Friday, 21 May 2010

Kano 2011: Ko Takai zai taki sa’a?

Malam Salihu Sagir Takai to tantama babu kan cewa shine dan takarar gwamna karkashin jam’iyyar ANPP da Gwamna Mallam Ibrahim Shekarau ke son ya zama magajin sa a zaben 2011. Taron da kwanakin baya akayi a gidan gwamnatin jihar Kano dan kaddamar da Takai Shekarau ya fito karara yana jinjinawa wa dan takarar sa.

Kafin zancen ya fito fili kan goyon bayan Takai yan siyasa da yan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar ANPP sunyi ta koke koke da kokarin nusar da gwamna yayi adalci wajen fidda dan takara.

Takai ya kasance kwaminishinan kananan hukumomi a gwamnatin Shekarau a yanzu.Har yanzu Gwamna Shekarau bai fito ya bayyanawa al’ummar jihar Kano dalilan da yasa ya fifita Takai a kan sauran masu neman takaran gwamna ba. Kuma Shekarau na amfani da dammar sana tsaida dan takara dan sanin cewa a tsarin da muke a kai a yanzu na dimokaradiyya da wuya gwamna ya tsaida dan takara jam’iyyar sa bata tsaida shi ba.

Jam’iyyar ANPP a jihar Kano tayi farin jinin masu son takaran gwamna a karkashin ta. Cikin jiga jigan masu neman takarar sun hada da Mataimakin Gwamna Inginiya Abdullahi Tijjani Gwarzo da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya da Alhaji Sani Kawan Kofar Mata da Sheik Ibrahim Khalil da Inginiya Sarki Labaran da Sanata Mohammed Adamu Bello da Alhaji Habibu Sale Minjibir da sauran su.

A bisa tsarin jam’iyyu a kan baiwa yan takara dama in basu daidaita ba a tsakanin sub a su shiga zaben fidda gwani dan gwada kwanji a fidda wanda yayi nasara. Koken da ragowar yan takara a jam’iyyar ANPP a jihar Kano keyi kenan domin hanyar da aka dauka ga dukkanin alamu suna zargin ba za’ayi masu adalci ba.

Tuni mafi yawa daga cikin yan takarar neman gwamna a karkashin jam’iyyar ANPP a jihar Kano sun fito karara sun bayyana cewa basu amince da take taken Gwamna Shekarau na kin basu dammar su ta hanyar dankara masu Takai ba. Sanata Mohammed Bello ya fito ya bayyanawa duniya cewa in har ba’a bashi dammar sa ba to zai fice daga jam’iyyar ANPP. Haka ma ragowar yan takarar kamar Mataimakin Gwamna Inginiya Abdullahi Gwarzo da Sanata Kabiru Gaya da Alhaji Sani Lawan Kofar Mata da Alhaji Habibu Sale Minjibir sunyi Magana da muyar guda wajen kin yarda da saida Takai da mara masa baya da Gwamna Ibrahim Shekarau keyi da nusar dashi cewa rashin adalcin da ake son yin a iya kai jam’iyyar ta fadi zabe a 2011.

Amma me yasa Gwamna Shekarau ya kafe lallai Takai ne dan takarar sa? Amsa bai wuce yana ganin cewa shine wanda kila zai cigaba da manufofin gwamnatin sad a kuma kau da kai ga masu bukatar tone-tone bayan ya bar mulki ba. Ko kuma yana gain a tunanin sad a hangen nesa irin nasa Takai yafi sauran masu neman gwamnan jihar Kano nagarta da cancanta.

Suma ragowar yan takarar na gwamnan jihar Kano suna ganin cewa sun cancanta kuma sun taimakawa Shekarau a zaben 2003 da 2007. Kuma suna ganin suna da goyon baya da masoya da magoya baya da zai iya kaisu ga lashe zaben 2011.

Tsayar da Mallam Salihu Sagir Takai na fuskantar tirjiya ba wai daga yan takarar gwamna a jam’iyyar ANPP ba hard a Kansiloli da Chairmomi da Kwamishinoni da manyan jami’an gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau. Kazalika wasu yan jam’iyyar ta ANPP suna zargin Takai da rowa da rashin iya hulda da jama’a.

Shawara ga Mallam Ibrahim Shekarau in har yana son jam’iyyar sat a ANPP ta taka rawan gain a zaben 2011 ni a ganina ya kamata a matsayin sa na uba kuma jagora ya hada kan yan jam’iyyar sa. Ya kuma zama me koyi da tsarin dimokaradiyya ta hanyar baiwa kowa dammar sa . Ya bari ayi zaben fidda gwani a jam’iyyar ba tare da ana ganin hannuwan sa karara yana mara wa wani dan takara baya ba. Ya sani duk masu neman tsayawa takaran gwamna sun taimaka masa a lokacin da yake tsananin neman taimako.

Kuma Gwamna Shekarau ya san da cewa in ya matsa sai Takai to lallai aminan sa da abokan tafiyar sa a siyasa zasu iya bankarewa suma fice daga jami’iyyar ta ANPP da bat agama farfadowa daga halin da ta shiga ba sakamakon ficewar Janar Muhammadu Buhari daga jam’iyyar ba. Sannan wasu zasu iya kin ficewa daga jam’iyyar amma suyi mata zagon kasa.

Kuma Gwamna Shekarau ya tambayi kansa ko lallai ne ya sami biyan bukatun sa in Takai yayi nasarar zama gwamnan Kano a 2011? Baya duban yadda ake kwashewa tsakanin gwamnonin da suka sauka da wanda su da kansu suka tsayar har suka zaama gwamnoni masu ci a yanzu?

In Gwamna Ibrahim Shekarau ya manta to ya sani akwai jan aiki a gaban sa koda jam’iyyar sa kansu a hade kafin su iya lashe zaben 2011. A kullum jam’iyyar PDP a jihar Kano sai kara karfi take ga kuma sabuwar jam’iyyar CPC da Janar Buhari ke cikin ta da in har sun tsaida dan takaran gwamna mai nagarta suma zasu iya lashe zaben gwamna a Kano a 2011.


Tsakanin Gwamna Shekarau da Takai da masu adawa ba’a san maci tuwo ba sai miya ta kare. Ko Takai zai taki sa’a ya zama magajin Shekarau? Lokaci ne kadai zai bayyana mana.

Shehu Mustapha Chaji

shehuchaji@yahoo.com

No comments:

Post a Comment