Wednesday, 19 March 2008

Vincent Ogulafor ; Ko zai sake wa tuwo suna?

Yemira Vincent Ogulafor shine sabon shugaban jam'iyyar PDP na kasa.Ya zamo shugaban jam'iyyar ne sabannin harsashen masana harkokin siyasa dake ganin za'a fafata ne tsakanin tsohon gwamnan jihar Ebonyi Sam Egwu mai samun goton bayan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da Sanata Anyim Pius Anyim tsohon shugaban majalisar dattijai dake samun goyon bayan masu adawa da Cif Olusegun Obasanjo, amma sai Ogulafor ya kasance shugaba saboda samun goyon bayan gwamnonin jam'iyyar da yayi.

Kasan tuwan jam'iyyar PDP, jam'iyyar dake mulkin kasa yan Nijeriya zasu cigaba dasa mata ido kan yadda take tafiyar da al'amurran ta.Yanda take fassara tsarin dimokaradiyya na zama abin koyi ga sauran jam'iyyun adawa.Saboda yanda ake ganin jam'iyyar PDP keyi na zama abun koyi ga sauran jam'iyyu,misali yanda ake gudanar da zaben kananan hukumomi a jihohin da take mulki na samun kwaikwayon jihohin da jam'iyyun adawa ke mulki.Kazalika yanda suke tafiyar da harkokin su na zaben fidda gwani da zaben shugabanni na zama abin koyi ga jam'iyyun adawa.

Yan Nijeriya zasu cigaba dasa ido kan yadda Ogulafor zai tafiyar da jam'iyyar musamman siyasar cikin gidan jam'iyyar inda ake dankara wa yan jam'iyya yan takara da bashi suke soba ko kuma sukama zaba ba a lokutan zabubbukan fidda gwani . Sannan za'a sa ido kan yanda zai dawo da daraja da martabar jam'iyyar a idanun yan Nijeriya. Ga talakawan, sukan danganta duk wani cuta ko fin karfi ko kwace ko babakere ko handama ga jam'iyyar PDP.

Ogulafor a baya ya kasance sakataren jam'iyyar na kasa har na tsawon shekaru shida. Sun yi hannun riga ne da tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo kan zanen tazarce a karo na uku. Ya kasance cikin yan jam'iyyar da suka ki amincewa da wannan burin na Obasanjo.

Amma abin lura game da yanda Ogulafor zai tafiyar da jam'iyyar shine na in zai iya adalci kan batutuwan da zasu taso nan gaba da suka shafi gwamnonin jam'iyyar ganin cewa su suka daura shi bisa kujeran shugabancin jam'iyyar. Shin zai yi adalci a zabubbukan fidda gwani daya shafi gwamnonin PDP dama na Shugaban kasa? Tuni har ya fito fili ya fadawa yan Nijeriya cewa zai mika wuya kashi dari har da daya ga shugaban kasa Umaru Musa Yar'adua. Irin mika wuyan da Dakta Ahmadu Ali tsohon shugaban jam'iyyar yayi ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya janyo rudanin da jam'iyyar ta sami kanta da kuma zubar da kimar kasar nan a kasashen duniya game da lamuran zabe. Mika wuyan da Ahmadu Ali yayi yasa Obasanjo yaso ya canza kundin tsarin mulkin kasar nan dan samun zango na uku da kuma yan majalisar dattijai sukayi watsi da zancen ya kiya su "yan iska". Sannan mika wuyan shi ya janyo maye gurbin yan takara da wasu daban da rudanin daya janyo kotuna na nada wadanda basu tsaya zabe ba a matsayin gwamnoni da yan majalisa saboda su suka lashe zaben fidda gwani amma akayi masu fin karfi aka daura wasu daban.

Kalubalen dake gaban Ogulafor sun hada da shin zai iya dawo da martaban jam'iyyar PDP ? Shin zai iya jagorantar yan jam'iyyar domin aiwatar da manufofin jam'iyyar dake zancen inganta rayuwan yan Nijeriya ?Sannan zai iya karkafafa karfin jam'iyya da ikon ya kan masu mukamai na gwamnati?Kuma shin zai iya jagorantar jam'iyyar ba tare da yarda wasu suna tsoma baki ba ko su mayar dashi dan amshin shatar su ba?

