Friday 21 May 2010

Janar Babangida na cikin tsaka- mai -wuya

Masu goyon bayan Janar Babangida suna ganin cewa a lokacinsa ya samar da ci gaba ta fannoni da dama kamar su hukumar samar da aikin yi (N.D.E),Bankin talakawa (People’s Bank),hukumar kare haddura(FRSC),hukumar raya karkara (DEFRI),hukumar wayar da kan matasa (MAMSA) gina tagwayen hanyoyi kamar na Kaduna zuwa Kano,kafa jam’iyyu da ba su kudaden tafiyar da su,hukumar wayar da kan mata (Better Life) da sauran su .

Suna ganin cewa in har Babangida ya sake dawowa bisa kujerar mulki to zaa sami ci gaba fiye da wanda aka samu a lokacin da yake mulki irin na kama karya ta soja.Kuma suna ganin cewa in shi ya bata to a ba shi dama ya zo ya gyara.

Akwai masu ganin cewa kafin ma Babangida ya fito takara ana da bukatar ya yi wa `yan Najeriya cikakken bayani game da irin rawar da gwamnatinsa ta taka wajen soke zaben June 12 , yadda aka yi da sama da Dala biliyan goma sha-biyu na rarar man fetur, gaskiyar zancen yunkurin juyin mulkin marigayi Mamman batsa da kashe shi , shigar Najeriya kungiyar O.I.C da maida huldar jakadanci da kasar Isra’ila, da kuma uwa uba karbo bashi daga bankin duniya wato I.M.F, dora Najeriya bisa tafarkin S.A.P da ake ganin shi ya karya darajar Naira da kuma jefa Najeriya a halin da take ciki a yanzu.

Amma babban abin tambaya ga shi Babangida da magoya bayansa shi ne a yaushe shi janar din ya amince da kuma yarda da tsarin dimokuradiyya? Domin a lokacin sa ya kawo tsare-tsaren da ya yi wa dimokaradiyya targade ko kuma a ce ya karyata. A lokacinsa ne jam’iyyun N.R.C da S.D.P suka gudanar da zaben fidda gwani wanda Malam Adamu Ciroma a jam’iyyar N.R.C da marigayi Janar Shehu Musa Yar’aduwa ya lashe a jam’iyyar S.D.P sai kawai ba tare da wani muhimmin bayani ba ya rushe zaben nasu.
Haka ma Babangida ya sa `yansiyasa da al’ummar kasa sake shiryawa da fitowa sabon zaben da aka tsara na shugaban kasa a inda Alhaji Bashir Tofa na jam’iyyar N.R.C da marigayi Cif M.K.O Abiola na jam’iyyar S.D.P suka tsaya takara . Ana cikin ba da rahotannin sakamakon zaben, kwatsam sai Babangida ya soke zaben ba tare da wani kwakkwaran dalili ba. Rigingimun da suka biyo baya shi ya tilasta masa sauka daga kan mulki ba da shiri ba, bayan shekara takwas.

Soke zaben June 12 ya jefa Najeriya cikin wani yanayin rikici da tashin hankalin siyasar da tun yakin basasar Najeriya ba a taba fuskantar irin wannan yanayi ba. Tirjewar da kabilar Yarbawa suka yi na an soke zaben da dan uwansu ya dauki hanyar lashewa yasa a zaben 1999 aka barwa Yarbawa su kadai suka tsaya takara wato Cif Olu Falae da Cif Olusegun Obasanjo. Sanin kowa ne yadda Janar Babangida ya taka rawa wajen ganin cewa Cif Obasanjo shi ya lashe zaben.

A shekara bakwai da Shugaba Obasanjo ya yi yana mulki, sau nawa Janar Babangida ya fito domin kare talakawa daga manufofin gwamnatin da suke takura talaka da jefa talakawa cikin halin ni-` yasu? Shin da `yan Arewa suke ta koken cewa wannan gwamnatin na danne su, Babangida ya fito ya samar masu sauki?

Janar Babangida ya shaidawa `yan Najeriya cewa babu gudu , babu ja da baya, zai fito takarar neman Shugabacin kasa a zaben 2011 . Masu nazari kan harkokin siyasa na ta tsokaci kan rawar da Janar din zai taka wanda zai iya kai shi ga samun nasara ko faduwarsa a zabe. Tun zangon farko na wa’adin Shugaba Obasanjo masoya da magoya bayan Babangida suke ta kira gare shi ya fito amma Janar din ya yi bayanin cewa shi ba zaiyi takara da Shugaba Obasanjo ba.

Wani abin murna da farin ciki shi ne cewa fitowar ire-iren su Janar Babangida na tabbatar da dorewar tsarin dimokuradiyya a wannan kasa wanda mulkin soja ya ja mata tsaiko ga ci gaba ta fanin siyasa , zamantakewa da bunkasar tattalin arzikin kasa .
Zaben 2011 ya zama kalubale ga Janar Babangida domin ya riga ya furta cewa lallai zai fito . Dole cikin abubuwa uku a sami daya , ko dai ya ki fitowa takara wanda zai tabbatar da zancen manazartan harkokin siyasa cewa Janar Babangida matsoraci ne a fagen siyasa na gwagwarmayan neman al’umma ta mara masa baya ya kaiga darewa kan kujerar mulkin Najeriya a tsarin dimokuradiyya. Kai, in har ya fito takara aka kada shi a zaben to alkadarinsa ta karye a yadda al’umma suke ganin sa a wani dodon bango mai bada tsoro. Ko in ya fito takara har ya kai ga lashe zaben to ya tabbatar wa al’ummar Najeriya da duniya baki daya cewa shi ne mutumin da ya fi tasiri a siyasar wannan karni, ba a Najeriya kadai ba, har ga Afirka gabaki daya . Kuma wannan shi zai ba shi babbar dama na gyara sunansa a tarihin siyasar Najeriya domin mutanen Najeriya da dama suna ganin shi ne ya jefa Najeriya a halin da ta tsinci kanta a ciki har yanzu.

Dabara ta rage ga mai shiga rijiya , mu talakawa fatanmu shi ne Allah Ya ba mu shugaba nagari wanda zai fidda talaka daga halin kuncin da ya sami kansa a ciki .
Shehu Mustapha Chaji

shehuchaji@yahoo.com
08038222575

No comments:

Post a Comment