Monday, 16 December 2013

Jifar Shedan

Jifar Shedan Category: Mu Sha Dariya Category: Mu Sha Dariya Published on Friday, 25 October 2013 00:00 Written by Aminiya Hits: 3508 A wajan jifar shedan ne wani Bazzazagi da karambani sai ya ce shi a sama zai yi tasa jifar. Ga shi kato ne kuma baki kirin da shi, ga muni. Ya hau sama ya fara jifa ke nan sai jikkar kudinsa ta tsinke ta sullubo kasa. Gogan naku yana ganin haka, sai ya biyo abarsa suka yo kasa, yana kokarin sai ya cafki jikkarsa. Yana fadowa kasa, su kuwa alhazai sai suka ga kato a gabansu sai suka yi zaton shedan ne ya ji jifa ya bayyana a fili. Kawai sai suka ci gaba da antaya masa jifa, wasu ma har da takalmi; suna cewa: “Alugungumi, yau sai mun ga bayanka.” Shi kuwa sai ihu yake, yana cewa: “Ana insanun fi Zariya, Najeriya” (Ma’ana: Ni mutum ne dan Zariya, Najeriya). Da kyar wani Bakano ya cece shi! Daga Shehu Mustapha Chaji, Kano Culled from Aminiya http://aminiya.com.ng/index.php/mu-sha-dariya/3456-jifar-shedan

No comments:

Post a Comment