Sunday, 30 December 2007

Benazir Bhutto: Mace Mai Kamar Maza !

Ranar 27 ga watan Disambar 2007 zai kasance bakar rana a tarihin kasar Pakistan da gun masu gwagwarmayar kafuwa da dorewar tsarin dimokaradiya a duniya,saboda kisan gillar da akayi wa Malama Benazir Bhutto , tsohuwar Firaministan kasar Pakistan kuma mace ta farko data fara rike babban mukamin siyasa a kasar Musulmi a wannan zamanin.

An haife ta ranar 21 ga watan Yuni na shekarar 1953 a birnin Karachi na kasar Pakistan. Ta kuma yi karatu a manyan jami'oi wato Havard a Amurka da Oxford a Birtaniya.Mahaifinta Marigayi Zulfikar Ali ya gamu da ajalin sa ta hanyar rataya a hannun sojoji masu mulkin kasar a lokacin karkashin jagorancin Janar Zia Ul Haqq. Itama bata tsira ba daga mulkin danniya na sojojin kasar inda aka kama ta tare da tsare ta na tsawon shekaru kafin a sake ta, ta kuma bar kasar a shekarar 1984. A shekarar 1986 ta sake komawa Pakistan inda ta sami gagarumin tarba daga jama'ar kasar. Ta tsaya takara a karkashin jam'iyyar Pakistan People's Party(PPP) inda ta sami nasara ta kuma kasance Firaminista tana da shekaru talatin da biyar a duniya.

A lokacin mulkin ta, ta samar da wutar lantarki a kauyukan kasar da kuma gina makarantu a ko'ina cikin kasar.Manyan manufofin gwamnatin ta sune kokarin kawo karshen yunwa da samar da gidaje masu saukin kudi ga iyalai da gina asibitoci da lamurran da suka shafi kula da lafiya a birane da kauyukan kasar. Tayi matukar kokari wajen ganin cewa kasar ta , ta sami cigaban zamani kamar sauran kasashen yankin.

Zargin cin hanci da sama da fadi da dukiyar al'umma yasa shugaban kasa na lokacin Shugaba Leghari ya rushe gwamnatin ta, aka kuma damke mijin ta aka daure shi, ganin yanda abubuwa suka kasance , sai ta sake barin Pakistan ,inda ta shafe kusan shekaru goma ita da ya'yanta suna gudun hijiran sa kai a birnin Landan. Kuma duk da cewa bata kasar amma bata yi kasa a gwiwa ba wajen ganin cewa an dawo da mulkin dimokaradiya a kasar Pakistan ba.

Duk da barazanar da take fuskanta daga masu adawa da ita, ta koma kasar Pakistan a watan Octoban da ta gabata, ta kuma tsira daga harin kunan bakin waken da aka kai mata wanda yayi sanadiyar rasuwar mutane fiye da dari .Amma harin da aka sake kai mata a garin Rawalpindi yayi sanadiyar mutuwar ta da wasu mutum ashirin.

Shaka babu rasuwar Benazir Bhutto zai samar da babban gibi a siyasar Pakistan , musamman zaben da ake shirin gabatarwa ranar 8 ga watan Janairu . Jam'iyyar ta na PPP nada farin jini da tasiri da karfin gaske a kasar wanda saboda hakkar ta da tasirin da zata iya yi nema Janar Pervez Musharraf yayi wa tsohon firaminista Nawaz Sharif afuwa shima ya dawo kasar domin rage karfin Benazir Bhutto da yarjejeniyar da ta kulla da Janar Musharraf ya rushe na tayi masa firaminista.

Kasar Pakistan ta sake samun kanta a tsaka mai wuya sakamakon kisan Benazir Bhutto . Shi kansa Musharraf yana cikin halin bayan sa Kura gaban sa Zaki saboda magoya bayan Benazir Bhutto na ganin cewa ya kasa bata cikakken tsaro duk da barazanar da take fuskan ta daga masu adawa da ita. Ta bangaren gwamnati sun daura zargin kisan nata akan kungiyoyin al-Kaida da Taliban.Wata kungiyar masu tsattsauran ra'ayin addini sun nisan ta kan su daga daukar alhakin kisan nata. Ta bangaren magoya bayan Benazir Bhutto sun nuna shakkun su kan cewa jagoran sojin sa kai Baitullah Mehsud nada hannu a kisan nata duk da ikirarin da yayi na cewa zasu tura dan kunan bakin wake ya tarbe ta duk lokacin data dawo Pakistan.

Malama Benazir Bhutto ta shafe kusan shekaru shida na rayuwar ta a tsare a gidan kurkuku ko a hannun jami'an tsaro.Yan'uwan ta biyu wato Murtaza da Shahnawaz suma a baya kashe su aka yi. A shekarar 1977 lokacin da aka tsare mahaifin ta bayan juyin mulkin da Janar Zia ya jagoran ta , ya tuhume shi da laifin kisan kai, inda bayan shekaru biyu aka rataye shi. An daure Benazir Bhutto kafin a kashe mahaifin ta, inda ekaru biyar a gidan kurkuku, kuma yanda ta fada a wani yanayi mai wahalar gaske.

