Monday, 16 December 2013

Yadda taron ‘Dandalin Siyasa A Intanet’ ya gudana a Jihar Zamfara

A ranakun Juma’a da Asabar da suka gabata ne aka gudanar da gagarumin taron ‘Dandalin Siyasa A Intanet.’ Taron, wanda ake gudanarwa duk shekara, shi ne karo na biyar a bana kuma an gudanar da shi ne a zauren taro na Jibrin Bala Yakubu da ke birinin Gusau, Jihar Zamfara. Tun a daren Juma’ar da ta gabata, bayan mahalarta sun gama sauka masaukinsu, sai aka taru a dakin taro na King’s City Hotel Gusau, inda aka gabatar da kwarya-kwaryan bikin maraba. Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Wakkala, ya halarci bikin da kansa. A nan ne ’yan wasan kwaikwayo na Hukumar Al’adu ta Jihar Zamfara suka gabatar da wasan kwaikwayo mai ilimantarwa. Wasan nasu ya fadakar game da muhimmancin da ke tattare da muhawara da tattaunawa game da al’amuran siyasa da kuma na al’amuran yau da kullum. Kafin sannan, wasu daga cikin membobi da shugabannin ‘Dandalin Siyasa Na Intanet’ sun kai ziyara zuwa babban gidan yarin Gusau, inda suka gaishe da fursunoni da kuma taya su alhini. Haka kuma, sun kai irin wannan ziyara zuwa Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke garin Gusau, inda suka duba marasa lafiya da gaishe su. Daga nan ne kuma suka rankaya zuwa Asibitin Yariman Bakura da nufin gaishe da marasa lafiya. Daga bisani kuma suka yada zango a fadar mai martaba Sarkin Katsinan Gusau, domin gaisuwar ban girma. A ranar Asabar kuwa, mahalarta sun yi wa zauren taro na Jibrin Bala Yakubu tsinke, inda nan ne aka gudanar da gagarumin taron, wanda ya fadakar, ya ilimantar kuma ya kayatar. A yayin gabatar da jawabinsa na maraba, Shugaban Dandalin Siyasa A Intanet, Alhaji Hashim Ubale Yusuf, ya bayyana jin dadinsa a madadin ’yan dandali, musamman ga Gwamnatin Jihar Zamfara, wacce ta kasance mai masaukin mahalarta taron. Daga nan ne ya zayyana muhimman ayyukan da dandalin ya gudanar. A taron dandalin na bana, masana sun gabatar da muhimman takardu har guda biyu, inda daga bisani mahalarta taron suka bijiro da sharhi da tsokaci da kuma tambayoyi. Takardar farko, mai taken ‘Arewacin Najeriya Da Batun Tattaunawa Game Da Taron Makomar kasa,’ Dokta Sa’idu Ahmad Dukawa, babban malami a Jami’ar Bayero Kano ne ya gabatar da ita. Babban malamin ya yi tsokaci mai gamsarwa game da gazawar shugabanci a Najeriya, wanda haka ya haifar da matsalolin da suka hada da sace-sacen dukiyar gwamnati da hauhawar cin hanci da rashawa da sauransu da dama. Haka kuma, ya kawo misalan wasu daga cikin matsalolin da suka kawo wa Najeriya tarnaki, kamar tashe-tashen hankula da matsalar rashin tsaro. Bisa ga haka, ya ba da misali da ta’annatin tsagerun Neja-Delta da masu yin garkuwa da mutane don amsar kudin fansa, sannan kuma ya kawo misali da barnar da ’yan Boko Haram ke aiwatarwa a Arewacin Najeriya. Daga bisani kuma ya yi tsokaci na musamman game da ita kanta Arewa da matsalolinta da abin da ya kamata ta yi idan ta je wajen taron tattauna makomar kasa. Takarda ta biyu a wajen taron, Malam Nasiru Wada Khalil ne ya gabatar da ita, inda ya yi tsokaci tare da sharhi mai tsawo game da al’amuran kafafen sadarwa na intanet, musamman tare da kawo misalai daga majalisun yahoo na intanet a kasar Hausa ko kuma Arewa. Malamin ya bayyana dalla-dalla irin ci gaban da aka samu, a sakamakon amfani da wannan sabuwar fasahar sadarwa, wacce ta zama gama-gari a halin yanzu. Kadan daga cikin nasarorin sun hada da cewa fasahar intanet dai tana da tasiri da isar da sako cikin kankanen lokaci. Ta hanyar fasahar, al’umma suna kara wayewa da fahimtar inda aka sa gaba. Haka kuma ya bayyana cewa, ana isar da sako ga gwamnati, wanda kuma take fahimta da sauraro, saboda tasirin kafar ta intanet. Bayan kammala taron, an fitar da takardar bayan taro, wacce ta fitar da matsaya guda takwas, wadanda suka hada da: An bukaci gwamnoni 19 na Arewa da su dauki kwararan matakai domin magance matsalolin da ke addabar yankin. An bukaci al’ummar Arewa gaba daya, da su hada karfi da karfe, domin kawo karshen matsalolin tsaro da ke addabar yankin. Idan har yankin Arewa ya amince da ya shiga taron tattauna matsalolin kasa da ake shirin hadawa, to su hada kai su tafi da manufa guda daya. Taron ya bukaci kungiyoyin gama kai da makamantansu da su shirya gangamin wayar da kai domin fadakar da al’umma abin da ya kamata su yi, dangane da zabubbukan 2015 da ke tafe. An yi kira ga ’yan Majalisar Tarayya na Arewa da su yi tsayin daka wajen ganin ba a zartar da dokar nan da za ta dakile masu sukar gwamnati a intanet ba. Haka kuma, an yi roko na musamman ga Gwamnatin Tarayya da kuma kungiyar Malamam Jami’a Ta Najeriya, da su yi gaugawar kawo karshen yajin aiki da ake fama da shi a jami’o’in Najeriya, domin dalibai su koma bakin karatu. Dandalin kuma ya mika gaisuwar ta’aziyya ga kasar Afrika Ta Kudu saboda mutuwar dan kishin al’umma, Nelson Mandela. Daga karshe, dandalin ya mika godiya da yabawa ga Gwamnatin Jihar Zamfara, saboda daukar nauyin bakuncin taron, wanda ya zama gamsasshe. Taron ya samu halartar muhimman mutane maza da mata da suka hada da Shugaban Majalisar Tarayya, Alhaji Aminu Waziri Tabuwal, wanda Alhaji Abdulrahman Kawu Sumaila ya wakilta. Sai Alhaji Ibrahim Wakkala, Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara da Alhaji Hashim Ubale, wanda ya kasance Shugaban ‘Dandalin Siyasa A Intanet.’ An dai tashi taron lafiya tare da kudurin cewa za a gudanar da taro na gaba a badi, a Jihar Kano. Culled from Aminiya http://aminiya.com.ng/index.php/adabi/4019-yadda-taron-dandalin-siyasa-a-intanet-ya-gudana-a-jihar-zamfara

Tuesday, 10 December 2013

Congratulations to all Dandalites!

Congratulations to all Dandalites! Once again the Dandalin Siyasa Online Forum has proved to the world that it has finally come of age. It is now established that our great forum is now an institution and which we pray will outlive us and continue to contribute positively for the development and growth of our great country. The aim of this short letter is to apologize to the management and members of Dandalin Siyasa Online Forum my inability to intentionally miss our anniversaries, last year in Dutse and the latest in Gusau. It’s due to reasons many will come to understand in future. For two years before 19-March-2008 I had the idea of starting this great forum, but Allah’s time is the best and I created the forum on the mention date. I did it out of intrest of have such group in the North then. I never knew or predict it will be what is is today, and only Allah knows the greatness it will attain. The Dandalin Siyasa of yesterday is different from how it is today. In the past many regard the forum as my personal belonging, and that may be among the reasons some were against me, but with the present dandali which many I observed regard to “ours” has passed the stage of fighting the “Owner” or plotting against the leadership. With me out of the picture I think those fighting me in the name of dandali have no one to fight or plot against. The Great Dandalin Siyasa Online Forum, am using this channel to officially inform the leadership that I will be attending all Dandalin Siyasa Online Forum Anniversaries Insha Allah as it has been proved that its now an institution not a personal belonging of Chaji or an instrument to be used by him to further any kind of agenda from next year. From numerous comments I read, the youths, elites and even states governments from Northern Nigeria have hope in Dandalin Siyasa. They look toward dandali to provide the agenda for is good governance and democracy all about. Many now believe Dandalin Siyasa can chart the roadmap for growth and development in Northern Nigeria. I will also appeal to leadership of Dandalin Siyasa to be more patience and to also tighten its belt for future challenges as profile and influence of the forum is growing by the day. As humans we are bound to make mistakes and errors and when this happens, we should as usual forgive and forget for interest of our great forum, region and country. Once again a very big thank you to our great Chairman Pharm Hashim Ubale Yusufu, Engr. Sani Umar, Urwatu Bashir Saleh, Barr. Abdullahi Imam, Engr. Muazu Magaji, Nazeer Bello, Hon. Uba Danzainab, Hon. Binta Spikin, Mohammed Alhassan (BBS), Ahmed Salisu (ASI) Dr. Umar Tanko Yakasai, Mohammed Mansur Allawee, Saleh Dakata who all rose to keep the flag of Dandalin Siyasa flying in those trying period. I will remain gratefull to you all forever and continue to pray for your success and protections from all sorts of enemies. History will remember you and our people will continue to respect you forever. Many thanks to Zamfara State Deputy Governor Malam Ibrahim Muhammad Wakkala for all what he did to Dandalin Siyasafor successful 2013 annivesary. May Allah (swt) reward him abundantly and we pray that Governor Abdulazeez Yari will handover to him embracing each other. My appreciation to Engr. Rabiu Suleiman Bichi , SSG to Kano state government for identifying with Dandalin Siyasa, May Allah (swt) reward him abundantly, amen. My appreciations to all members of the Gusau 2003 Organizing committees, all members that attended the anniversary across the country, may Allah reward them abundantly. Once again a very big thank you to you all and I pray that ,all your needs in this world and hereafter will be fulfilled by Allah (swt). Thank You Shehu Mustapha Chaji Founder ( Dandalin Siyasa Online Forum)

DANDALIN SIYASA ON-LINE FORUM RAPPATEURS REPORT ON THE 5TH ANNIVERSARY, TAGGED “GUSAU 2013” HELD ON 7TH AND 8TH DECEMBER, 2013 AT J. B. YAKUBU SECRETARIAT, GUSAU, ZAMFARA STATE.

RAPPATEURS REPORT ON DANDALIN SIYASA 5TH ANNIVERSARY IN GUSAU December 8, 2013 at 1:14pm DANDALIN SIYASA ON-LINE FORUM RAPPATEURS REPORT ON THE 5TH ANNIVERSARY, TAGGED “GUSAU 2013” HELD ON 7TH AND 8TH DECEMBER, 2013 AT J. B. YAKUBU SECRETARIAT, GUSAU, ZAMFARA STATE. Introduction: Dandalin Siyasa on-line forum which is a non-profit making and non-political organization organizes meetings on annual basis to review the forum’s achievements of the preceding year and discuss ideas, capable of moving the forum forward, burning Nsational issues, and exchanging views and opinions during the conference. Papers were presented and discussed in an open forum. The annual general meeting also paves way for members to meet outside social media. This year’s meeting takes place in Zamfara State, therefore, delegates started arriving Gusau, the capital of Zamfara State, the venue of the event on Friday the 6th December, 2013. Members visited Gusau Central Prison as well as paid courtesy call to His Royal Highness, the Emir of Katsina-Gusau and orphanage home. Gala night was held in the night at City King Hotel, Gusau. Proceedings: Saturday’s programme started with an opening prayer by Dr Ibrahim Mai Bushura at 10:52am. Thereafter, the Chairman, Local Organizing Committee, Zamfara State chaprter presented a welcome address in which he welcomed delegates to Gusau 2013 Annual General Meeting. The Right Honorable Speaker, House of Assembly, Honorable Aminu Tambuwal who was represented by Honorable Kawu Sumaila presented a goodwill message. He assured the support of the Honorable Speaker in all the activities of the forum. Earlier in his speech, the Governor of Kano State, His Excellency Engineer Rabiu Musa Kwankwaso, represented by the Secretary to Kano State Government Alhaji Rabiu Suleiman Bichi expressed appreciation in the activities of Dandali On-line forum. He used the opportunity to briefly enumerate some of the achievements of Kano State Government. At the end, the Secretary to the State Government officially tendered the Governor’s request to host next year’s general meeting in 2014. In his remarks, the National Chairman, Dandalin Siyasa On-line Forum, Pharmacist Hashimu Ubale Yusuf traced the historical development of the forum from its inception to the present time. He stated that the first meeting was held in 2009 at Mambayya House, Kano; second meeting took place at Gamji Park, Kaduna; third meeting was in Sokoto, then Dutse in Jigawa State and the fifth in Gusau, Zamfara State. According to him, as at now the forum is blessed with prominent personalities such as the Deputy Governor of Zamfara State and the Secretary to the Kano State Government among many others. The Chairman extended the forum’s appreciation to all members who contributed towards the successful hosting of Gusau 2013 Annual General Meeting. At the end, Hashim Ubale called on the members of the National Assembly to be very cautious in restraining online users to exercise their fundamental human right as enshrined in the constitution of the Federal Republic of Nigeria. Presenting his speech, the Governor of Zamfara State Alhaji Abdul-aziz Yari Abubakar who was represented by his Deputy Alhaji Ibrahim Wakkala maintains that the importance of this forum cannot be over-emphasized. He therefore, called on the members of the Dandali Foundation On-line Forum to put more efforts in ensuring that north regain its lost glory. He then highlighted some of the achievements recorded by his administration which include sales of fertilizer at subsidized price; payments of fees for qualifying examinations; feeding pupils in primary and secondary schools; and rehabilitation of both state and federal roads among others. The representative of the Governor then urged members to remain committed, united and resolute in restoration of good governance in Nigerian polity at all times. First paper presentation by Dr Sa’idu Ahmad Dukawa titled “Northern Nigeria and the Discourse on National Conference”. Major points discussed in the paper are: The myriad problems in Nigeria include corruption, insecurity, injustice, lack of infrastructure, and election malpractice among others. Major problems that are so particular in Northern Nigeria are, poverty, educational backwardness, insecurity, and illiteracy. Outlines “SWOT” - (Strength, Weaknesses, Opportunities and Threats). The analysis is indeed a food for thought for the discussions and strategy of Dandali Group. Inherent contradiction in the idea on the proposed conference by Goodluck Ebele Jonathan whether it is going to be national or sovereign. North is economically disadvantage which is as a result of leadership failure. Suggestions: Need for a collective aspiration and agenda for the region before the national conference North must ensure that the representative to the conference must be by local government not religion, region or ethnic nationalities. North must insist on Federal character before south- south can have 50% of petroleum revenue. Need for Dandali to consult all stakeholders to enlighten them on the disadvantage position of the nation. The presenter is in support of the conference since it is unavoidable. North must participate with collective agenda. Second paper presentation by Nasiru Wada Khalil titled “Virtual Communities of Interest and Political Economy of Nigeria: Remarks on the Role and Outcomes of Hausa Social Networks”. Major points discussed in the paper are: Outline various types of online Hausa social forums The existence of social media, change the people outlook about government and how they relate with their people. The paper traced the history of media usage in northern Nigeria. It explains the role of social media in society such as information sharing, education/indoctrination, means of self expression and a chance for its users to reach out. The paper argues that ethnicity, regionalism, religious differences are the major determinant of online social group members. Policy makers abhor social media because it gives unrestricted means of information gathering and exchange which is the most effective tool in bringing about transparency and accountability. Suggestions: The forum needs to be pro-active The forum needs to be focus and agenda setters for the government. There is also the need for the forum to be watchful of government influence in order to maintain their impartiality, objectivity and independent status. Comments/Contributions/Questions No patriotism in northern Nigeria. People should therefore be patriotic Selfish interest and greediness is one of the major causative agents in poor leadership particularly in northern Nigeria. Northern part is confronted with numerous problems and as such where do we go from here? We should learn how to elect qualitative leaders who would promote our aspirations. The influence of social media cannot be over- emphasized. Apart from information sharing, enlightenment and entertainment, it also contributed immensely in Middle Eastern uprisings. No consensus leader in the whole of Arewa but, with the emergence of Dandali On-line forum, there is hope for Northern Nigeria to regain its lost glory. People in the north should not be afraid to participate at the proposed national conference. People should go with open minds to discuss issues freely. Response by presenters: 1. Dr Saidu Ahmad Dukawa: Shed more light on the abundant natural and human resources endowed in the northern part especially population and economy. Those who want Nigeria to be divided from the north are responding from southern pressure. Northern leaders do not empower people like what previous leaders such as Sardauna did. They don’t want the country to be divided because they want to sustain themselves in power. Ibrahim Babangida, Abacha, Obasanjo did similar exercises to maintain power. The same thing President Ebele Jonathan has embarked upon. 2. Nasir Wada Khalil: Called on members of the forum to be very vigilant on government domination about the activities of the forum and to be wary on the postings of government activities in the forum because of their own interest. We must keep vigilant, focus and maintain our interest. Vote of Thanks Malam Umar Sa’id Tudun Wada urged members to work hard in promoting the activities of the forum. He said the postings on the forum are very encouraging, they indicate that our efforts are not wasteful. He thanked everybody for their resilience and patience throughout today’s deliberations. And this is because of the situation the north and Nigeria has found itself and the need to have solutions to our numerous problems. Lastly the Secretary to the Government of Kano State Alhaji Rabiu Suleiman Bichi said he has listened to all deliberations and he understood them perfectly but, the policy decision Kano has taken over the national dialogue not to participate has been commendable on so many grounds. Namely among which is just a waste of time and resources. Besides, there is scarcity of leadership in the north and also the followers do not believe in the leadership which is supposed to be a mutual trust between the leaders and the followers. The national dialogue has history of dividing Nigerians and the committee itself is led by questionable characters that in their past activities, they were found to have intention of dividing the country in a coup and also the committee is composed of characters that are not patriotic to Nigeria as such Kano would not participate. The South-West also indicated similar concern and General Buhari our leader, has clearly come out criticizing such fora. Other Matters Arising Four additional members were incorporated into the membership of Board of Trustees. These members are: Alhaji Ibrahim Wakkala; Alhaji Rabiu Suleiman Bichi; Senator Isah Yahaya Zarewa; and Malam Ahmed Sajo. The Deputy Governor of Zamfara State led members in prayer for Saleh Dakata who had accident and being hospitalized in Kano. Zamfara State Government is of the opinion that National Conference is not in any way the solution to the numerous national problems. Communiqué on the 5th Anniversary of Dandalin Siyasa On-line Forum, Theme “Northern Drawing Board: Who Leads The Way? Held on 7TH and 8TH December, 2013 at J. B. Yakubu Secretariat, Gusau, Zamfara State. Communiqué: At Dandali 5th anniversary forum tagged “Gusau 2013” held on 7th and 8th December, 2013, major burning national issues were identified and discussed amongst which include: Anti Cyber Proposed bill by the National Assembly; National Conference/ Dialogue and Socio-Economic Challenges bedeviling Northern Nigeria. The forum observed with regret that, the anti-cyber critic Bill, is undemocratic, unconstitutional and outright infringement on people’s fundamental freedom of self expressions in a democratic setting. As such it will and most be resisted by all concerned. On National Conference/Dialogue, the forum believed that it is never a solution to Nigeria’s socio-economic and political crisis, hence, the forum calls on National leaders to rescind the decision and be popular on policies amongst Nigerians. Major Challenges of the North were identified as poverty, lack of education, political rights, Security and Civic Education especially through social media. Other major observations noted are: No patriotism in northern Nigeria. People should therefore be patriotic Selfish interest and greediness is one of the major causative agents in poor leadership particularly in northern Nigeria. Northern part is confronted with numerous challenges, such as its political destiny. There is the need to be decisive. That North should learn how to elect qualitative leaders who would promote their needs and aspirations. The influence of social media cannot be over- emphasized. Apart from information sharing, enlightenment and entertainment, it should also be a veritable instrument of civic education for the average Northerner. No consensus leader in the whole of Arewa but, with the emergence of Dandali on-line forum, there is hope for Northern Nigeria to regain its lost glory. Based on the aforementioned observations, recommends as follows: 1. There is need for the 19 northern states to take pro-active measures in tackling socio-economic problems bedeviling the region. 2. There is need for concerted effort from all and sundry, to find a lasting solution to the lingering and deadly security problems in the region. 3. If the region must attain the up-coming national conference, there is need for the region to go with common sets of agendas. 4. As 2015 general election is approaching, we recommend massive voters education in the region. Civil societies, NGOs and government need to design robust measures in order to enlighten the general public on how to stop rigging and other mal- practices during elections. 5. We also recommend that, National Assembly members from the North must make sure the anti- cyber critic bill is not passed. We believe it is unconstitutional and undemocratic and cannot stand a taste of time. 6. We also urge both the Federal Government and ASUU to quickly resolve their differences so that students can go back to classes. 7. The forum wishes to extent its heartfelt condolence to the people of South African Government and Africa in General over the death of Nelson Mandela. 8. Lastly, the forum is immensely very grateful to the Government and people of Zamfara State for their wonderful reception and hospitality. Dr Usman Muhammad Muhammad Fatuhu Mainasara Yakubu Kurfi (Chairman) (Member) (Secretary)

Saturday, 7 December 2013

ADDRESS BY HIS EXCELLENCY, THE EXECUTIVE GOVERNOR OF ZAMFARA STATE, HONOURABLE ABDUL’AZIZ YARI ABUBAKAR, SHATTIMAN MAFARA, MADE AT THE ANNUAL NATIONAL CONFERENCE OF DANDALIN SIYASA ONLINE FORUM, ON FRIDAY 7TH DECEMBER, 2013

ADDRESS BY HIS EXCELLENCY, THE EXECUTIVE GOVERNOR OF ZAMFARA STATE, HONOURABLE ABDUL’AZIZ YARI ABUBAKAR, SHATTIMAN MAFARA, MADE AT THE ANNUAL NATIONAL CONFERENCE OF DANDALIN SIYASA ONLINE FORUM, ON FRIDAY 7TH DECEMBER, 2013 It is a source of pleasure for me to address this gathering of members of the online discussion group of Dandalin Siyasa who are here in Zamfara State for the 2013 annual conference of the group. 2. I understand that this is the 5th conference since the creation of this forum. Over the years, Dandalin Siyasa has provided an invaluable platform for evaluation of public policies and appraisal of day to day operations of governments in Nigeria. It has gained prominence for debating issues of concern to the northern part of the country, where it draws most of its membership, and the country as a whole. 3. I believe this group is driven by the passionate desire of its members for strengthening our democracy and building a prosperous Nigeria which will occupy its proper place on the continent and on the global arena. Gladly, the online activities of forums such as yours have begun to bear fruitful results. Today, more than any other time, our people have embraced the online social media as a means of drawing the attention of governments and policy makers to issues that will strengthen democratic governance and speed up development. I must therefore commend the foresight of the founding fathers of this group, Malam Shehu Mustapha Chaji along with his committed friends, which led to the formation of the group. It is my hope that it will continue to inspire leaders at different levels to be more committed to issues of development and inject in the youths who are expected to assume greater leadership responsibilities in the future skills that will help them develop a clear vision for their communities and the country. 4. I would like to call on the group to concentrate more efforts in propagating those values that would facilitate the reawakening of the north so as to regain its lost glory. There is no better time for this than now, considering the clamour from various quarters for re-evaluation of our federal system. We in the north cannot and will not play a second fiddle in the Nigerian federation. If we are to restore the glory of the region we must have a united front on crucial issues like the proposed National Conference irrespective of party, ethnic and religious differences. 5. We in Zamfara State are of the opinion that the proposed National Conference is not a panacea to the myriad of problems bedevilling our polity. We don’t need a National Conference to address the problem of acute shortage of electricity; We don’t need such conference to address the lingering crisis in our education sector. We don’t need the conference to address the nagging issue of security across the federation. A conference need not be held before we could tackle the issue of corruption in this country. We also don’t need a conference to address the issue of organised oil theft. We in fact don’t need a conference before we realise the need to be fair and transparent in sharing the revenues accruing to the Federation Account. We already have a democratic constitution and democratically elected leaders in place. 6. All we need in this country is for the leadership to be purposeful and fully alive to its responsibilities. All we need is to abide by the rules of the game; respect the provisions of the constitution and always be mindful of the fact that we are servants of our people and not their overlords. 7. As you are holding this event here in Zamfara State, it will not be out of place for me to recount to you some of the modest achievements recorded by our administration within the past two and a half years. The reason for our emphasis on provision of infrastructure is the fact that Zamfara State is basically a rural state which needs to be opened up for wider development opportunities through the provision of infrastructure. In addition to the colossal investment made by the government in roads construction, modest achievements have equally been recorded in education, health, water supply and agriculture: Zamfara State is the only state throughout the federation that sells fertilizers at a heavily subsidised rate of N1000 per bag. This policy started from the inception of our administration and we intend to sustain it throughout our tenure; Every year, the State Government spends over N400 million for payment of NECO and WAEC examination fees for all final year secondary school students of the state; In addition to completion of construction of hostels and classrooms which we inherited from the immediate past administration, our administration has rehabilitated all boarding secondary schools under the Ministry of Education and provided beds, chairs and mattresses for the students; The State Government spends an average of 188 million naira monthly for feeding of pupils and students across the state. This is in addition to provision of an average of ten thousand bags of assorted grains every month for schools; We have completed the construction of the multi million naira Yariman Bakura Specialist Hospital, Gusau; We have upgraded some Primary Health Centres across the state to the status of General Hospitals. This is in addition to construction of additional structures for the hospitals at Maru, Talata Mafara and Bakura; Our administration has rehabilitated some federal roads stretching over 222.5 kilometres across the state within the past 2 years. These roads are: Mayanchi- Anka- Daki Takwas- Gummi to Sokoto border; Gusau- Kasuwar Daji- Kaura Namoda- Dauran- Zurmi- Gidan Jaja We have constructed a number of road networks across the state: 75.9 kilometre Wanke- Danjibga- Kucheri road; 128 kilometre Magami- Dan Gulbi- Dan Kurmi- Sabon Birni- Bagega- Anka road; 75 kilometre Talata Mafara- Rini- Janbako- Boko road; 42 kilometre Tashar Awwali- Kagara- Garbadu- Sauna- Talata Mafara road; 11 Kilometre, Yandoto- Shemori- Mada road; 14.5 Gummi -Fass road; 33.5 Gummi- Gyalange- Bardoki- Gayari; Equally, under the State and Local Governments Joint Account we have embarked upon the construction of township roads across all the 14 Local Government Areas of the state. A minimum of 20 kilometres would be constructed in each Local Government. This is in addition to the urban roads already executed in Gusau and Talata Mafara. 8. Before I conclude, I would like to call on you to remain committed to your mission of bringing about social change through online activities. You should use this conference as a platform to further cement your solidarity and renew your commitment to carry on with this all important social calling. I would also like to assure you of the support of Zamfara State Government in the pursuance of your objective of promoting good governance at all times. 9. It is now my pleasure to declare this 5th National Annual Conference of Dandalin Siyasa online forum open. I wish you successful deliberations and God’s guidance throughout. 10. Thank you and wassalamu Alaikum. December 7, 2013 i

LABARI: Ba Sai An Yi Taron Kasa Za A Gane Barayin Man Fetur Ba - Mataimakin Gwamnan Zamfara

LABARI: Ba Sai An Yi Taron Kasa Za A Gane Barayin Man Fetur Ba - Mataimakin Gwamnan Zamfara Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Malam Ibrahim Wakkala, ya bayyana rashin goyon bayan gwamnatin Zamfara kan taron tattauna makomar kasa, wanda shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kafa kwamitin neman shawara don yadda za a gudanar da taron. Ibrahim Wakkala, ya bayyana hakan a yau a jihar Zamfara, ya yin taron kasa, na kungiyar Dandalin Siyasa Online Forum, wanda ake gudanarwa a halin yanzu a J.B. Yakubu Secretariat, Gusau, inda ya ce ko kadan gwamnatin su ba ta goyon bayan gudanar da taro na tattauna makomar kasa, saboda a cewarsa ba sai an gudanar da shi ba sannan za a san matsalolin da suka dabaibaye Nijeriya, ko kuma sanin su wane ne barayin man fetur din da ake hakowa a kasar nan, domin kuwa duk sanannu ne, ba boyayyu ba. Taron karo na biyar, ya samu halartar mutane da dama da suka hada da: Malam Ibrahim Wakkala, mataimakin gwamnan Zamfara; Rabi'u Suleiman Bichi, sakataren gwamnatin jihar Kano; Hon. Abdulrahman Kawu Sumaila, dan majalisar tarayya daga Kano, da sauran su. Culled from Rariya

‘Gusau is Trouping’ as the Dandalin Siyasa 5th Anniversary Activities begins today

‘Gusau is Trouping’ as the Dandalin Siyasa 5th Anniversary Activities begins today By Muhammad Sani Dandalin Siyasa Online is the first ever online political discussion forum in the Nothern Nigeria which was established on Yahoo Groups in the year 2008 by Comrade Shehu Mustapha Chaji who was for a very long time thinking a way to re-orient the Youth in our society about the true leadership. The first anniversay of Dandalin Siyaya took place in Kano in the year 2009, it was indeed a memorable event which later became a kind of general assembly, because faces has met faces; the names that people have been reading in your emails for long time now you meet in reality, that was what creates alot of enthusiasm among the members to continue the battle. However, the subsequent events in Kaduna, Sokoto and Dutse in 2010, 2011 and 2012 resepctively, were also very much encouraging due to the increasing membership and the callibre of membership which includes former Governors, Ministers, Commissioners, Politicians, Professions, Academicians and what you can not even think of; having these kind of individuals in a Forum generate alot of intellectual debates which affects the political development of the Country. The Gusau event as we are about to witness would greatly follow the trend, though when the Central Organising Committe went for a courtesy visit under the leadership of Barrister Abdullahi Imam to His Excellency the Deputy Governor of Zamfara State Malam Ibrahim Wakkala who has was an actiive member of Dandalin Siyasa Online has stated that” Insha Allah the Gusau 2013 as the event was tagged would be the best ever Dandalin Siyasa event”. The Speaker of the House of Representatives Alh. Aminu Waziri Tambuwal beside other numerous dignitaries are expected to grace the occation which includes: Garkuwan Sokoto Alh. Attahiru Bafarawa, Senator Isa Yahaya Zarewa, Alh. Rabi’u Sulaiman Bichi. Taskira,com would broadcats the event LIVE as it happens. Culled from Taskira.com

Tabarbarewar Mulki A Tafin Hannun Jonathan Hobbasar Dandalin Siyasa Ta Dawowa Da Kima Da Martabar Arewa

Tabarbarewar Mulki A Tafin Hannun Jonathan Hobbasar Dandalin Siyasa Ta Dawowa Da Kima Da Martabar Arewa Daga, Sharafaddeen Sidi Umar, Sokoto Gurbacewar mabanbantan al'amurra a yankin Arewacin tarayyar Nijeriya, da suka hada da: tabarbarewar shugabanci, sha'anin tsaro da ilimi, da koma baya a fannin kasuwanci da tattalin arziki, da yawaitar cin hanci da rashawa da kwan-gaba-kwan-baya a haujin noma da kiyo da yadda Arewa da 'yan Arewa suke ci gaba da zama saniyar ware a mulkin kama-karyar PDP karkashin shugaba Jonathan da sauran dinbin kalubalen da ke fuskantar Arewa na daga cikin batutuwan da al'ummar kasa za su tattauna a babban taron shekara-shekara na Dandalin Siyasa da ke Duniyar Gizo wanda za a gudanar a Gusau, babban birnin jihar Zamfara. Taron na kasa karo na biyar wanda ke da taken "Koma Bayan Arewa: Wa Ke Da Laifi? Za a gudanar da shi ne a ranakun 6 da 7 zuwa 8 ga watan Disamba. Masani ilimin harhada magunguna Hashimu Ubale Yusuf shi ne shugaban Dandalin Siyasa na kasa a jiya da yau. Wakilinmu ya ba mu labarin Dandalin Siyasa wani fitaccen Dandali ne da a farko aka asasa a yahoogroups a duniyar gizo inda jama'a da dama ke baje kolin hajar ra'ayoyinsu kan mabanbantan al'amurran da suka jibanci siyasa, zamantakewa da tattalin arziki, da sauran batutuwa da dama da suka shafi cigaban kasa da matsalolinta da ma hanyoyin magance su. Daga baya ne aka fadada shi ta hanyar buda shafin Facebook na Dandalin Siyasa. A haka ya zuwa lokacin hada wannan rahoton akwai manbobin Dandalin Siyasa na yahoogroups 1, 964 da kuma wasu manbobi 6, 733 da ke a shafin Facebook wadanda duka sun fito ne daga ko wane lungu da sakon Nijeriya, haka ma akwai manbobin da ke a sauran sassan kasashen duniya. Bugu da kari Dandali ya hada jama'a da dama daga jam'iyyun siyasa daban-daban, wadanda duka ke musayar ra'ayi tare da muhawarori masu ma'ana ba tare da amfani da zafafan kalamai kan wani ko wasu ba, kamar yadda dokar Dandali ta shata, a daya gefen tare da bin dokar kasa ta 'yancin fadin albarkacin baki. A cikin Dandalin akwai zaratan shugabannin siyasa, 'yan siyar akida, 'yan siyasar zaure da 'yan siyasar da ke iya azata ta zauna, baya ga manya, matsakaita, da kananan ma'aikatan Gwamnati, da 'yan kasuwa, da masu mulki da masu iko da 'yan Rabbana ka wadata mu, da dalibai da malamansu da sauran mabanbantan al'umma maza da mata. Mai sharhin al'amurran yau da kullum, kazalika hazikin matashi mai juriya da kwazo Shehu Mustapha Chaji ne ya assasa, ya kuma tsugunna ya haifi Dandalin shekaru biyar da suka gabata, duk kuwa da cewar a yau ba shi ne ke da hakkin mallakar Dandalin ba, amma a jiya da yau ana kallonsa a matsayin ma'assasin da ya assasa haduwar jama'a a waje daya domin tattauna lamurra daya da zummar samar da matsaya daya da za ta amfani al'umma bai daya a matsayin kasa daya al'umma daya. Domin samun nasarar taron, an kafa kwamitoci biyar wadanda za su hada hannu da karfe domin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu. Kwamitocin su ne; babban kwamitin tsare-tsare da na kudi, da na gabatar da makalu, da na tarbon baki da tsaro da kuma kwamitin yada labarai wadanda duka za su gudanar da ayyuka daban-daban. Fitaccen lauyan nan da ke da kwarewa da gogewa a aikinsa, kazalika shugaban Gidauniyar Dandali Barista Abdullahi Imam ne shugaban kwamitin tsare-tsare. Yayin da babban Janar Manaja na gidan radiyon Freedom, Umar Sa'id Tudun Wada da fitacciyar marubuciya kuma Mai Bada Shawara ta Musamman ga Gwamna Kwankwaso na jihar Kano Hon. Binta Rabi 'u Spikin, za su kasance a matsayin manbobi. Haka ma akwai Alhaji Uba Dan Zainab, Mashawarci na Musamman ga Gwamnatin Kwankwasiyya kan sha'anin wasanni, da kuma kwararriyar 'yar jarida, kuma editar mujallar Concern, Hajiya Nana A. Gwadabe. Sauran su ne; Injiya Sani Umar, da Sadik Imam, da Hajiya Jamila Sani da Ahmad Salisu Isyaku da Abdulrahman Ringim da Dakta Bashir M, da Abdulkadir Sardauna da kuma Dakta Umar Tanko Yakasai. Kwamitin kudi kuwa, Injiniya Sani Umar ne ya kasance shugaba tare da manbobi hudu da za su take masa baya, kamar yadda Umar Sa'id Tudun Wada zai jagoranci kwamitin buga makalu. Bugu da kari kwamitin tarbon baki da tsaro yana da; Uba Dan-Zainab a matsayin shugaba, yayin da Yusuf Dingyadi (Magayakin Garkuwan Sakkwato) da wasu 'yan Dandalin za su kasance manbobi. Kari da karau babban jigo a Dandali kazalika daya daga cikin jagororin da suka taka suke kuma cigaba da taka muhimmiyar rawar cigaban Dandalin Siyasa, Urwatu Bashir-Saleh zai kasance shugaban kwamitin yada labarai. A taron an tsara za a gabatar da muhimman kasidu da makalu daga bakunan masana ilimi, matsaloli da siyasar Arewa wadanda duka mahalarta taron za su amfana daga rumbun iliminsu ta yadda za a ga matsalolin Arewa a zahiri da hanyoyin magance su. A tattaunawarsa da LEADERSHIP Hausa, shugaban kwamitin yada labarai na babban taron na Gusau 2013, Urwatu Bashir-Saleh ya bayyana cewar taron ya zarce ya kuma shiga gaban sauran tarukan Dandali da suka gabata. Ga kalamansa "Wannan taron ya sha bamban da sauran tarukkan da aka gudanar a baya. Dalili taron Gusau zai yi kokarin duba kalubalen da ke gaban Arewa wanda a yanzu haka yake yi wa yankin da al'ummar yankin mummunar barazana. A lura a shekarun baya ba mu fuskanci tabarbarewar al'amurra a Arewa ba kamar wannan lokacin da muke ciki, saboda haka a yanzu za mu duba mu yi nazari tare da tankade da rairayar gano bakin zaren ta hanyar gabatar da lacca daga gurin masana ilimin siyasa da kuma bayanai daga bakin