Thursday 8 May 2008

Shekaru 60 na mulkin PDP: Zancen Ogulafor da kanshin gaskiya

Yerima Vincent Ogulafor , Shugaban jam’iyyar PDP na kasa a kwanananan ya sanar da yan Nijeriya cewa jam’iyyar sa zata mulki Nijeriya na tsawon shekaru 60. Zancen na Ogulafor ya janyo masa suka daga masoya bin tsarin dimokaradiyya na hakika, sannan cikin zantuttukan nasa ya nemi da Nijeriya ta kasance kasa mai bin tafarkin jam’iyya guda daya rak.
Jam’iyyar PDP ta saba da aikata wasu abubuwa daya sabawa tsarin dimokaradiyya. Kuma abin abin mamaki shine yanda suke son abubuwa su kasance haka nan yake kasancewa ko ana so ko ba’aso. Kafin tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya kamala wa’adin sa na farko, tsohon hambareren shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar ta PDP Cif Tony Anenih yayi shelar cewa babu gurbi ga wani sabanin Obasanjo dake da niyyar zama a fadan mulkin kasa ta “Aso Rock” . Haka zancen ya kasance inda PDP suka tabbatar wa yan Nijeriya cewa babu gurbi a fadar Aso Rock , kuma abubuwan da suka faru bayan haka a yau ya zama tarihi.
Obasanjo da kansa shima a lokacin yakin neman zaben 2007 ya fadi cewa zaben na 2007 zabe ne na “ko a mutu ko ayi rai”, kuma tabbas sun tabbatar wa yan Nijeriya cewa zaben na 2007 na a mutu ko ayi rai ne domin har yanzu kasar da yan kasar basu gama farfadowa da irin mamayan da PDP tayi masu ba. Koda kotunan zabe sun soke wasu zabubbukan na jam’iyyar PDP , jam’iyyar ta bayyana niyyar ta na ganin cewa yan takarar ta da aka soke zaben su, su zata sake tsayarwa dan su koma kan mukaman su, jam’iyyar ta tabbatar da haka a zaben da aka sake a jihohin Kogi da Adamawa.
Wai shin me yasa jam’iyyar PDP ke samun yadda take so ne a kullum? Shin korafe-korafen da yan Nijeriya keyi kan jam’iyyar PDP da yanda ta keta hurumin zabe a zaben 2007 da gaske suke yin ta? Sannan yan Nijeriya suna goyon bayan jam’iyyar PDP ne da yasa ita kadai ce jam’iyyar da ta wasu a ko’ina cikin kasa? Shin gwamnatin PDP ta aiwatar da ayyukan cigaban kasa ne a tsawon shekaru 9 da har yasa yan Nijeriya ke son baiwa jam’iyyar goyon bayan har na shekaru 51 masu zuwa? Lallai yanda al’amurra ke tafiya da kyar in PDP basu yi shekaru 60 suna mulki ba, sai dai in bisa hanya yan Nijeriya sun farga da sanin hakkin su na hakika a tsarin demokaradiyya da kuma samun dammar kidaya kuri’oin su kamar yadda suke.
A yanzu haka jam’iyyar ta shafe shekaru 8 tana mulki. A yanzu kuma Shugaba Umaru Musa Yar’adua ya shafe shekara 1 cikin 4 na mulkin sa a zangon farko (mance da zancen shari’ar dake gaban kotun koli), yayin da zai kamala wa’adin sa na farko jam’iyyar PDP zata ta shafe shekaru 12 tana mulki. Kuma da alamun cewa Shugaba Yar’adua zai ci moriyar gyaran kudin mulkin kasar nan inda kila ayi zancen maida wa’adin mulki zuwa zango guda na tsawon shekaru biyar ko shida , sannan dokar ta fara aiki a shekarar 2011, in ka lissafa shekaru biyar ko shida PDP zata shafe shekaru 17 ko 18 tana mulki.
Kamar yadda aka saba in Shugaba Yar’adua ya kamala wa’adin sa na zangon farko sau biyu(?) sai mulki ya koma kudu kamar yadda Obasanjo ya aiwatar a aikace. Mataimakin Shugaban kasa , Jonathan Goodluck na jira inda shima inda rabon sa ya shafe shekaru 8 a wa’adin zango biyu ko shekaru 5 ko 6 a wa’adi guda a inda a shekarar 20….., PDP zata shafe shekaru kusan 30 ko fiye tana mulki.
