Thursday, 20 March 2014

Majalisar Siyasa ta intanet ta karrama ’ya’yanta

Bashir Yahuza Malumfashi, a Kaduna A ranar Asabar ta makon jiya ce majalisar nan da ake kira da suna Dandalin Siyasa, wacce ke tattauna al’amuran siyasa a intanet ta gudanar da taronta na shekara-shekara, inda ta karrama hudu daga cikin membobinta. Taron, wanda ya gudana a zauren taro na Gamji Gate da ke Kaduna, ya faro ne da gabatar da membobin dandalin, wadanda suka samu halartar taron, inda daga bisani, Shugaban Dandalin na Jihar Kaduna, Alhaji Yakubu Rigasa ya gabatar da jawabin maraba. A jawabinsa, mai gudanar da dandalin, wanda kuma shi ne ya kirkiro shi, Malam Shehu Mustafa Chaji, ya fadi cewa ya kirkiro dandalin ne a ranar 19 ga March na shekarar 2008, domin fadakarwa gami da wayar da kan al’umma game da al’amuran siyasa a kasar nan. Sauran wadanda suka gabatar da jawabi a wurin, sun hada da Shugaban Kwamitin Gudanarwa na dandalin, Alhaji Hashimu Ubale Yusuf da Malam Umaru Sa’idu Tudun Wada da kuma Malam Yakubu Jos. Dukkansu dai sun nuna bukatar samun canji a zamantakewar al’ummar Najeriya, inda za a rika gudanar da al’amuran mulki da zamantakewa cikin dacewa, mutunta juna, da niyyar kawo ci gaba a Najeriya. Wadanda aka karrama a wurin taron sun hada da Alhaji Umaru Dembo, da John danfulani da Hajiya Binta Zakari da kuma Hajiya A’isha Zakari. Da yake nuna bukatarsa ta daukar dawainiyar taron dandalin na badi a Sakkwato, dan jarida mai zaman kansa, Alhaji Yusuf Abubakar Dingyadi, ya tabbatar wa membobin dandalin cewa, za su ga abin mamaki a taron na Sakkwato, inda ya sha alwashin halartar gwamnoni biyu a taron. Haka kuma ya jaddada cewa membobin dandalin na Jihar Sakkwato, za su yi wa mahalarta taron gagarumar tarba, tare da zagayawa da su wuraren tarihi a Jihar Sakkwato, domin buda ido. An dai tashi taron lafiya. http://www.aminiya.com/kano/AMINIYA/051110%20Aminiya/page%2027.pdf

No comments:

Post a Comment