Rahotannin rabin zango na Majalisar Dattawa dana Tarrayya na kasa sunyi nuni ga gazawar walikan mu na Arewa wajen mika kudurorin dokoki duk da miliyoyin nairorin da suke karba a matsayin albashi da alawus – alawus.
Wakilan da suka fito daga jihohin da Hausawa da Fulani suka fi yawa sunfi ragowar yan Arewa dake majalisar Tarrayya zaman dumama kujera. Kazalika, manyan yan majalisar dattawa musamman tsofaffin gwamnoni suma ba abinda suka kulla wa wadanda suke wakilta ta hanyar gabatar da kudurin dokoki.
Kafin fitowar rahotannin a kullum ka bude radiyo zakaji ance dan majalisa ko sanata me wakiltan …. Ya bada atamfofi da injinan yin taliya da Babura da shaddoji da kananan jeneratoci da kekuna da sauran su. Wadanda ake turowa gidajen rediyon, kaji suna ta alfahari da tutiyar cewa ga irin dinbin nasarorin da wakilan su ya kawo masu. Kai harma da fadin cewa wakilin nasu ya bada naira dubu goma-goma a ja jari.
Bawai ina kushe dan abinda suke rabawa yan jagaliyar su bane a’a amma menene ainihin ayyukan da suka wajabta a kansu a matsayin sun a wakilan jama’a. A tsarin dimokaradiya majalisun dattawa da wakilai suna da muhimmiyar rawan da suke takawa wajen tsara kudirorin dokokin da rayuwan yan kasa zai inganta.
Sabanin haka namu wakilan daga na Tarrayya zuwa Jihohi basa bada wakilcin daya kamata inda basa iya tantance aiyukan taimako da ihisani da aiyukan daya wajabta a kansu na tsara dokoki da kudirorin da zai inganta rayuwar yan mazabar su da kasa gabaki daya. Babu wanda zakaji a cikin su yana fadama wadanda yake wakilta wane irin dokoki suke so ya mika ga majalisa ko kuma yana ma neman shawarar su kan wasu dokoki da ake batun kafawa da ake muhawara a kansu a majalisa.
Shin wakilan mu basa tunanin nauyin dake kansu na inganta rayuwar wadanda suke wakilta ta hanyar samar da dokokin da zai inganta rayuwar su? A cikin su waye ya nemi a kafa dokar da zai hana tsadar gidajen haya ko dokar da zata hana jami’an gwamnati su daina kai ya’yan su makarantu masu zaman kansu ko dokar da zata kare hakkokin mata daga mazajen da basu da tausayi balle imani? Mafi yawan sub a wannan ne a gaban suba , sai neman kwangiloli da karban albashi da alawus masu tsoka.
Sannan mafi yawan wakilan abinda ke gaban su shine su kara aure da sayan manyan gidaje da motoci da kai iyalan su kasashen waje domin haihuwa. Sun sanda cewa a makarantun mu daga firamare zuwa jami’a babu kyakyawan yanayin bada ilimi , haka ma asibitocin mu babu magunguna da kayan aiki , ga tsadar rayuwa a kullum alhalin albashin ma’aikata bai karu ba balle ayi maganar masu kananan sana’a da marasa aikin yi da sauran su. Maimakon su sa ido wajen ganin al’amurra sun gyaru a’a sai dai susa shaddoji masu Karen tsada su shigo cikin majalisa suna zazzare ido basa iya cewa komai.
Amma me yasa wakilan mu daga nan Arewa suke zaman dumama kujera a majalisa? Kuma ta wane hanyoyi ake bi a fitar dasu takara daga ma jam’iyyun siyasa? Sannan mafi yawan su zabin jama’a ne ko a’a? Su waye suka fi cin gajiyar su a aiyuka na taimako? Saboda in ba’a sake lale ba to yankin Arewa zai cigaba da zama koma baya kan ragowar bangarorin kasar nan, domin su mafi yawan wakilan su kan je ne domin samar wa yankin su dokokin da zasu cigaba kamar yadda suka sami dokar da tasa a basu rabo mafi tsoka daga kudaden da gwamnati ke samu kan albarkatun man fetur.
Tsarin da ake bi na fitar da yan takara da zasu wakilci al'umma ba'a basu dama wajen fitar da wadanda suke ganin cewa zai iya wakiltan su bisa amana da sanin ya kamata. Wadanda ake tsayarwa sun kasance wadanda iyayen gida a siyasa suka tsayar ko wadanda yan bunburutu da yan jagaliyar siyasa suka daure wa gindi ko kuma wanda kawai ya wayi gari ya yanke hukuncin shiga siyasa dan ya sami kudi. Mafi yawan mutane da za'a tambaye su sun san yadda ake tsayar da wakilan su, zasu ce a'a.
In har da gaske yan Arewa na bukatan canji kan irin wakilan dake wakiltan su , to sai sun darje sun duba cancantar kowane dan takara a jerin masu neman wakilcin a jam'iyyu. Sannan kada su sake yarda zumudin son wani dan takaran shugaban kasa ko gwamna yasa su rufe idannun su , su kadawa wadanda basu cancanta ba kuri'a. Akwai wadanda ko fosta basu buga ba balle su fadawa mutane manufofin da zasu ai'watar in an zabe su,amma sun zama wakilai saboda wani ya goya su sun haye basa ganin koshi daya goya su da gashi.
Wakilan mu a majalisun Tarayya dana Jihohi inda gaske suke kan cewa suna wakiltan mazabar su ba kansu ba , to ya zama wajibi su bude kofofin da wadanda suke wakilta zasu san me suke ciki da kuma bada nasu shawarwarin yayin da wata muhimmiyar batu na kasa ko jiha ta taso. Ya kamata suna da ofisoshin da suke aiki ba kuma mattataran yan bangar suba. Su kuma bude shafin yanar gizo da zasu rika sanar da jama'ar su me suke ciki da kuma bada lambobin wayan su wanda koda sakon "text" ne sai wadanda suke wakilta su basu shawarwari da bukatun da suke so.
Lokaci yayi da talakawa zasu fara tantance yan kasuwa da siyasa , da masu siyasa don inganta rayuwar al'umma da kasa gabaki daya. Duk me neman kudi ya tafi kasuwa, wanda yake son bautawa al'umma , shi jama'a ya kamata su mara wa baya. Sannan tunda kusan dukkan wakilan mu basa tabuka komai, to lallai talakawa su canza su a zabe me zuwa da wasu wadanda suke ganin zasu kare muradun su.
A karshe ya kamata talakawa su san aiyukan kowane zababbe daga shugaban kasa zuwa kansila dan sanin ko yana shugabanci ko wakilci na gari. . Ka gan a gobe in mikaji wani wakili kona Tarayya kona Jiha na bugun kirji da cewa ya raba atamfofi da babura sai mu tambayeshi kudurruka da dokoki nawa ya gabatar a majalisa. A zaben 2011 duk wakilin dake neman kuri'ar mu ya fada mana wane kudurin dokoki yake da burin gabatarwa da rayuwan mu zata inganta.
Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com
Saturday, 18 July 2009
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment