo mai ilimantarwa. Wasan nasu ya fadakar game da muhimmancin da ke tattare da muhawara da tattaunawa game da al’amuran siyasa da kuma na al’amuran yau da kullum.
Kafin sannan, wasu daga cikin membobi da shugabannin ‘Dandalin Siyasa Na Intanet’ sun kai ziyara zuwa babban gidan yarin Gusau, inda suka gaishe da fursunoni da kuma taya su alhini. Haka kuma, sun kai irin wannan ziyara zuwa Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke garin Gusau, inda suka duba marasa lafiya da gaishe su. Daga nan ne kuma suka rankaya zuwa Asibitin Yariman Bakura da nufin gaishe da marasa lafiya. Daga bisani kuma suka yada zango a fadar mai martaba Sarkin Katsinan Gusau, domin gaisuwar ban girma.
A ranar Asabar kuwa, mahalarta sun yi wa zauren taro na Jibrin Bala Yakubu tsinke, inda nan ne aka gudanar da gagarumin taron, wanda ya fadakar, ya ilimantar kuma ya kayatar.
A yayin gabatar da jawabinsa na maraba, Shugaban Dandalin Siyasa A Intanet, Alhaji Hashim Ubale Yusuf, ya bayyana jin dadinsa a madadin ’yan dandali, musamman ga Gwamnatin Jihar Zamfara, wacce ta kasance mai masaukin mahalarta taron. Daga nan ne ya zayyana muhimman ayyukan da dandalin ya gudanar.
A taron dandalin na bana, masana sun gabatar da muhimman takardu har guda biyu, inda daga bisani mahalarta taron suka bijiro da sharhi da tsokaci da kuma tambayoyi.
Takardar farko, mai taken ‘Arewacin Najeriya Da Batun Tattaunawa Game Da Taron Makomar kasa,’ Dokta Sa’idu Ahmad Dukawa, babban malami a Jami’ar Bayero Kano ne ya gabatar da ita. Babban malamin ya yi tsokaci mai gamsarwa game da gazawar shugabanci a Najeriya, wanda haka ya haifar da matsalolin da suka hada da sace-sacen dukiyar gwamnati da hauhawar cin hanci da rashawa da sauransu da dama.
Haka kuma, ya kawo misalan wasu daga cikin matsalolin da suka kawo wa Najeriya tarnaki, kamar tashe-tashen hankula da matsalar rashin tsaro. Bisa ga haka, ya ba da misali da ta’annatin tsagerun Neja-Delta da masu yin garkuwa da mutane don amsar kudin fansa, sannan kuma ya kawo misali da barnar da ’yan Boko Haram ke aiwatarwa a Arewacin Najeriya. Daga bisani kuma ya yi tsokaci na musamman game da ita kanta Arewa da matsalolinta da abin da ya kamata ta yi idan ta je wajen taron tattauna makomar kasa.
Takarda ta biyu a wajen taron, Malam Nasiru Wada Khalil ne ya gabatar da ita, inda ya yi tsokaci tare da sharhi mai tsawo game da al’amuran kafafen sadarwa na intanet, musamman tare da kawo misalai daga majalisun yahoo na intanet a kasar Hausa ko kuma Arewa.
Malamin ya bayyana dalla-dalla irin ci gaban da aka samu, a sakamakon amfani da wannan sabuwar fasahar sadarwa, wacce ta zama gama-gari a halin yanzu. Kadan daga cikin nasarorin sun hada da cewa fasahar intanet dai tana da tasiri da isar da sako cikin kankanen lokaci. Ta hanyar fasahar, al’umma suna kara wayewa da fahimtar inda aka sa gaba. Haka kuma ya bayyana cewa, ana isar da sako ga gwamnati, wanda kuma take fahimta da sauraro, saboda tasirin kafar ta intanet.
Bayan kammala taron, an fitar da takardar bayan taro, wacce ta fitar da matsaya guda takwas, wadanda suka hada da: An bukaci gwamnoni 19 na Arewa da su dauki kwararan matakai domin magance matsalolin da ke addabar yankin. An bukaci al’ummar Arewa gaba daya, da su hada karfi da karfe, domin kawo karshen matsalolin tsaro da ke addabar yankin. Idan har yankin Arewa ya amince da ya shiga taron tattauna matsalolin kasa da ake shirin hadawa, to su hada kai su tafi da manufa guda daya. Taron ya bukaci kungiyoyin gama kai da makamantansu da su shirya gangamin wayar da kai domin fadakar da al’umma abin da ya kamata su yi, dangane da zabubbukan 2015 da ke tafe. An yi kira ga ’yan Majalisar Tarayya na Arewa da su yi tsayin daka wajen ganin ba a zartar da dokar nan da za ta dakile masu sukar gwamnati a intanet ba. Haka kuma, an yi roko na musamman ga Gwamnatin Tarayya da kuma kungiyar Malamam Jami’a Ta Najeriya, da su yi gaugawar kawo karshen yajin aiki da ake fama da shi a jami’o’in Najeriya, domin dalibai su koma bakin karatu. Dandalin kuma ya mika gaisuwar ta’aziyya ga kasar Afrika Ta Kudu saboda mutuwar dan kishin al’umma, Nelson Mandela. Daga karshe, dandalin ya mika godiya da yabawa ga Gwamnatin Jihar Zamfara, saboda daukar nauyin bakuncin taron, wanda ya zama gamsasshe.
Taron ya samu halartar muhimman mutane maza da mata da suka hada da Shugaban Majalisar Tarayya, Alhaji Aminu Waziri Tabuwal, wanda Alhaji Abdulrahman Kawu Sumaila ya wakilta. Sai Alhaji Ibrahim Wakkala, Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara da Alhaji Hashim Ubale, wanda ya kasance Shugaban ‘Dandalin Siyasa A Intanet.’
An dai tashi taron lafiya tare da kudurin cewa za a gudanar da taro na gaba a badi, a Jihar Kano.
Culled from Aminiya
http://aminiya.com.ng/index.php/adabi/4019-yadda-taron-dandalin-siyasa-a-intanet-ya-gudana-a-jihar-zamfara
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment