Sunday 30 September 2007

TUNAWA DA RANAR KUDUS: RANAR JADDADA GOYON BAYA GA PALASTINAWA

A watan Yuli na shekarar 1979 marigayi Imamu Ruhullah al-Khomeini(r.a)ya bada fatawa ga al'ummar Musulmin duniya da masoya 'yanci da adalci na cewa kowace ranar Jumma'a ta karshen watan Ramalana ta kasance ranar Kudus. Kuma wannan fatawar ita ta canza al-kiblar gwagwarmayar Kudus da Palastinawa daga gwagwarmayar yan kasanci da Larabawa zuwa wani al'amari da ya hau kan al'ummar Musulmin duniya.

Menene Ranar Kudus? Kudus ta kasance Palastinu ga al'ummar Musulmi,ga su kuma Yahudawa ta kasance kasar Isra'ila. A kasar Kudus Masallacin al-Aksa ko Baitul-Mukaddas yake inda ya kasance al-Kibla ta farko ga Musulmi ,kuma Masallaci na uku mafi daraja bayan Ka'aba mai girma da Masallacin Manzo Muhammad(saw)dake garin Madinatun Munauwara.

Ranar Kudus ta kasance rana ta hadin kai a tsakanin Musulmin duniya domin tunkarar matsalar Kudus da ta kasance abunda ya shafi dukkan Musulmi,kuma ranar Kudus ta kasance ranar da Musulmin duniya zasu isar da sako da murya guda domin al'ummar duniya ta sani ko a sake tunatar da ita irin zaluncin da danniya da kama karya da cin mutumcin da Yahudawan kasar mamaya ta Isra'ila kewa al'ummar Palastinawa dama Musulmi musamman kasashen Musulmin dake makotaka da Isra'ila.Ranar Kudus ta kuma kasance ranar da al'ummar Musulmi zasu tattauna tare da nemo mafita game da halin da al'ummar Palastinu suka sami kan su da tono da bankado irin makirce-makircen da kasar mamaya ta Isra'ila kewa Palastinawa da al'ummar Musulmi a ko'ina cikin duniya.

Shekarun bayan yakin duniya na biyu zasu kasance a bin tunawa da jimami ba wai ga al'ummar Palastinu da Musulmi kadai ba ,a'a harma da masoya 'yanci da adalci da walwala a ko'ina cikin duniya saboda mamayar zalunci da mulkin mallaka na babakere da Isra'ila tayi wa Palastinu.Sannan labari ne sananne ta yadda kasar Isra'ila ta jera shekaru tana karkashe Palastinawa mata da yara da tsofaffi,tare da rusa masu gidaje da gonaki da makarantu da asibitoci da wuraren sana'a da tilastawa dubun dubatan Palastinawa hijira zuwa wasu kasashe .Duk da irin zaluncin keta da ta'asar da Isra'ila keta aikatawa har yanzu ,kasashen dake da'awar 'yanci da kare hakkin dan-adam da dimokaradiya ke tallafawa Isra'ila da bata cikakken kwarin gwiwa kan abinda take aikatawa na assha ga al'ummar Palastinu musamman kasar Amerika.

Ranar Kudus rana ce ta masoya yanci da adalci da zaman lafiya da daidaituwa da mutumta hakkin dan-adam a ko'ina cikin duniya wadanda suke nuna goyon bayan su ga Palastinawa da ake zalunta da kuma kokarin isar da sakon halin kakani-kayin da Palastinawa ke ciki ga wadanda basu sani ba ko kuma suka jahilci halin da Palastinawa e ciki a hannun kasar Isra'ila .Kuma ranar Kudus ta kasance ranar da al'ummar Musulmi zasu tunatar da kawunan su cewa Masallacin al-Aksa ko Baitul-Mukaddas baya karkashin kulawar su da ikon su.Kazalika Ranar Kudus ta kasance ranar da kusan shekaru ashirin al'ummar Musulmi dake da wayewa ta siyasar duniya dama wadanda ba Musulmi ba da suka tsani zalunci da danniya ke isar da sakonni ta hanyoyin da yafi yi masu sauki na isar da sakon su na Allah -wadai ga kasar mamayar Isra'ila da nema wa Palastinawa da ake zaluntagoyon baya domin al'ummar duniya su tallafa masu.

Ranar Kudus ta kasance rana ta musamman saboda ta kasance ranar da ake sake jaddada goyon baya ga al'ummar Palastinawa wanda Musulmin duniya keyi harma da masoya 'yanci a ko'ina cikin duniya.Ranar Kudus rana ce ta sake samun natsuwa a zukatan Musulmin duniya da Palastinawa kan sanin cewa dole wata rana Kudus ta komo hannun Musulmi da Palastinawa.

Mu rika tunawa da Ranar Kudus ta hanyoyin da zamu iya koda kuwa yaya yake domin mu nuna wa al'ummar Palastinawa da ake zalunta cewa muna tare da su, su kuma kasar mamaya ta Isra'ila su san da cewa bama goyon bayan ta'assar da suke aikatawa sannan muna Allah-wadai da zaluncin da suke aikatawa.Sannan mu sake jaddada muhimmancin Masallacin al-Aksa ko Baitul-Mukaddas ga Musulmin duniya.

Haza Wassalam

Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com

No comments:

Post a Comment