Monday 17 December 2007

LABARIN ZOMO DA MANGWARO

Wata rana ne Zomo na tsalle-tsallen sa yana tunanin zuci,daya karaso karkashin wata bishiyar Mangoro yana daga kansa sama sai ya hango wani Mangoro jajawur, ga girma kuma gashi ya nuna sosai.Ganin haka ya fara tunanin yaya zai yi ya sami Mangwaron dan shi ba zai iya hawa bishiyar ba. Yana tunanin yanda zai yi sai ga Kurciya ta sauka a kan bishiyar Mangwaron.Tana hango Zomo tayi masa sallama "barka dai "shima Zomo ya maida gaisuwar "kaima barka dai" Sannan ya kara da cewa "taimaka mani Kurciya ki tsinkar mani wancan Mangoron".

Kurciya a take ta tashi ta kusanci Mangwaron dan ta tsinka .Domin yawun ta ya tsinke da ganin mangoron kuma tayi tunanin ta cinye shi ita kadai. Amma da ta tsinki Mangoron sai ta kasa rikewa da bakin ta ,sakamakon haka sai Mangoron ya fado kasa.

Zomo na ganin haka cikin murna yac wa Kurciya"nagode" ya sun kuya ya dauki Mangwaro sai ya gan Mangwaron nata gungurawa daga gare shi , kai kamar Mangoron ne da kan sa ke gungurawa.Mamaki ya kama Zomo yana cewa" anya Mangoro da kansa zai yi ta gungurawa haka! Yana dubawa da kyau sai ya lura da cewa Mangoron ya fado ne a bayan Bushiya ya kuma makale a jikin kayoyin dake jikin ta. Shi yasa in ta motsa sai Mangoron ma ya motsa. Bushiya na ganin mangwaro a bayan sa ,ya yanke shawarar cewa Mangoron nasa ne kuma gashi da son Mangwaro. A take sai ya yanke shawarar ya arcen da Mangoron. Zomo na ganin haka ya kwada masa kira yana "tsaya! tsaya! dawo! Ina zaka da Mangoro na? Bushiya na jin haka sai ya samu waje ya tsaya, yace ma Zomo "Mangoron nan a baya na ya fado saboda haka Mangwaron nan nawa ne" . Kurciya na kallon su sai tace "kai, ku daina gardama a zancen gaskiya Mangoro dai nawa ne dan ni na tsinko shi daga kan bishiya". Haka dai suka rinka gardama da rants-rantse kan cewa ko wannen su na da'awar cewa Mangoro nasa ne.

Suna cikin wannan yamutsin sai ga Kare yazo wuce wa .Sai ya tsaya yana kallon hayaniya da tada jijiyoyin wuya da suke yi. Sai yace masu"wai kan me kuke wannan daga murya? Sai duk suka taho wajen sa , sai dayan su ya kada baki yace"Kare ka kasance mai hikima da kwarewa sakamakon zaman ka da mutane, saboda haka muna son kayi mana shari'a bisa adalci kan wanda yafi cancanta ya tafi da wannan Mangoro". Sai ko wannen su ya bashi labarin dalilin sa na cewa Mangoro nasa ne. Kare yayi tunani ,sai ya tambaya "wa ya fara ganin Mangoron ? Sai Zomo ya kada baki yace "ni ne! ni ne ! Sai kare ya sake tambaya "wa ya tsinko Mangoro? Sai Kurciya tayi tsalle ta ce "ni ce! ni ce na tsinko! Sai kare ya sake tambaya " wa ya dauki Mangoro bayan an tsinko? Sai Bushiya ya ce "ni ne! ni ne domin a baya na ya fado! Sai Kare ya yanke masu hukunci kan cewa "matsalar da kuke fuskanta shine ko wannan ku nada iko akan Mangoro, amma Mangoro guda daya ne , saboda haka na yanke hukuncin cewa za'a raba maku Mangoro ku daidai gida uku".

Mamaki da murna ya kama dabbobin gaba daya kan hukuncin da Kare ya yanke masu. A take Bushiya ya dauko Mangoro daga bayan sa ,ya raba gida hudu. Ya fara mika wa Zomo "ga rabon ka saboda fara ganin Mangoro". Sai ya mika wa kurciya yana cewa "ga naki rabon dan tsinko mangoron da kika yi". Sai ya baiwa kansa wani bangaren yace "saboda ya fado a baya na". Sannan ya baiwa Kare wani bangaren yace "ga naka " Kare yayi mamakin gaske cike da farin ciki sai ya ce "me yasa nima kuka bani wani bangaren a matsayin rabo na?" Sai Bushiya ya ce "saboda ka bamu shawaran da muka ji dadi ". Ta wannan hanyar dukkan su suka sami rabon shan Mangoro mai dadi cikin jin dadi da annashuwa.

Darasin da wannan labarin ke koyar wa ita ce raba dai dai aiki ne mai kyau domin yana kawo farin ciki da warware matsaloli da dama.

Haza wassalam

Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com

No comments:

Post a Comment