Monday, 16 December 2013

Rahoto: Yadda Taron Dandalin Siyasa Ya Gudana A Zamfara

Al’ummar yankin Arewacin tarayyar Nijeriyar yau sun baje kolin hajar ra’ayoyinsu kan mabanbantan matsaloli, kalubale da kwan-gaba-kwan baya da ke addabar yankin wanda kai tsaye za a kwatanta da ukubobin mulki irin na gashin ragon layya da talakawa da al’ummar kasa ke fuskanta karkashin mulkin jam’iyyar PDP. Wannan ya biyo baya ne a babban taron Dandalin Siyasa na kasa karo na biyar da aka gudanar a Gusau birnin jihar Zamfara a makon da ya gabata a karkashin daukar nauyin Gwamnatin Abdul-aziz Yari Abubakar. A karshen taron bayan musayar ra’ayi, tattaunawa da gabatar da mukalu Dandalin Siyasa ya fitar da takardar bayan taro wadda ta yi bayani dalla-dalla kan matsayar da manbobin Dandalin suka cimma bakidaya. Taron tattunawa kan makomar kasa da Gwamnatin Tarayya ta kudiri aniyar gabatarwa ba zai samar da wata mafita ko wani gyara ga matsalolin da Nijeriya da ‘yan Nijeriya ke fuskanta ba. Dandalin ya ce taron ba ya da kowane irin alfanun da zai magance dimbin matsalolin da kasa ke fuskanta don haka suka yi kiran da a soke taron bakidaya. Bugu da kari Dandalin ya kuma yi magana kan manyan matsaloli da kalubalen da ke addabar yankin Arewa da suka had da; fatara da koma baya a fannin ilimi da tabarbarewar sha’anin tsaro da rashin cikakkiyar dama a lamurran siyasa. Haka ma wasu abubuwan da Dandalin ya cimma matsaya a kansu su ne; babu sadaukar da kai a siyasar Nijeriya, haka ma siyasar tana cikin mawuyacin halin da ke bukatar a sake daidaita lamurra. A kan wannan bayanin ya nuna bukatar da ke akwai ta zaben shugabanni nagari wadanda za su tafiyar da mulkin gaskiya a tafarkin gaskiya. Dakta Usman Muhammad, Malami a jami’ar Abuja shine ya karanta takardar bayan taron wadda a ciki kuma ta yi kira ga majalisar tarayy da ta yi fatali da batun dokar hukuntan wadanda ke suka da caccaka a dandalin sadarwa na zamani. A kan wannan bayanin ya yi kira ga masu shata dokoki daga yankin Arewa da kada su aminta a tabbatar da dokar. Baya ga wannan Dandalin ya bayyana cewar babu wani kwakkwaran amintaccen dan siyasa daya da ya samu karbuwa, goyon baya da amincewar jimlatan din al’ummar Arewa, wanda akan wannan bayanin ya nuna bisa ga bayyanar Dandalin Siyasa akwai kyakkyawan tsammanin Arewa da ‘yan Arewa za su samu ingantaccen dan takarar da zai samu karbuwa a yankin bakidaya. A jawabin da ya gabatar a matsayinsa na mai masaukin baki, Gwamna Yari ya bayyana cewar a bisa ga gazawar Gwamnatin tarayya wajen magance satar man fetur, da rabon tattalin arzikin kasa da ake yi yadda aka ga dama don haka taron tattaunawa na kasa da za a gudanar ba zai haifar da da mai ido ba ga siyasar Nijeriya. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ta bakin mataimakisa Ibrahim Wakkala. A nasa jawabin Gwamna Kwankwaso na jihar Kano shi kansa ya yi kakkausan kira ga al’ummar Arewa da su kauracewa Babban Taron na Kasa yana mai cewa “Ko kadan taron ba ya da wani amfani a garemu don haka muke kira da a kaurace masa. Baya ga wannan jagoran na Kwankwasiyya wanda Sakataren Gwamnatin jihar Kano, Rabi’u Sulaiman Bichi ya wakilta ya yabawa hobbasar kwazon Dandalin Siyasa na