masu mulki a Arewar yau." A bisa ga yadda yake son ganin taron ya zama ya kuma kasance ya bayyana cewar "Fatarmu ita ce taron ya fito da tarin matsalolin da suka dabaibaye Arewa da yadda za a yi maganinsu. Haka ma fatarmu ce mu ga an tattauna, an yi musayar ra'ayi tare da fito da al'amurran da ke gaban yankin Arewa da batun kwato 'yancinta tare da nemo hanyar dawowa da kwarjini da marbatar yankin da aka sani a baya. Haka ma zan so taron ya zama manuniya da aika sakon musamman ga shugabanninmu." Ya bayyana. Game da hanyoyin da Dandalin ke bi wajen isar da sako ga masu rike da madafun iko; shugaban kwamitin wanda yana daya daga cikin masu kula da Dandalin Siyasa, hasalima wanda ke fadi tashin ganin lamurran Dandalin sun tafi yadda ya kamata, ya bayyana cewar "Akwai hanyoyi da yawa na isar da sako, bayar da shawara ko korafi ga Gwamnati. Daya daga cikin hanyoyin shi ne ta duniyar gizo. Kasancewar Dandalin Siyasa mahada ce da ta tattara mutane da dama, akan baiwa Gwamnati shawara akan abin da ta yi bisa kuskure ko abin da ya kamata ta yi wa al'ummarta." "Haka kuma Dandalin Siyasa yana da matukar alfanu da tasiri wajen bayar da shawarwari ga masu mulki wadanda jami'ansu da masu ba su shawara ba su hankaltar da su akai, amma a Dandali sai ka fadi ra'ayinka ko shawara kamar dai yadda dokar Nigeriya ta bayar da damar 'yancin fadin albarkacin baki. Kamar kuma yadda aka sani Dandali yana kunshe da masu ra'ayin siyasa kala-kala, hakan ya kansa a yi adawa, a fafata tare da sukar juna domin zaburarwa ga siyasar kasa da su kansu 'yan siyasar. Duka a cikin Dandalin Siyasa ne ake gayawa Gwamnati bukatu da matsalolin jama'a, musamman wadanda ba su da dama ko hanyar da za su isar da sakonsu ga Gwamnatin da take mulkarsa." To ko baya ga wannan ko akwai wani alfanu da al'umma ke amfana daga Dandalin Siyasa? Ita ce tambayar da LEADERSHIP Hausa ta yi wa matashin Bakanen ya kuma amsa da cewar "Kwarai kuwa baya ga Dandalin Siyasa na duniyar gizo, haka ma muna da Gidauniyar Tallafawa ta Dandali wadda muka kira "Dandali Foundation" wadda kuma ke da rajista da hukumar yi wa kamfanoni da kungiyoyi rajista. An kuma kafa Gidauniyar ne domin bayar da taimako da tallafawa mabukata. Daga cikin ayyukan da Gidauniyar Dandali ta sanya a gaba akwai ziyara da bayar da tallafi ga masu cutar yoyon fitsari mukan kuma ba su kyautar sutura, da sabulai da omo. Haka ma mukan bayar bayar da taimako ga daurarru a gidajen Kurkuku. Baya ga wannan a lokuta da dama Gidauniyar Dandali kan kai gudunmuwar kayan sakawa, abinci, da sutura ga mutanen da suka fuskanci ambaliyar ruwa, baya ga wannan akan kuma taimaki manbobin Dandali da suka samu kansu a wani hali na jajantawa. LEADERSHIP Hausa ta kalato cewar bisa ga ingantattun muhawarorin da ake tafkawa a Dandalin da hobbasar da manbobin Dandalin ke yi wajen fadakarwa da zaburar da masu rike da madafun ikon kan nauyin da ke kansu; Dandalin Siyasa kamar sauran takwarorinsa ya fuskanci matsaloli da kalubale, daga ciki 'yan dandatsanci sun goge Dandalin daga duniyar gizo bakidaya a 2010. Wannan bai sa zuciya ta karaya ba, domin an sake dawowa da Dandalin sabo. Haka ma wasu manbobin Dandalin da ke ganin an yi masu ba daidai ba, sun balle suka kafa wani wajen tattaunawar, duka domin a rage karfi da kuma dusashe hasken Dandalin Siyasa, wanda duk da barazana, kalaman batanci, karairayi da suka da caccaka ga shugabanni da wanda ya assasa shi ba su sanya guiwarsu ta yi sanyi ba, hasalima Dandalin Siyasa ya kara karfi tare da kara daura damarar tabbatar da shugabanci na gaskiya a tafarkin gaskiya. Wadanda ke tafiyarwa da kula da Dandalin su ne, Urwatu Bashir-Saleh da Uba Tanko Mijin-Yawa (Uba [an Zainab) da Saleh Dakata da Sadik Imam da Auwal Rimi. Sai dai akwai masu sanya alamar ayar tambayar da ke neman sanin dalilin da ya sa duka Kanawa ne ke kula da Dandalin? Ga wanda ke neman ya zama manba a Dandalin Siyasa abinda zai yi kawai shi ne aika sakon e-mail na nuna cewar yana son a saka shi a cikin manbobi zuwa ga: dandalinsiyasa-subscribe@yahoogroups.com, daga wannan shikenan za a tura masa da sakon gayyata sai ya rika samun sakonnin Dandalin ta akwatin sakonninsa. Baya ga wannan akwai ko'odinetocin Dandali a jihohi da birnin tarayya, wadanda suka hada da; Dakta Usman Muhammad (Abuja) Yusuf Dingyadi (Sakkwato) Lawan Dan'antu (Zamfara) Musa Guri (Jigawa) Yusi Bajoga (Gombe) Uba Dan Zainab (Kano) Bashir Mainasara Kurfi (Katsina) da kuma Babangida Hassan (Bauchi) A shekaru biyar da suka gabata aka fara gudanar da taron Dandalin Siyasa na farko a Kano. Daga nan sai Kaduna da Sakkwato sai Dutse a Jigawa, da kuma wanda za a yi kwanan nan a Gusau, jihar Zamfara. Duka wadannan tarukan an gudanar da su ne a karkashin jagorancin shugaban Dandali Hashimu Ubale Yusuf. Koma dai yaya ne yayin da Dandalin Siyasa ya shirya tsaf domin tattauna matsalolin Arewa a wannan babban taron, abu mafi muhimmanci shi ne akwai matukar bukatar siyasar nunin yatsu ta zama tarihi a Arewa gabanin zaben 2015, domin tunkarar zaben. Saboda dattawan Arewa, manyan 'yan siyasar Arewa, shugabannin addini, kasaitattun 'yan kasuwar Arewa da jimlatan din wadanda suka ji gishirin kai bancen sanin ilmuka daban-daban, sun yi ittifakin cewar mafita ga Arewa da 'yan Arewa ita ce a hada kai, a kuma yi kawance da sauran sassan kasa domin samun amintaccen dan takarar da zai tabbatar da hadin kan kasa, zaman lafiya da inganta rayuwar al'umma a tafarkin Sallama da Salama. Sharafaddeen Sidi Umar culled from Leadership Hausa