Akwai ayyuka masu yawan gaske a gaban Ogulafor inda gaske yake. Misali aiwatar da shawarwarin da kwamitin sulhu da tsohon mataimakin shigaban kasa Alex Ekwueme kewa shugabanci da aka ajiye rahoton a gefe, dan in anyi amfani da rahoton kwamitin watakila wasu yan jam'iyyar ada zasu komo jam'iyyar kamar yanda Alhaji Abubakar Rimi da Alhaji Ghali Umar Na'abba suka dawo jam'iyyar . Da kuma daidaita tsarin shugabancin jam'iyyar a jihohi inda wasu magoya bayan Obasanjo suka mamayeshugabancin jam'iyyar . Sannan ko zai iya taimakawa wajen amsa kiran yan jam'iyyar na dawowa da tsohon kudin tsari mulkin jam'iyyar dan raba Obasanjo da shugabantar kwamitin amintattu na jam'iyyar.

Da sannu yan Nijeriya zasu fahimci salon jagoranci irin na Ogulafor domin ta haka kawai za'a banbanta shi dasu Barnabas Gemade da Audu Ogbeh da Ahmadu Ali da a lokutan su akayi watsi da manufofin jam'iyyar aka rika gasa wa talakawa aya a hannun su, su kuma suka tsuke bakunan su har tasu ta hada su da Obasanjo.Haka kuma yan Nijeriya zasu sa masa ido su gani ko zai yi jagorancin sa bisa gaskiya da adalci da rikon amana da mutumta yan jam'iyya wanda ta haka zai iya sa yan Nijeriya su canza tunanin su bisa jam'iyyar PDP kan yadda Obasanjo ya tilasta masu suke kallon ta.

Hazawassalam

Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com

Saturday, 8 March 2008

Talakawan Nijeriya na rayuwa cikin matsi.

In banda karfin hali irin na yan Nijeriya,musamman ma talakawa ba,da sun fara begen gwamnatin baya saboda yanda a kullum rayuwar yau da kullum sai kara wahala saboda yanda kayan abinci keta kara farashi kamar kullun waina.

Talakawan Nijeriya a yau na rayuwa cikin matsi domin kullum yaje kasuwa sai ya tarar da hauhawan farashin kayayyakin masarufi da kusan kashi arba'in zuwa hamsin.Shi kuma abunda yake samu in ma yana da abinyi babu wani kari da yake samu dake tafiya dai-dai da hauhawan farashin kayayyaki.

Ta bangaren tsaro kuma har yau a tsare hanya ayi wa jama'a kwace har da raba su da rayukan su sai cigaba yake.Hanyoyin da a shekarun baya ba'a san yan fashi da makami da tare su ba, suma yan fashi na tarewa a yanzu suna yin fashi har da kisa,,kai kace ko babu jami'an tsaro a kasar.

A yau a kasar nan in talaka ya kamu da rashin lafiya to lallai kashin sa ya bushe.Tsakanin talaka da asibiti sai kallo domin ba zai iya biyan kudaden da suke cazan mara lafiya ba. Sai dai ya sha maganin gargajiya in ya dace ya warke. In kuma rashin lafiyar ya shafi tiyata ko magunguna masu tsada to sai dai in yana da hanya a nemi taimako gun jama'a ta kafofin watsa labarai ko ya kwanta a gida ya saurari mutuwa.Saboda yanda gwamnati keta zame hannuwan ta game da harkar lafiya a yau sana'ar saida maganin bature dana gargajiya da asibitoci masu zaman kansu ya zama harka mai ribar gaske.

Ilimi zamani dama na addini mai inganci yafi karfin talaka.In har kana son ya'yan ka su sami ilimi mai inganci to lallai sai suna zuwa makarantu masu zaman kansu . Sanin cewa ilimi tsani ne ga samun rayuwa mai dadi da daukaka a rayuwar duniya,kamar yadda a yau ya'yan talakawa suka sami dama mai yawa a rayuwar su har da shugabantar al'ummomin su , sai gashi a yau karatu ya gagari dan talaka. Yan boko sunyi amfani da damar da suka samu wajen hana ya'yan talakawa samun ilimi dama raba kan al'umma saboda da ya'yan talakawa da ya'yan masu shuni ba zasu taba haduwa ba ,saboda makarantun su daga firamare zuwa jami'a daban-daban ne.

Rashin aikin yi na cikin abubuwan dake cima talakawa tuwo a kwarya. Sana'oi da kasuwancin da talakawa ke tabawa sun cushe saboda yawan masu yin ta. Misali sana'ar Achaba ko Aski ko saida katin waya ko tireda ko leburanci da sauran su anyi masu yawa har ba'a iya samun na masarufi.Rashin wutar lantarki yasa kamfanoni da masana'antu masu yawa sun rufe wanda zasu iya baiwa dubbban jama'a aikin yi. Masu aikin gwamnati ko manya kamfanoni na cikin fargaba a kullum na rasa aiyukan su,saboda kila a cigaba da raba mutane da aikin su kamar a lokacin gwamnatin baya.

