Tuesday 18 September 2007

A BAR KOTUNA SU HALASTA ZABEN YAR'ADUA

A jawabin da Alhaji Umaru Musa Yar'adua yayi bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kasar Nijeriya ya fito karara ya amince da cewa an sami kura-kurai a zaben daya kaishi ga zama shugaban kasa .Sannan kuma rahoton kungiyoyin sa-ido da martanin da jam'iyyun adawa suka bayar bayan zaben na watan afrilu na nuni da cewa basu gamsu da zabubbukan ba.

Jam'iyyun adawa da yan takara a karkashin jam'iyyun nasu sun yi abinda ya dace , wato maimakon yanke wa kansu hukunci ta hanyar tunzura magoya bayan su , su tada zaune tsaye sai suka shigar da kararaki a gaban kotunan zabe dan neman abi masu kadin hakkin su dana magoya bayan su .Kuma wannan mataki da suka dauka ya janyo masu yabo da sam barka domin ya nuna cewa suna son zaman lafiya da kishin kasar su da toshe duk watav kofa da wasu zasu cimma burin su na siyasa.

Duk da ikirarin da tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC)Farfesa Maurice Iwu keyi na cewa zabe sam barka da kuma rahoton kungiyoyin sa-ido dasu kuma suka bada bayanan cewa ba'a taba zabe mai muni ba a duniya kamar zaben Nijeriya na wannan shekarar.To ko a nan akwai bukatar kotu ta fayyace mana tsakanin su , su wanene makaryata!

Abubuwan dake ta faruwa a kasar nan tun bayan zabe ta bangaren jam'iyyun adawa nada ban takaici musamman ta bangaren jam'iyyar adawa ta ANPP. Da farko suka fito sukayi babatun cewa an atafka magudi suka dawo suka karbi goron gayyata na shiga gwamnatin hadin kan kasa duk da cewa sun shigar da kara a gaban kotu .Sai gashi sun janye karar da suka shigar a kotu kan zaben shugaban kasa ba tare da duba irin halin matsi da takura da magoya bayan su suka shiga ba da sunan cewa dan kasa ta zauna lafiya.Haka ma bayanai nata zuwa na cewa jam'iyyar AC da dan takarar shugaban kasar ta Alhaji Atiku Abubakar na fuskantar matsin lamba kan cewa suma su janye karar da suka shigar kotu.Ko suma zasu yi amai su lashe ?

Kan dai batun janye kararaki a gaban kotunan zabe ,kafofin watsa labarai sun ruwaito yunkurin shawo kan Janar Muhammadu Buhari ya janye karar sa dake gaban kotu kan batun magudin zabe da ya gurfanar da jam'iyyar PDP da Alhaji Umaru Musa Yar'adua da Dakta Jonatan Goodluck .Inda bisa jagorancin tsohon shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari da Galadiman Katsina mai sharia Mamman Nasir da shugaban bankin First Bank Alhaji Umaru Mutallab da kuma tsohon shugaban rusheshiyar jam'iyyar DPN Alhaji Saleh Hassan suka yi zama na musamman da Janar Buhari domin shawo kan sa ya janye karar sa dake gaban kotu ,saboda suna ganin cewa ta haka za'a sami hadin kai da zaman lafiya a kasa.Ta bangaren Janar Buhari bai yi kasa a gwiwa ba wajen sanar dasu cewa zai cigaba da bin kadin shari'ar sa.

Ni a ganinav bai kamata ana tursasawa jam'iyyun adawa da yan takara su janye karar da suka shigar kotu ba.Yin haka tawaya ne ga tsarin dimokaradiya .Dole ne mu nuna wa kasashen duniya cewa da gaske muke bisa da'awar bin tsarin dimokaradiya duk da abinda wasu suka aikata a lokacin zaben wannan shekarar.Yan siyasar Nijeriya basa daukan darasi da yiwa kansu fada,amma in shari'a tayi aikin ta ,to zai zama darasi ga yan baya gun ganin cewa sun bi hanyoyin da suka dace dan zama shugabanni da wakilan al'umma.

