Saturday 7 December 2013

Tabarbarewar Mulki A Tafin Hannun Jonathan Hobbasar Dandalin Siyasa Ta Dawowa Da Kima Da Martabar Arewa

Tabarbarewar Mulki A Tafin Hannun Jonathan Hobbasar Dandalin Siyasa Ta Dawowa Da Kima Da Martabar Arewa Daga, Sharafaddeen Sidi Umar, Sokoto Gurbacewar mabanbantan al'amurra a yankin Arewacin tarayyar Nijeriya, da suka hada da: tabarbarewar shugabanci, sha'anin tsaro da ilimi, da koma baya a fannin kasuwanci da tattalin arziki, da yawaitar cin hanci da rashawa da kwan-gaba-kwan-baya a haujin noma da kiyo da yadda Arewa da 'yan Arewa suke ci gaba da zama saniyar ware a mulkin kama-karyar PDP karkashin shugaba Jonathan da sauran dinbin kalubalen da ke fuskantar Arewa na daga cikin batutuwan da al'ummar kasa za su tattauna a babban taron shekara-shekara na Dandalin Siyasa da ke Duniyar Gizo wanda za a gudanar a Gusau, babban birnin jihar Zamfara. Taron na kasa karo na biyar wanda ke da taken "Koma Bayan Arewa: Wa Ke Da Laifi? Za a gudanar da shi ne a ranakun 6 da 7 zuwa 8 ga watan Disamba. Masani ilimin harhada magunguna Hashimu Ubale Yusuf shi ne shugaban Dandalin Siyasa na kasa a jiya da yau. Wakilinmu ya ba mu labarin Dandalin Siyasa wani fitaccen Dandali ne da a farko aka asasa a yahoogroups a duniyar gizo inda jama'a da dama ke baje kolin hajar ra'ayoyinsu kan mabanbantan al'amurran da suka jibanci siyasa, zamantakewa da tattalin arziki, da sauran batutuwa da dama da suka shafi cigaban kasa da matsalolinta da ma hanyoyin magance su. Daga baya ne aka fadada shi ta hanyar buda shafin Facebook na Dandalin Siyasa. A haka ya zuwa lokacin hada wannan rahoton akwai manbobin Dandalin Siyasa na yahoogroups 1, 964 da kuma wasu manbobi 6, 733 da ke a shafin Facebook wadanda duka sun fito ne daga ko wane lungu da sakon Nijeriya, haka ma akwai manbobin da ke a sauran sassan kasashen duniya. Bugu da kari Dandali ya hada jama'a da dama daga jam'iyyun siyasa daban-daban, wadanda duka ke musayar ra'ayi tare da muhawarori masu ma'ana ba tare da amfani da zafafan kalamai kan wani ko wasu ba, kamar yadda dokar Dandali ta shata, a daya gefen tare da bin dokar kasa ta 'yancin fadin albarkacin baki. A cikin Dandalin akwai zaratan shugabannin siyasa, 'yan siyar akida, 'yan siyasar zaure da 'yan siyasar da ke iya azata ta zauna, baya ga manya, matsakaita, da kananan ma'aikatan Gwamnati, da 'yan kasuwa, da masu mulki da masu iko da 'yan Rabbana ka wadata mu, da dalibai da malamansu da sauran mabanbantan al'umma maza da mata. Mai sharhin al'amurran yau da kullum, kazalika hazikin matashi mai juriya da kwazo Shehu Mustapha Chaji ne ya assasa, ya kuma tsugunna ya haifi Dandalin shekaru biyar da suka gabata, duk kuwa da cewar a yau ba shi ne ke da hakkin mallakar Dandalin ba, amma a jiya da yau ana kallonsa a matsayin ma'assasin da ya assasa haduwar jama'a a waje daya domin tattauna lamurra daya da zummar samar da matsaya daya da za ta amfani al'umma bai daya a matsayin kasa daya al'umma daya. Domin samun nasarar taron, an kafa kwamitoci biyar wadanda za su hada hannu da karfe domin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu. Kwamitocin su ne; babban kwamitin tsare-tsare da na kudi, da na gabatar da makalu, da na tarbon baki da tsaro da kuma kwamitin yada labarai wadanda duka za su gudanar da ayyuka daban-daban. Fitaccen lauyan nan da ke da kwarewa da gogewa a aikinsa, kazalika shugaban Gidauniyar Dandali Barista Abdullahi Imam ne shugaban kwamitin tsare-tsare. Yayin da babban Janar Manaja na gidan radiyon Freedom, Umar Sa'id Tudun Wada da fitacciyar marubuciya kuma Mai Bada Shawara ta Musamman ga Gwamna Kwankwaso na jihar Kano Hon. Binta Rabi 'u Spikin, za su kasance a matsayin manbobi. Haka ma akwai Alhaji Uba Dan Zainab, Mashawarci na Musamman ga Gwamnatin Kwankwasiyya kan sha'anin wasanni, da kuma kwararriyar 'yar jarida, kuma editar mujallar Concern, Hajiya Nana A. Gwadabe. Sauran su ne; Injiya Sani Umar, da Sadik Imam, da Hajiya Jamila Sani da Ahmad Salisu Isyaku da Abdulrahman Ringim da Dakta Bashir M, da Abdulkadir Sardauna da kuma Dakta Umar Tanko Yakasai. Kwamitin kudi kuwa, Injiniya Sani Umar ne ya kasance shugaba tare da manbobi hudu da za su take masa baya, kamar yadda Umar Sa'id Tudun Wada zai jagoranci kwamitin buga makalu. Bugu