Zancen da Ogulafor yayi na samun tsarin jam’iyya daya rak na bisa hanya saboda jam’iyyun da ake kira na adawa a yau sun zama masu fuska biyu kuma yan amshin shatar jam’iyyar PDP . Babbar jam’iyyar adawa ta ANPP a yau ta sami kanta a halin tsaka mai wuya inda ya’yan jam’iyyar nata tururuwan fita daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar PDP, wasu kuma sun raba kafa suna makale a kan Katanga kamar gizago. Gwamna Ali Modu Sheriff na jihar Barno , ya bayyanawa Shugaba Yar’adua gaba da gaba cewa in har kotu ta soke zaben sa , to shi da magoya bayan sa zasu yiwa Yar’adua yakin neman zabe . Shi kuma tsohon gwamnan jihar Zamfara Sanata Ahmed Sani, Yeriman Bakura, cewa yayi yana da burin ya mulki Nijeriya , kuma ta shiga jam’iyyar PDP kawai ne zai iya cimma burin sa. Shi kuma Gwamna Isa Yuguda na jihar Bauchi nata kaiwa da komowa domin ganin ya auri diyar Shugaba Yar’adua, in ya cimma burin sa to da wuya ya kasance cikin yan adawa suna adawa da sirikin sa.
Jihohin Kano da Zamfara da suka kasance a sashin Arewa maso yamma shiyyar da Shugaba Yar’adua ya fito , tabbas PDP zata so ta kafa gwamnatoci a jihohin . Ta bangaren jihar Zamfara , tuni Yerima yayi alkawarin komawa jam’iyyar PDP dashi da jama’ar sa . Amma a bangaren Jihar Kano sai da yan dabaru, kuma tuni abubuwa na nuni ga irin rawar da Gwamna Ibrahim Shekarau zai so ya taka bayan ya bar mulki a shekarar 2011. Da alamu Gwamna Shekarau zai so ya taka rawa a siyasar tsakiya kamar yanda takwarorin sa a da gwamnoni sannan a yanzu sanatoci wato Saminu Turaki da Adamu Aliero . Magoya bayan Shekarau tuni suka mika amincewar su da goyon bayan su game da yadda Yar’adua ke tafiyar da kasar nan bisa ayyukan cigaba , sannan labarai nata yawo kan cewa Shekarau da Yar’adua “abokai ne na makaranta” a jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria, kuma matan su aminan juna ne, shi yasa ma matar Shekarau tana cikin sahun farko da suka fara zuwa yiwa Yar’adua murna bayan hukumar zabe tace shine ya lashe zaben 2007.
Ta bagaren jam’iyyar A.C tuni ta dare gida biyu da masu son shiga gwamnatin hadin kan kasa da masu adawa. Kuma tuni gaggan jam’iyyar keta ficewa suna komawa jam’iyyar PDP kamar su Alhaji Abubakar Rimi da Alhaji Ghali Umar Na’abba.
Inda gaske yan Nijeriya suke na son bin tsarin dimokaradiyya to da jan aiki a gaban su . A matakin farko yan Nijeriya na bukatar zabe na gaskiya a inda za’a kidaya kuri’oin su kamar yadda suke. Tsarin dimokaradiyya ya ginu ne bisa wakilci na hakika da shugabanci na gari. Magudi da murdiyar zabe da dankara wa jama’a wanda bashi suka zaba ba yayi nesa da hakikanin tsarin dimokaradiyya na gaskiya. In za’a gudanar da zabe na gaskiya yan Nijeriya basu damu ba in jam’iyyar ta PDP zata shafe shekaru 1,000 tana mulki ba wai ma shekaru 60 da Ogulafor ke fadin zasu yi ba.
Yan Nijeriya na bukatar jam’iyyun adawa na gaskiya wadanda zasu jajirce wajen adawa na gaskiya , ba wai jam’iyyun adawa dake amfani da dammar su domin cinikayya da jam’iyya mai mulki ba dan biyan bukatun kansu ba
Hazawassalam
Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com

No comments:

Post a Comment