Sunday, 10 October 2010

Shugaba Jonathan : Kyan Alkawari .......

Da Shugaba Goodluck Ebele Jonathan ya zabi yabi shawarwarin da mafi yawan yan Nijeriya suka bashi na kin shiga zaben shekara ta 2011 a matsayin dan takara da kasar bata shiga halin rudani da tsaka mai wuya da ta sami kanta a ciki a yanzu ba. Tun kafin ma ya fito karara ya nuna aniyarsa ta tsayawa takara kawunan yan kasa ya rabu tsakanin yan – arewaci da yan kudanci.

A shekarar 1999 da sojoji zasu mika ragamar mulki ga yan siyasa bisa tsarin mulkin farin hula yan siyasa a lokacin suka amince su baiwa yan kudancin Nijeriya dama su fidda shugaban kasa daga sashin su saboda su huce kan matsalar da tsohon Shugaban Kasa Janar Ibrahim Babangida ya jefa kasar kan rushe zaben 12 ga watan June na 1993 inda ake kyautata zaton Marigayi Cif M.K.O Abiola ne ya lashe zaben. A zaben na 1999 Cif Olusegun Obasanjo na jam’iyyar PDP da Cif Olu Falae na APP/AD kadai suka tsaya takaran neman shugabancin kasa. Daga baya bayanai sun fito kan yadda jam’iyyar PDP ta tsara karba karba tsakanin kudanci da arewacin Nijeriya. Jam’iyyar ta shirya jarjejeniya a ind sashin kudu zasu yi shekaru takwas sannan arewacin kasa suma su dana har na tsawon shekaru takwas.

Bayan rasuwar tsohon Shugaban Kasa marigayi Umaru Musa Yar’adua, aka rantsar da Mataimakin sa Dakta Goodluck Jonatan a matsayin Shugaban Kasa. Sabanin tunanin mafi yawan yan Najeriya inda suka zaci Jonathan zai maida hankali gun cika alkawarukkan da gwamnatin su ta dauka kamar kudurori bakwai da samar da wutar lantarki da sa ido bisa ahuwan da aka yiwa tsagerun Neja Delta da sauran su. Sai kawai suka wayi gari Shugaba Jonathan yasa kafa take yarjejeniyar dake tsakanin kudu da arewa a jam’iyyar sa ta PDP . Ya fito karara ya nuna cewa kundin tsarin mulkin Nijeriya ya bashi damar tsayawa takara. Duk da masu kira a gare shi kar ya tsaya takara sun fito sunyi nuni da cewa a gaban sa aka tsara yarjejeniyar a likacin yana Mataimakin Gwamnan Jihar Bayelsa.

In zamu koma baya a shekarar 1976 da aka kashe marigayi Janar Murtala Mohammed inda Janar Olusegun Obasanjo ya gaje shi duk da cewa tsarin mulkin kasa ta bashi dama na iya kwabe kakin sa ya shiga takara baiyi haka ba saboda mutumtaka . Haka ma a shekarar 1999 da Janar Abdulsalam Abubakar zai mika mulki ga farin hula shima bai nuna zalama da karanta ya fake da zancen tsarin mulkin kasa ta bashi dama ya tsaya takara ba. Shi yasa masu nazari kan siyasar Najeriya ke ganin cewa shima Shugaba Jonathan duk da dokar kasa ta bashi damar tsayawa takara amma tunda akwai yarjejeniya shima ya kamata ya hakura da takara ya maida hankali wajen gudanar da ingantattcen zabe.

Wasu yan Najeriya na ganin baima kamata Shugaba Jonathan ya nemi takara ba tunda su a ganin su babu wasu ayyuka na cigaba da inganta rayuwar talaka da za’a ce kai tsaye talakawa sun amfana dashi ba .Suna kawo tabarbarewan tsaro da karuwan cin hanci da rashawa da almubazaranci da dukiyar kasa da rashin hanyoyi masu kyau dake sanadiyar rasa rayuka da rashin ingantattacen asibitoci da magunguna da makarantu da sauran su. Koda yake magoya bayan Jonathan na ganin cewa in aka bashi lokaci ya kafa tsare-tsaren da nan gaba in yan Nijeriya suka bashi dama zasu darge musamman kan ayyukan cigaban kasa.

Yan Arewacin Najeriya na korafin cewa Shugaba Jonathan na dakile ayyukan da zasu kai yankin su ga cigaba kamar yin kafar angulu ga yashe kogin kwara da dakatar da aiki jirjin kasa da cire yan yakin daga muhimman mukamai yana maye su da wasu daga yankin da ya fito ko zuwa wani bangaren. Sannan uwa uba rawar da suke zargin sa da takawa wajen kare kungiyar MEND da ta dauki alhakin kai tagwayen hare hare a birnin Abujaduk da sun fito sunyi ikirarin haka. Sannan tsohon madugun kungiyar MEND a hirar da tashar talabijin ta aljazira tayi dashi yace wani na hannun daman Shugaba Jonathan ya nemi yayi wa kuniyar MEND bayanin cewa suce babu hannun su a harin sannan yace wasu yan Arewa ne ke bayan harin.A takaice wasu yan Arewa na gain mulkin Shugaba Jonathan yafi karkata ga dadadawa wani bangare na kasar sannan bai dauki dukkan al’ummar Nijeriya a matsayin jama’ar sa ba.

Lokaci har yanzu bai kurewa Shugaba Jonathan ba na ko ya girmama yarjejeniyar da jam’iyyar sa ta PDP ta gindaya ba na mulki ya koma Arewa a zaben 2011 ta tsayar da dan takara daga Arewa. Najeriya kasa ce mai tarin kabilu da addinai da ra’ayoyi mabanbanta saboda haka tsarin karba karba tsari ne dake taimakawa wajen dunkulewan kasar mu a matsayin al’umma daya. In kuma har ya dage sai ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar PDP to sai ayyukan sa a fannin cigaban kasa su fidda shi in jama’a na bukatar ya cigaba da mulki ko a’a.

Amma wasu yan Nijeriya na ganin abinda yafi dacewa shine Shugaba Jonathan ya hakura da takara zuwa nan gaba domin ya sami damar gudanar da zaben da mafi yawan yan Nijeriya zasu amince dashi . Koba komai dattijantaka da mutumtaka na cika ne in babba ya kasance mai cika alkawari. Yan jam’iyyar sa ta PDP nada dama ko su amince masa ya tsaya takara ko kuma su nemi ya girmama tsarin karba karba da suke kanta tun shekarar 1999.

Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com

No comments:

Post a Comment