Monday 6 July 2009

Ko gwamna Yuguda yaci moriyar ganga ……?

Duk me bibiyar al’amurran siyasa a Nijeriya nada masaniyar cewa Mallam Isa Yuguda gwamnan jihar Bauchi ya canza sheka daga jam’iyyar da aka zabe shi wato jam’iyyar ANPP zuwa jam’iyyar PDP. Wani dalilin da yasa canjin shekar Yuguda ya zama abin zance shine yanda a zaben 2007 jama’ar jihar Bauchi suka jajirce sai an basu wada suka zaba.

Gwagwarmayar da talakawan jihar Bauchi sukayi na ganin cewa jam’iyyar da suke mara wa baya dad an takaran gwamnan ta Mallam Isa Yuguda ya lashe zaben na 2007 wanda ake yiwa taken A Kasa A Tsare A Raka ya kasance wani zabe da talakawan Nijeriya ke tutiya dashi domin suna ganin in al’ummar Nijeriya zasu yi tsayin daka kamar jama’ar Jihar Bauchi to tabbas fasalin zabubbuka zasu sauya a Nijeriya.

Amma abinda yafi daurewa talakawan jihar Bauchi da Nijeriya kai shine yanda dare daya Yuguda yayi tsallen daya koma jam’iyyar PDP. Sanin duk me bibiyar siyasar jihar Bauchi kafin zaben na 2007 ya san cewa an azabtar da Yuguda a lokacin da yake jam’iyyar PDP saboda kawai ya nemi takarar gwamnan jihar Bauchi a karkashin jam’iyyar. A wancan lokacin tsohon gwamnan jihar Bauchi Alhaji Adamu Mu’azu yabi duk hanyoyin da zai iya wajen ganin ya hana Mallam Isa Yuguda takara a karkashin jam’iyyar PDP. Sunce shi bama dan jihar Bauchi bane ga kuma bita da kullin da yasa ya tsallake rijiya da baya a hannun yan daban dake goyon bayan tsohon gwamnan.


Wulakanci da kama karya da izgilancin da yake fuskanta a hannun yan jam’iyyar PDP a lokacin ya tilasta masa komawa jam’iyyar ANPP a lokacin. Inda su kuma suka bashi tikitin takara a matsayin dan takaran sun a gwamna. Faduwa kuma tazo dai dai da zama inda yaci albarkacin goyon bayan da Janar Muhammadu Buhari ke dashi a jihar. Duk da kumbiya-kumbiyar da tsohon gwamna Adamu Mu’azu da jam’iyyar sat a PDP sukayi na ganin cewa sun nada nasu , hakan ya fuskanci turjiya da naki inda dubun – dubatan mutane maza da mata , manya da matasa suka kaura daga gidajen su da hana kansu barci dae da rana said a aka tabbatar masu da jam’iyyar da suka zaba dad an takaranta wato Mallam Isa Yuguda.

Duk da alfaharin da jama’ar jihar Bauchi keyi na ganin karshen jam’iyyar PDP a jihar da kuma jinjinan da Janar Buhari keyi da zaben na mutanen Bauchi . Gwamna Yuguda ya shiga neman dalilai da hujjojin da zai bashi dammar tsallakewa zuwa tsohuwar jam’iyyar sat a PDP. A zancen gaskiya canjin shekar nasa ya baiwa mutane mamaki ganin yanda ya kwance way an gwagwarmayar kawo karshen mulkin PDP a jihar Bauchi a zaben 2007 zani a kasuwa.


Yamadidin d ake tayi da zancen canjin shekar gwamna Yuguda sabanin na sauran gwamnonin da suka canza sheka shine na gazawar say a shawo kan mataimakin sa Alhaji Muhammad Garba Gadi ya biyo shi zuwa jam’iyyar PDP. Turjiyar da Yuguda ya fuskanta daga Gadi shi yasa ake ganin cewa ya lashi takobin ganin bayan mataimakin nasa ta hanyar ganin cewa an tsig shi daga mukamin sa.

Kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa an baiwa kowane dan majalisar jihar ta Bauchi naira miliyan goma in har ya yarda ya sanya hannu a tsige mataimakin gwamna Garba Gadi. Kuma labaran na nuni da cewa mafi yawan yan majalisar suna tare da Gwamna Yuguda a yunkurin nasa na ganin an tsige mataimakin sa. Karfin mulki da kudi na iya sanyawa Yuguda ya gan bayan mataimakin nasa a kowane lokaci.

Amma abin tambaya anan shine in har Yuguda yayi nasaran ganin an tsige mataimakin nasa , yayi wa jam’iyyar ANPP adalci? Shin tsakanin Yuguda da Gadi wane ne yafi halalcin zama a kan kujerar sa? Sanan shin Yuguda yayi wa jama’ar jihar Bauchi adalchi kuwa? Kuma a zaben 2007 wa jama’ar Bauchi suka zaba tsakanin Yuguda da jam’iyyar ANPP? Samun amsoshin tambayoyin da aka zana na iya dora Gwamna Yuguda bisa sikeli domin ayi masa adalci.


A halin da ake ciki a yanzu ko an tsige Alhaji Muhammad Garba Gadi ko Gwamna Isa Yuguda ya hakura su kammala wa’adin zangon sun a farko tare , ya rigaya ya bayyana mataimakin nasa a matsayin wanda ake zalunta da nuna masa fin karfi. A yanayin dan’adam yakan tausayawa wanda yake ganin ana wa fin karfi. Hakan ta kasance tsakanin tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso inda ya rika takura wa Mallam Ibrahim Shekarau a wancan lokacin said a ya bar aikin gwamnati. Ko shi Gwamna Yuguda ya sami goyon bayan jama’ar jihar Bauchi ne saboda yanda suka gan an takura masa.

Tunda shi Gwamna Yuguda ya rigaya ya koma jam’iyyar PDP bai dace ace yana gallazawa mataimakin sa ba saboda yaki komawa jam’iiyar PDP ba. Ya kamata Yuguda ya sakar masa mara su kamala wa’adin su tare, tunda in zai sake tsayawa ba tare zasu sake tsayawa ba tunda ba jam’iyyar su daya ba. Kuma hakan na iya sa magoya bayan mataimakin gwamnan day an jam’iyyar ANPP su daji sanyi-sanyi kan yakan bayan da suke ganin Yuguda yayi masu.

Zaben 2011 in Allah ya kaimu shi zai bayyana tsakanin Yuguda da jam’iyyar ANPP wake da jihar Bauchi bisa hakika. Wannan zaben ne zai kawo karshen bugun kirjin da kowane bangare keyi na cewa shi aka zaba ba dayan ba.

Su kuma mutanen jihar Bauchi a lokacin za’a tabbatar da cewa abubuwan da sukayi a lokacin zaben 2007 saboda Yuguda sukayi ko kuma jam’iyyar ANPP.

Gay an majalisar jihar Bauchi suyi adalci da sanin ya kamata game da tuhume-tuhumen da aka mika masu na tsige mataimakin gwamna Alhaji Muhammad Garba Gadi daga kujerrar sa. Su kuma sani duniya kallon su tare da samar masu da gurbi a tarihi a matayin wadanda suka kasance yan amshin shata suka aiwatar da son rai bisa farashin da akayi masu suka sallama. Ko kuma masu yanci da bin hanyoyin adalci wajen yanke dukannin wani hukunci dake gaban su.

Lokaci ne kawai zai canza tunanin day an Nijeriya ke dashi kan ganin da sukewa Gwamna Isa Yuguda a matsayin wanda ya ci moriyar ganga ya yada kore. Inda wasu masu zafafawa ma ke ganin cewa yaci amanar mutanen Bauchi. Tabbas hankalin masu bibiyar siyasa a Nijeriya zai karkata ga jihar Bauchi a zaben 2011 domin ganin yadda za’a kwashe tsakanin Yuguda da jam’iyyar ANPP, a lokacin ne za’a tabbatar da ko Yuguda yaci moriyar ganga …..

Shehu Mustapha Chaji

shehuchaji@yahoo.com

No comments:

Post a Comment