da kari kwamitin tarbon baki da tsaro yana da; Uba Dan-Zainab a matsayin shugaba, yayin da Yusuf Dingyadi (Magayakin Garkuwan Sakkwato) da wasu 'yan Dandalin za su kasance manbobi. Kari da karau babban jigo a Dandali kazalika daya daga cikin jagororin da suka taka suke kuma cigaba da taka muhimmiyar rawar cigaban Dandalin Siyasa, Urwatu Bashir-Saleh zai kasance shugaban kwamitin yada labarai. A taron an tsara za a gabatar da muhimman kasidu da makalu daga bakunan masana ilimi, matsaloli da siyasar Arewa wadanda duka mahalarta taron za su amfana daga rumbun iliminsu ta yadda za a ga matsalolin Arewa a zahiri da hanyoyin magance su. A tattaunawarsa da LEADERSHIP Hausa, shugaban kwamitin yada labarai na babban taron na Gusau 2013, Urwatu Bashir-Saleh ya bayyana cewar taron ya zarce ya kuma shiga gaban sauran tarukan Dandali da suka gabata. Ga kalamansa "Wannan taron ya sha bamban da sauran tarukkan da aka gudanar a baya. Dalili taron Gusau zai yi kokarin duba kalubalen da ke gaban Arewa wanda a yanzu haka yake yi wa yankin da al'ummar yankin mummunar barazana. A lura a shekarun baya ba mu fuskanci tabarbarewar al'amurra a Arewa ba kamar wannan lokacin da muke ciki, saboda haka a yanzu za mu duba mu yi nazari tare da tankade da rairayar gano bakin zaren ta hanyar gabatar da lacca daga gurin masana ilimin siyasa da kuma bayanai daga bakin masu mulki a Arewar yau." A bisa ga yadda yake son ganin taron ya zama ya kuma kasance ya bayyana cewar "Fatarmu ita ce taron ya fito da tarin matsalolin da suka dabaibaye Arewa da yadda za a yi maganinsu. Haka ma fatarmu ce mu ga an tattauna, an yi musayar ra'ayi tare da fito da al'amurran da ke gaban yankin Arewa da batun kwato 'yancinta tare da nemo hanyar dawowa da kwarjini da marbatar yankin da aka sani a baya. Haka ma zan so taron ya zama manuniya da aika sakon musamman ga shugabanninmu." Ya bayyana. Game da hanyoyin da Dandalin ke bi wajen isar da sako ga masu rike da madafun iko; shugaban kwamitin wanda yana daya daga cikin masu kula da Dandalin Siyasa, hasalima wanda ke fadi tashin ganin lamurran Dandalin sun tafi yadda ya kamata, ya bayyana cewar "Akwai hanyoyi da yawa na isar da sako, bayar da shawara ko korafi ga Gwamnati. Daya daga cikin hanyoyin shi ne ta duniyar gizo. Kasancewar Dandalin Siyasa mahada ce da ta tattara mutane da dama, akan baiwa Gwamnati shawara akan abin da ta yi bisa kuskure ko abin da ya kamata ta yi wa al'ummarta." "Haka kuma Dandalin Siyasa yana da matukar alfanu da tasiri wajen bayar da shawarwari ga masu mulki wadanda jami'ansu da masu ba su shawara ba su hankaltar da su akai, amma a Dandali sai ka fadi ra'ayinka ko shawara kamar dai yadda dokar Nigeriya ta bayar da damar 'yancin fadin albarkacin baki. Kamar kuma yadda aka sani Dandali yana kunshe da masu ra'ayin siyasa kala-kala, hakan ya kansa a yi adawa, a fafata tare da sukar juna domin zaburarwa ga siyasar kasa da su kansu 'yan siyasar. Duka a cikin Dandalin Siyasa ne ake gayawa Gwamnati bukatu da matsalolin jama'a, musamman wadanda ba su da dama ko hanyar da za su isar da sakonsu ga Gwamnatin da take mulkarsa." To ko baya ga wannan ko akwai wani alfanu da al'umma ke amfana daga Dandalin Siyasa? Ita ce tambayar da LEADERSHIP Hausa ta yi wa matashin Bakanen ya kuma amsa da cewar "Kwarai kuwa baya ga Dandalin Siyasa na duniyar gizo, haka ma muna da Gidauniyar Tallafawa ta Dandali wadda muka kira "Dandali Foundation" wadda kuma ke da rajista da hukumar yi wa kamfanoni da kungiyoyi rajista. An kuma kafa Gidauniyar ne domin bayar da taimako da tallafawa mabukata. Daga cikin ayyukan da Gidauniyar Dandali ta sanya a gaba akwai ziyara da bayar da tallafi ga masu cutar yoyon fitsari mukan kuma ba su kyautar sutura, da sabulai da omo. Haka ma mukan bayar bayar da taimako ga daurarru a gidajen Kurkuku. Baya ga wannan a lokuta da dama Gidauniyar Dandali kan kai gudunmuwar kayan sakawa, abinci, da sutura ga mutanen da suka fuskanci ambaliyar ruwa, baya ga wannan akan kuma taimaki manbobin Dandali da suka samu kansu a wani hali na jajantawa. LEADERSHIP Hausa ta kalato cewar bisa ga ingantattun muhawarorin da ake tafkawa a Dandalin da hobbasar da manbobin Dandalin ke yi wajen fadakarwa da zaburar da masu rike da madafun ikon kan nauyin da ke