Saturday 7 December 2013

LABARI: Ba Sai An Yi Taron Kasa Za A Gane Barayin Man Fetur Ba - Mataimakin Gwamnan Zamfara

LABARI: Ba Sai An Yi Taron Kasa Za A Gane Barayin Man Fetur Ba - Mataimakin Gwamnan Zamfara Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Malam Ibrahim Wakkala, ya bayyana rashin goyon bayan gwamnatin Zamfara kan taron tattauna makomar kasa, wanda shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kafa kwamitin neman shawara don yadda za a gudanar da taron. Ibrahim Wakkala, ya bayyana hakan a yau a jihar Zamfara, ya yin taron kasa, na kungiyar Dandalin Siyasa Online Forum, wanda ake gudanarwa a halin yanzu a J.B. Yakubu Secretariat, Gusau, inda ya ce ko kadan gwamnatin su ba ta goyon bayan gudanar da taro na tattauna makomar kasa, saboda a cewarsa ba sai an gudanar da shi ba sannan za a san matsalolin da suka dabaibaye Nijeriya, ko kuma sanin su wane ne barayin man fetur din da ake hakowa a kasar nan, domin kuwa duk sanannu ne, ba boyayyu ba. Taron karo na biyar, ya samu halartar mutane da dama da suka hada da: Malam Ibrahim Wakkala, mataimakin gwamnan Zamfara; Rabi'u Suleiman Bichi, sakataren gwamnatin jihar Kano; Hon. Abdulrahman Kawu Sumaila, dan majalisar tarayya daga Kano, da sauran su. Culled from Rariya

No comments:

Post a Comment