Thursday 8 May 2008

KALUBALEN DAKE GABAN HUKUMAR FRSC

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (Federal Road Safety Commission)a bana ta cika shekaru ashirin da kafuwa . an dai kafa hukumar FRSC a lokacin mulkin Janar Ibrahim Babangida , dan ta sa ido kan tabbatar da bin dokokin hanya a kan kanana da manyan hanyoyin mu da baiwa hukumomi shawarwari kan halin da hanyoyin suke ciki , kuma inda bukatar gyara, su sanar a gyara. Suna kuma wayar da kan direbobi da sauran jama’a kan alfarnun bin dokokin hanya. Hukumar ta FRSC tayi rawar gani duk da matsalolin da take fuskanta na kunen kashi daga direbobi da kuma kasa aiwatar da shawarwarin da take bayarwa ga hukumomi kan yanayin da hanyoyi kasar ke ciki.
Kasantuwar hadurra na abubuwan hawa na kan gaba cikin jerin abubuwan dake kashe bil adama , inda itace ta tara a jerin annobar dake shekawa da mutane lahira , inda take sanadiyar mutuwan mutane a kalla miliyan daya da dubu dari biyu a shekara a kasashen duniya tare da kusan mutane miliyan hamsin dake samun raunuka.Kuma masana a fegen na ganin cewa in ba’a dauki mataki ba nan da shekarar 2020 hadurra na iya sanadiyar zama annoba ta uku da zata rika hallaka bil adama a duniya.
Matsalar hadurran abubuwan hawa ta sanya a yau da kyar ka sami wani dan Nijeriya da wani nasa bai taba gamuwa da hatsari ba wala ya rasa ransa ko ya sami rauni ko kuma ya tsallake rijiya da baya ba. Amma me yasa har yanzu matsalar dada karuwa yake duk da kokarin da hukumar FRSC keyi? Duk da cewa hanyoyin mu a yau basu da cikaken inganci, bai isa ace rashin kyawun hanyoyin kawai ke janyo yawan hadurra ba. Akwai matsaloli kamar tukin ganganci da gudu fiye da kima da kazamin lodi dake sa karuwan hadurra a kan hanyoyin mu. Sannan uwa uba sakacin hukumomi wajen ganin cewa ana bin dokokin hanya kamar yadda ya kamata.
Shin zamu cigaba ne da zuba ido karfen nasara nata kashe mana mutane saboda sakaci da rashin kula? Zamu cigaba da zuba ido ne wasu yan kunan bakin wake dan suna rike da sitari suna jefa rayukan mu cikin hatsari ? Kuma a yaushe zamu daina yarda wasu suna fakewa da kaddara bayan sun cuche mu dan rashin kula da ganganci ?
Mafi hatsari cikin mutanen dake zirga-zirga bisa hanyoyin mu sune direbobin manyan motoci daga tirela zuwa tifofi da direbobin motocin haya daga bas zuwa direbobin kananan motoci da yan achaba. A kullum kabi manyan hanyoyi sai ka tarar da hatsari wanda ke sanadiyar mutuwan jama’a . A yau in tafiya ta kama ka , to kana kan siradin mutuwa saboda halin masu tuki a kan hanyoyin mu.
Daya daga cikin sakacin hukumar FRSC itace na kasa aiwatar da dokokin hanya kamar yadda ya kamata. Wai shin ina jami’an hukumar ta FRSC suke inda kusan dukkan motocin haya dake zirga-zirga a cikin gari da masu dogon tafiya sun maida mugun lodi ko overload kamar haka dama can ya kamata a rika lodi. Duk motocin haya a yau daga bas-bas zuwa kananan motoci suna loda mutane kamar dabbobi a inda zaka tarar da karamar mota daya kamata mutane uku su zauna a baya za’a loda mutum hudu ko biyar, sannan a gaba daya kamata direba da mutum daya zasu zauna sai ka tarar an loda mutum biyu ko uku bayan shi direban !Sannan har a cikin boot suke loda fasinjoji. Balle yan bas da zasu loda mutane har kan inji , ga kaya an lafta a baya da kan motar . Manyan motoci kam kamar su Roka abun ba’a cewa komai domin ga kaya an loda har can koli sannan ga mutane da dabbobi a can koli bisa kaya.
In harda gaske hukumar FRSC keyi na da’awar suna ganin ana bin dokokin hanya to ya zama tilas , ba sani ba sabo su rika tabbatar da cewa ana bin dokokin hanya. Sannan su tabbatar da cewa duk wanda ya karya dokan hanya to lallai ya fuskanci hukunci mai tsanani. Kuma su rika bincike kan musabbabin hatsari, sannan in aka sami direba da laifin tukin ganganci ko kazamin gudu ko sakaci da sauran su to su tabbatar da cewa doka tayi aiki a kansa da kuma soke lasisin tukin sa na har abada. Inda dokokin su keda nakasu sai su nemi gyaran fuska ga dokokin dan ya basu dammar yin aikin su kamar yadda ya kamata.
Sannan al’umma nada rawa na musamman da zasu taka wajen ganin cewa an sami raguwar hadurra a hanyoyin mu , musamman Malaman addini wajen fayyace wa mabiya bin hakkin haddi . Duk yayin da aka sami wani yayi tukin ganganci ko sakacin daya kai ga rasa rayuwa ko rayuka sai kaji ance wai an yafe! Lallai a wayar da kan jama’a kan muhimmancin bin haddi wato su bi kadin hakkin su. Sannan su daina tsuke bakunan su yayin da dan kunan bakin waken kan sitari zai kaisu ga halaka suna ji suna gani , da kai koken su ga hukumomi kan mai wannan mugun hali.
Hukumar FRSC nada jan aiki a kansu na kare rayuwa da dukiyoyin yan kasa daga hannun mugayen mutane dake fakewa da sitari su hallaka yan kasa. Suna kuma da bukatar tallafi kamar yanda sauran hukumomin tsaro ke samu daga gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi da kamfanoni masu zaman kansu da sauran al’umma . Dukkan yan kasa ya kamata su tallafa wa hukumar FRSC domin ganin cewa an sami saukin samun marayu da masu takaba da nakasassu saboda kunnen kashi da mugun hali na wasu marasa tunani da rashin imani da rashin kan gado dan kawai suna tuki a kan hanyoyin mu.

Haza Wassalam
Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com

No comments:

Post a Comment