Ina kuma kira ga shugaban kasa Alhaji Umaru Musa Yar'adua , da in da bazar sa ake rawa wajen kokarin ganin cewa an shawo kan yan adawa su janye kararakin su dake gaban kotu ,to lallai ya tsawatar ya kuma hana saboda zai nuna cewa bada gaske yake ba kan gyara batun zabe da kuma kokarin sa na tsabtace harkokin zabe. Kuma tsoron me yake ji ! Cikin biyu dole a yi abu guda wato ko kotuna su tabbatar da zaben sa ko kuma su rushe zaben suce a sake ,in yan Nijeriya sun gamsu da ayyukan da yayi a watannin da suka gabata sai su zabe shi !

Zancen magudin zabe da kararakin dake gaban kotuna sun shige zancen Arewaci ko Kabilanci ko Bangaranci ! Zance ake kan tabbatar da adalci da samar da kyakyawar turba a tarihi yayin da yan baya zasu karanci tarihin kasar nan anan gaba Dole ne a dawo da tsarin samar da shugabanci bisa turban gaskiya da adalci da rikon amana.

Duk da cewa wasu yan Nijeriya na ganin cewa Shugaba Yar'adua yayi rawan gani a wasu fannonin a watannin da yayi bisa kujerar mulki kamar samar da wadatattcen man fetur a farashi bai daya da soke cinikin matatar man fetur na Kaduna da Fatakwal da wasu kwangilolin da basa bisa ka'ida a gwamnatin baya da dakatar da korar ma'aikata dama dawo da wasun su bakin aiki da sauran su. Duk wannan bai hana wasu a cikin gida da kasashen waje daina ganin gwamnatin sa a matsayin haramtacciyar gwamnati ba! Shugaba Yar'adua na iya samar wa gwamnatin sa halacci ne kadai ta hanyar kotuna!! Masu kaiwa da komowa domin ganin an janye kararakin ba masoya na gaskiya bane ga shugaba Yar'adua!!! Gaba tafi baya yawa dan tarihi ba zai kyale duk wanda dashi aka dafa aka sha a zaben wannan shekarar ba sai in har kotu ta zartar da hukuncin ta.

Janar Buhari a yau ya kasance gwarzon dimokaradiya shi kadai tilo,ya san da cewa gwagwarmayar da yake yi na gyara al'amurran dimokaradiyya a Nijeriya a yau duk masoya cigaban dimokaradiyya na gaskiya na tare da shi .Kuma ya san da cewa ya taka matsayi na musamman a farfajiyar bunkasar dimokaradiya ba'a Nijeriya kadai ba a'a a Afrika gabaki daya.Kada ya ja da baya ya bi kadin shari'ar da ya shigar a madadin talakawan Nijeriya har kotun koli ta kasa!

Jam'iyyun adawa da suka shiga gwamnati da wadanda suka janye shari'ar da suka shigar kotu su san da cewa sun ci amanar yan jam'iyyar su da magoya bayan su.Su kuma sani cewa lallai tarihi ya tanadar masu inda zai ajiye su,kuma tabbas su saurari makoma irin ta jam'iyyar AD!

Ga talakawan Nijeriya kada mu taba yarda a maida kasar mu mai bin tsarin jam'iyya guda, kuma kada mu gaji da gwagwarmayar sai kasar mu ta shiga sahun kasashen da ake zabe na gaskiya da amana ,kasar mu ta kasance abun koyi ga kasashen Afrika da abin alfahari ga bakaken fata a ko'ina cikin duniya.

Yan siyasa a kowane jam'iyya da suka shigar da kara a kotu su cigaba da bin kadin hakkokin magoya bayan su har kotun koli.Dole ne mu hada karfi da karfe wajen dawo da martaba da mutumcin kasar mu a idon kasashen duniya.

Haza wassalam

Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com

No comments:

Post a Comment