Saturday 6 October 2007

Badakalar kwangila :Ya wajaba Etteh Tayi Murabus!

Mace ta farko da ta fara rike mukami mafi girma a Nigeria wato Uwargida Patricia Olubunmi Etteh na shugabantar majalisar wakilai na cikin tsaka mai wuya ko kuma ace tana cikin halin dana sani saboda halin da ta tsinci kanta na badakalar zargin aringizon kwangilar kwaskwarimar gidanta da mataimakinta Hon. Babangida Nguroje da motocin alfarma guda goma sha biyu kan tsabar kudi naira miliyan dari shida da ashirin da takwas!

Kamar yadda kwamitin Idoko ya bada rahoton sa ,sun sami shugabar majalisar da laifi dunu-dumu kan zargin da ake yi mata inda kwamitin ya gano cewa ba'a ma bi tsarin daya kamata ba wajen bada kwangilolin,domin da farko ba'a tallata kwangilar ba a jaridu ,na biyu kanfanonin dake kwangilar basu da rajista da hukuma da wasu laifufukan da kwamitin ya bankado.Amma ita Uwargida Etteh ta dage kan cewa bata da laifi saboda haka ba zata amsa kiraye-kirayen da ake tayi mata ba na tayi murabus ko ta fuskanci tsigewa.

Mafi yawan 'yan Nigeria nada ra'ayin cewa a wannan halin da talakawa ke cikin bakin talauci da fatara ace an sami shugabar majalisar wakilai ta kashe zunzurutun kudi na miliyoyin nairori har sama da dari shida saboda kwaskwarimar gidaje da sayen motocin alfarma bai dace ba.Sannan wasu na ganin cewa bata ma chancanci rike mukamin ba saboda rashin gogewa da ilimi mai zurfi,saboda sana'ar data goge a kanta itace na gyran gashi!Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ne ya dankara wa 'yan Nijeriya ita saboda dalilan dashi kansa yafi kowa sani.

Tun lokacin da wasu 'yan majalisar wakilai karkashin lemar "Integrity Group" bisa jagorancin Hon.Faruk Lawan da John Halims Agoda Da Mercy Almona Isei suka shiga gwagwarmayar ganin Etteh ta rabu da kujerar ta magoya bayan ta ke zargin su da cewa suna wannan kaiwa da komowa ne saboda basu sami biyan bukatun su ba na shugabantar kwamitocin majalisar masu maiko. Shi dai Hon.Faruk Lawan shine jagoran wadanda suka tsaya har Etteh ta kujerar shugabancin majalisar wakilai an kuma wayi gari a yau shine jagoran masu son ganin bayan ta !

Bankado badakalar aringizon kwangilolin gyran gigan su Uwargida Etteh ke da wuya harkokin majalisar wakilai ya tsaya chak.Rabon majalisar ta zauna domin tattauna da tsara dokoki an kwana biyu saboda Etteh na fargaban majalisa ta zauna dan bata san yadda za'a kwashe ba. Lallai Uwargida Etteh ta tafka abun kunya da Allah-wadai ,ta kuma zubar da mutunci da kimar majalisar tarayya a idanun 'yan Nijeriya saboda haka ya zama wajibi ,ya zamo tilas tayi murabus! In kuma taki to lallai ya wajaba ga 'yan majalisar wakilai su tasa keyar ta , ta hanyar tsigewa sannan hukumomin yaki da cin hanci da almundahana suyi aikin su a kanta.

In har da gaske gwamnatin Alhaji Umaru Musa 'Yar'adua keyi na da'awar yaki da cin hanci da rub da ciki da dukiyar al'umma to su shawarce ta tayi murabus domin tana rike da mukami mai muhimmancin gaske na tsara wa kasa dokoki.Sannan zai zama wata dama ga gwamnatin na 'Yar'adua su rabu da yan amshin shatar Obasanjo da suke nema suyi wa gwamnatin sa kene-kane.

Ya kuma kamata Uwargida Etteh ta amsa kiraye-kirayen da shugabanin siyasa da addini da al'umma keyi mata na tayi murabus .Wannan kiraye -kiraye da ake yi mata ya nuna cewa a fili bata da goyon bayan 'yan Nijeriya,Sannan inda wani mutunci ko martaba da suke anin ta dashi ,to ya zube.Ita kuma a kokarinta na ganin cewa bata sauka daga kujerar ta na shugabantar majalisar waklai ba ta dauki wasu matakai da zasu kara jefa ta cikin tsaka mai wuya.Domin da farko tayi amfani da kabilanci ,inda ta kaiwa Alhaji Lamidi Adedibu ziyara shi kuma yayi maganganun neman tada zaune tsaye inda ya dangata matsalar ta da makomar kabilar 'Yarbawa.Haka kuma taso tayi amfani da addini inda ta bada umarnin masallacin dake gidanta mazauni sannan ta gina majami'a.

Ya kamata ta san da cewa ba wai 'yan Nijeriya sun tsane ta bane dan kawai tana mace ko Bayarabiya ba a'a suna ganin cewa bukatun kanta da jin dadin ta kawai shine a gaban ta.Saboda labarai dake fitowa game da ita suna nunawa ne zuwa ga almubazaranci.Tayi bikin kece raini a ranar zagayowar ranar haihuwar ta a kasar Amurka,ga kuma neman da tayi a saya mata injin tausa na miliyoyin nairori! Ga kuma wannan badakalar na kwaskwariman gida, gaidan da kwanannan Alhaji Aminu Bello Masari ya fita a cikin sa bayan zama na shekaru hudu da yayi.

Uwargida Etteh ta baiwa 'yan Nijeriya musamman mata da kabilar ta na 'Yarbawa kunya.Domin kungiyoyin mata da suka yi ta tsalle-tsalle na murnan ganin cewa hakar su ta fara cimma ruwa na ganin cewa ana damawa dasu a kololuwar siyasar Nijeriya ta basu kunya domin ta aikata abinda mazan da suka jagoranci majalisar basu aikata ba.Ta bangaren kabilar ta na 'Yarbawa ta sake dama masu lissafi domin ya sake bayyana a gare su cewa halin bera da handama da babakere bai takaita ga wasu kabila ko yankin kasar ba a'a matsala ce dake tattare da rashin adalci da rikon amana da kishin kasa.

In 'yan majalisar wakilai suka yi nasarar kawar da Etteh ko kuma taga haza tayi murabus a kashin kanta,to ya kamata suyi kyakyawan nazari bisa mahangar adalci kan wanda zaifi dacewa ya ko ta jagoranci majalisar.Cikin abubuwan da zasu duba shine na zaben wanda ake ganin cewa baya fuskantar barazanar soke zaben sa saboda tafka magudin zabe a gaban kuliya manta sabo.Da kuma duba mutumin da suke ganin cewa ba zai zama karen farauta ko dan amshin shata ga "Aso Rock"ba.Irin shugaban da suka zabar ma kan su shine madubin da al'umma zasu yi ta kollon su dashi.Misali irin shugabancin da Aljaji Ghali Umar Na'abba yayi wa majalisar wakilai a zango na farko ya bata daraja da kwarjini a idon 'yan Nijeriya da kasashen waje.Haka ma shugabancin da Alhaji Aminu Bello Masari yayi wa majalisar shi ya bata ruhin da ta sami chajin murkushe tazarce.

Lokaci yayi da Uwargida Patricia Etteh zata amsa kiran yan Nijeriya tayi murabus.Kasantuwar ta da cigaba da jagorantar majalisar wakilai ba a bin amincewa bane ga 'yan Nijeriya saboda ta bayyana tana da laifi a badakalar kwangilolin kwaskwarimar gidanta dana mataimakin ta kamar yadda rahoton kwamitin Idoko ya bayyana.Mutunci madara ne in .....

Haza Wassalam

Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com

No comments:

Post a Comment