fadakar da shugabanni da jagororin siyasar yau kan halin ha’ula’in da al’ummar kasa suke ciki. Shugaban Dandalin Siyasa Hashimu Ubale Yusuf bai yi kasa a guiwa ba wajen bayyana yadda Dandalin ya kafu a 2008 da ‘yan manbobi kalilan, amma a yau bisa ga gamsuwa da abubuwan da ake tattaunawa an wayi gari akwai dubban manbobin Dandali na yahoogroups da nashafin Facebook. A taron an kuma aminta da karin wasu Manbobin Kwamitin Amintattu na Dandali ba ya ga wadanda ake da su. Wadanda aka tabbatar sune: Mataimakin Gwamnan Zamfara, Ibrahim Wakkala da Sakataren Gwamnatin jihar Kano, Rabi’u Bichi, da biyu daga cikin masu kula da Dandalin, Urwatu Bashir-Saleh da Uba Dan Zainab da Ahmad Sajo, daraktan yada labarai ga Gwamna Murtala Nyako na jihar Adamawa. Tun da fari gabanin ranar babban taron sai da aka fara kai ziyara a ranar jumu’a a gidan Kurkuku da gidan Marayu ta yadda Dandalin ya bayar da tallafin tufafi da kayan amfanin yau da kullum ga wadanda abin ya shafa domin tausaya masu ga halin da suke ciki tare karfafa masu guiwar samun kyakkyawar makoma a gaba. Kazalika domin neman albarkar masu albarka, haka ma an kai gaisuwar girma a gidan Mai Martaba Sarkin Katsinan Gusau. Baya ga wannan kuma a daren ranar babban taron, Gwamna Yari ya jagoranci cin liyafar musamman a fadar Gwamnatinsa a inda aka ci a ka kuma sha abincin alfarma a gidan alfarma a bisa ga bakuntar bakin mai alfarma. Baya ga wannan haka ma a ranar lahadi Kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara Ibrahim Muhammad Birnin-Magaji ya jagoranci shugabannin Dandalin a ziyarar gani da idanu kan muhimman ayyukan raya kasa da ci gaban al’umma da Gwamnatin Shehi ta gudanar a Zamfara daga 2011 da ta fara jan zaren mulk zuwa yau. Wakilinmu ya ba mu labarin Dandalin Siyasa wani fitaccen Dandali ne da a farko aka asasa a yahoogroups a duniyar gizo inda jama’a da dama ke baje kolin hajar ra’ayoyinsu kan mabanbantan al’amurran da suka jibanci siyasa, zamantakewa da tattalin arziki, da sauran batutuwa da dama da suka shafi cigaban kasa da matsalolinta da ma hanyoyin magance su. Daga baya ne aka fadada shi ta hanyar buda shafin Facebook na Dandalin Siyasa. A haka ya zuwa lokacin hada wannan rahoton akwai manbobin Dandalin Siyasa na yahoogroups 1, 964 da kuma wasu manbobi 6, 733 da ke a shafin Facebook wadanda duka sun fito ne daga ko wane lungu da sakon Nijeriya, haka ma akwai manbobin da ke a sauran sassan kasashen duniya. Bugu da kari Dandali ya hada jama’a da dama daga jam’iyyun siyasa daban-daban, wadanda duka ke musayar ra’ayi tare da muhawarori masu ma’ana ba tare da amfani da zafafan kalamai kan wani ko wasu ba, kamar yadda dokar Dandali ta shata, a daya gefen tare da bin dokar kasa ta ‘yancin fadin albarkacin baki. A cikin Dandalin akwai zaratan shugabannin siyasa, ‘yan siyar akida, ‘yan siyasar zaure da ‘yan siyasar da ke iya azata ta zauna, baya ga manya, matsakaita, da kananan ma’aikatan Gwamnati, da ‘yan kasuwa, da masu mulki da masu iko da ‘yan Rabbana ka wadata mu, da dalibai da Malamansu da sauran mabanbanta al’umma maza da mata. Fassarar Sharafaddeen Sidi Umar da Hussaini Ibrahim, Gusau. Culled from Leadership Hausa

No comments:

Post a Comment