A lokutan zabe tuni talakan Nijeriya kuri'ar sa ta rasa muhimmanci saboda wanda zai zaba daban ,wanda za'a dankara masa daban.Da zabe ya gabato sai shugabanin kasa dana gargajiya dana addini su fito suna umartan talakawa su fito zabe, talakawa kan amsa kiran su ,su fito mazan su da matan su su yi zabe. Amma abin takaici shine sai a tafka magudi sannan a fito a fada masu cewa cin zabe ta haramtacciyar hanya daga Allah ne ! Saboda halin ya bunburutun siyasa na rubda ciki da kuri'oin talakawa lallai talakawa zasu sake tunani a zabubbukan gaba nasu daina zabe gaba daya domin babu bukatar fitowa su bata lokacin su.

Duk da halin matsin rayuwa da talaka ya sami kansa a yau na tsadan kayayyakin masarufi babu wani malamin addini ko basaraken gargajiya ko kungiyoyin bangaranci ko shugabanin siyasa daga shugaban kasa zuwa kansila daya nemi a kawo wa talaka dauki, in ma sunyi magana to dogon turanci ne dama yin shiru shi yafi. Yanda yan amshin shatar gwamnati ke fitowa dan kalubalantar masu neman hakkin su , basa iya fitowa su fadawa gwamnati cewa yunwa na neman kassara talakawa domin tsadar abinci ya wuce hankali.

Rainin hankali da wulakancin da ake yiwa talakawan Nijeriya zai cigaba in har suka kasa banbance adalci da kabilanci da bangaranci. Cikin dabarun da masu mulkin kasar nan ke amfani da ita wajen cigaba da danne su shine na canza taku da zarar talakawa zasu gane, wato tsarin mulkin karba -karba,alhalin su masu mulki dodo daya suke yiwa tsafi. In talakawa zasu cigaba da yarda da zancen mulki yankin su ko kuma wanda suke addini daya dashi ba tare da lura da cancantar sa da hanyar daya ya zama mai mulki ba ,to za'a dade ana shan wahala.

Lokaci kuma yayi da talakawan Nijeriya zasu daina yarda ana mai dasu mara yanci a kasar su ta haihuwa. Kad su gaza ga neman hakkokin su da tsarin mulkin kasa ya basu bisa dokar kasa. Kada su yarda da farfagandar da ake yadawa na cewa Nijeriya ba zata taba gyaruwa ba, mu fara da gyara tunanin mu na cewa Nijeriya zata gyaru kuma tama fi wasu kasashen duniya dake da'awar cigaba. Kowa ya sani matsalar Nijeriya na rashin samun kyakyawan shugabanci ne, duk ranar da tayi dace da shugaba mai kishin al'ummar sa , mai magana daya , wanda ya zama shugaba bisa halartacciyar hanya, jarumi ba matsoraci ba , to lallai kasar mu zata cigaba.

Kuma talakawa su gane dabarun masu mulkin kasar nan na wofitar da tunanin mutane na yanda nan gaba in lokacin zabe yazo zasu ci karen su babu babbaka. A gobe za'a sake zabe talakawa su fito zabe su kuma yi iyakar iyawan su wajen ganin anyi zabe na gaskiya kamar yadda ta kasance a wasu jihohi a zabubbukan baya..In suka yarda suka mika wuya ta hanyar kin fitowa zabubbuka a nan gaba to zasu cigaba da zama karkashin mulkin fin karfi da sunan dimokaradiyya.

Hakki ne daya rataya akan talakawan Nijeriya su taka wa yan cuwa-cuwan siyasa burki dan cigaban kasar mu. In har talakawa zasu yarda a saye su kan naira dari biyu da sabulan wanki , to basu yiwa kansu da kasar su adalci ba.Ko'ina cikin duniya ana ta cigaba musamman kasashe masu albarkatun man fetur da dangogin sa inda abincin talaka shine shinkafa da madara da kaji, amma mu a kasar mu duk da arzikin mu garin kwaki da tuwon hatsi na gagaran talaka sau uku a rana. Yan siyasar mu har gobe cigaban gwamnatocin su shine gina kwalbatoci da rijiyoyi da rumfuna!

Wajibi ne ga talakawan Nijeriya su tashi tsaye dan a basu hakkokin su da tsarin mulkin kasa ya basu. Kin yin haka zai sa su kasance cikin rayuwan kaskanci da rayuwa maras tabbas ga ya'yan su da jikokin su. Bamu da wata kasa data wuce Nijeriya saboda haka dole mu tsaya mu ceche ta dan kawunan mu da bayan mu.

Hazawassalam

Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com