kansu; Dandalin Siyasa kamar sauran takwarorinsa ya fuskanci matsaloli da kalubale, daga ciki 'yan dandatsanci sun goge Dandalin daga duniyar gizo bakidaya a 2010. Wannan bai sa zuciya ta karaya ba, domin an sake dawowa da Dandalin sabo. Haka ma wasu manbobin Dandalin da ke ganin an yi masu ba daidai ba, sun balle suka kafa wani wajen tattaunawar, duka domin a rage karfi da kuma dusashe hasken Dandalin Siyasa, wanda duk da barazana, kalaman batanci, karairayi da suka da caccaka ga shugabanni da wanda ya assasa shi ba su sanya guiwarsu ta yi sanyi ba, hasalima Dandalin Siyasa ya kara karfi tare da kara daura damarar tabbatar da shugabanci na gaskiya a tafarkin gaskiya. Wadanda ke tafiyarwa da kula da Dandalin su ne, Urwatu Bashir-Saleh da Uba Tanko Mijin-Yawa (Uba [an Zainab) da Saleh Dakata da Sadik Imam da Auwal Rimi. Sai dai akwai masu sanya alamar ayar tambayar da ke neman sanin dalilin da ya sa duka Kanawa ne ke kula da Dandalin? Ga wanda ke neman ya zama manba a Dandalin Siyasa abinda zai yi kawai shi ne aika sakon e-mail na nuna cewar yana son a saka shi a cikin manbobi zuwa ga: dandalinsiyasa-subscribe@yahoogroups.com, daga wannan shikenan za a tura masa da sakon gayyata sai ya rika samun sakonnin Dandalin ta akwatin sakonninsa. Baya ga wannan akwai ko'odinetocin Dandali a jihohi da birnin tarayya, wadanda suka hada da; Dakta Usman Muhammad (Abuja) Yusuf Dingyadi (Sakkwato) Lawan Dan'antu (Zamfara) Musa Guri (Jigawa) Yusi Bajoga (Gombe) Uba Dan Zainab (Kano) Bashir Mainasara Kurfi (Katsina) da kuma Babangida Hassan (Bauchi) A shekaru biyar da suka gabata aka fara gudanar da taron Dandalin Siyasa na farko a Kano. Daga nan sai Kaduna da Sakkwato sai Dutse a Jigawa, da kuma wanda za a yi kwanan nan a Gusau, jihar Zamfara. Duka wadannan tarukan an gudanar da su ne a karkashin jagorancin shugaban Dandali Hashimu Ubale Yusuf. Koma dai yaya ne yayin da Dandalin Siyasa ya shirya tsaf domin tattauna matsalolin Arewa a wannan babban taron, abu mafi muhimmanci shi ne akwai matukar bukatar siyasar nunin yatsu ta zama tarihi a Arewa gabanin zaben 2015, domin tunkarar zaben. Saboda dattawan Arewa, manyan 'yan siyasar Arewa, shugabannin addini, kasaitattun 'yan kasuwar Arewa da jimlatan din wadanda suka ji gishirin kai bancen sanin ilmuka daban-daban, sun yi ittifakin cewar mafita ga Arewa da 'yan Arewa ita ce a hada kai, a kuma yi kawance da sauran sassan kasa domin samun amintaccen dan takarar da zai tabbatar da hadin kan kasa, zaman lafiya da inganta rayuwar al'umma a tafarkin Sallama da Salama. Sharafaddeen Sidi Umar culled from Leadership Hausa

1 comment:

  1. http://www.fnur.bu.edu.eg/
    http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/422-2013-12-10-10-18-01
    http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/421-2013-12-10-09-48-39
    http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/419-2013-12-09-07-21-12
    http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/420-2013-12-10-09-48-38
    http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/417-2013
    http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/418-2013-12-09-07-17-28
    http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/415-2013-12-03-08-09-23
    http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/416-2013-12-03-08-25-21
    http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/413-2013-11-21-07-50-21
    http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/414-2013-11-25-09-38-30
    http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/411-2013-11-20-08-11-53
    http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/412-2014
    http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/409-2013-2014
    http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/410-2013-11-13-17-25-28
    http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/407-2013-11-09-08-51-15
    http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/408-2013-11-13-11-55-53
    http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/405-2013-11-09-08-42-05
    http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/406-2013-11-09-08-46-10
    http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/403-2013-11-09-08-25-

    ReplyDelete