Ta zama Firaministan kasar Pakistan a shekarun 1988 zuwa 1990 da 1993 zuwa 1996. Tay matukar kokarin ta wajen ganin cewa an yafe wa juna abubuwan da suka faru a shekarun baya a kasar da kokarin ganin cewqa an rage banbancin da ake nunawa tsakanin maza da mata.

Kafin dawowar ta Pakistan ,wasu yan kasar na zargin ta da ganawa da sojoji masu mulkin kasar , inda sukayi tataunawar sirri domin a bata damar taka wata rawa ta musamman a siyasar kasar.Wannan yasa wasu yan kasar na zargin ta da cin amanar tsarin bunkasar dimokaradiya a asar.Inda wasu kuma na ganin cewa tattaunawar nada amfanu ga kafuwar dimokaradiya a kasar. Su kuma kasashen Yamma na ganin cewa goyon baya da karbuwa da take dashi a kasar ,tunda ta kasan ce tanada sassaucin ra'ayi na iya baiwa Janar Musharraf halarci a da'awar sa na "yaki da ta'addanci".

A jawaban ta marigayiya Benazir Bhutto bata boye fahimtar ta kan masu tsattsauran ra'ayin addinin Musulunci ba, kan yanda suke gudanar da al'amurran su a kasar, inda tayi alkawarin in aka zabe ta zata samo hanyar da yafi dacewa wajen magan ce matsalar tsattsauran ra'ayin addini sabanin yanda Janar Musharraf ke tinkaran lamarin.Ta kuma yi alkawarin cewa zata cika alkawarorin da Musharraf ya kasa cikawa kan batun makarantun madarasah inda zata aiwatar da sauye-sauyean makarantun, zata kuma baiwa hukumar IAEA damar ganawa da Abdulkadir Khan kan fasahar nukiliyar Pakistan.

Mutuwar Benazir Bhutto yasa ta cimma manufofinta da ta kasa cimma lokacin da take raye.Yanda ta gamu da ajalinta ya sanya duk an mance da kurakuran da ake ganin ta tafka lokacin data jagoranci kasar a baya. A ko'ina cikin duniya an kadu da mutuwar ta inda shugabanin kasashen duniya sukayi jawaban kwarai a kanta.Kuma ga dukan alamu mutuwar nata zai bude sabon babi a gwagwarmayar kafuwar dimokaradiya a kasar Pakistan da makomar Janar Musharraf da kuma yadda kasar zata tinkari matsalar masu tsattsauran ra'ayin addini. Kasar Pakisatan na dab da fadawa cikin mumunan yanayin siyasa koma yakin basasa sakamakon kashe Benazir Bhutto. Matsalar da kasar ta sami kanta ya zarce matsalar cikin gida ko yanki. Pakistan kasa ce da masu tsananin kishin addinin Musulunci keda tasiri a siyasan ce, kuma kasar nada fasahar makamin nukiliya wanda wadannan dalilai biyu barazana ce ga kasar Amerika da Turai.

Tarihi zai ruwaito Benazir Bhutto a matsayin wata mace data tsaya kai da fata kan akidu da manufofin da tayi imani dasu ba tare da jin tsoro ba, tasa kasar ta agaba duk da barazanar da take fuskanta har ta bar duniya tana kan gwagwarmayar inganta rayuwar al'umman kasar ta.

Haza Wassalam,

Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com

Monday, 17 December 2007

LABARIN ZOMO DA MANGWARO

Wata rana ne Zomo na tsalle-tsallen sa yana tunanin zuci,daya karaso karkashin wata bishiyar Mangoro yana daga kansa sama sai ya hango wani Mangoro jajawur, ga girma kuma gashi ya nuna sosai.Ganin haka ya fara tunanin yaya zai yi ya sami Mangwaron dan shi ba zai iya hawa bishiyar ba. Yana tunanin yanda zai yi sai ga Kurciya ta sauka a kan bishiyar Mangwaron.Tana hango Zomo tayi masa sallama "barka dai "shima Zomo ya maida gaisuwar "kaima barka dai" Sannan ya kara da cewa "taimaka mani Kurciya ki tsinkar mani wancan Mangoron".

Kurciya a take ta tashi ta kusanci Mangwaron dan ta tsinka .Domin yawun ta ya tsinke da ganin mangoron kuma tayi tunanin ta cinye shi ita kadai. Amma da ta tsinki Mangoron sai ta kasa rikewa da bakin ta ,sakamakon haka sai Mangoron ya fado kasa.

Zomo na ganin haka cikin murna yac wa Kurciya"nagode" ya sun kuya ya dauki Mangwaro sai ya gan Mangwaron nata gungurawa daga gare shi , kai kamar Mangoron ne da kan sa ke gungurawa.Mamaki ya kama Zomo yana cewa" anya Mangoro da kansa zai yi ta gungurawa haka! Yana dubawa da kyau sai ya lura da cewa Mangoron ya fado ne a bayan Bushiya ya kuma makale a jikin kayoyin dake jikin ta. Shi yasa in ta motsa sai Mangoron ma ya motsa. Bushiya na ganin mangwaro a bayan sa ,ya yanke shawarar cewa Mangoron nasa ne kuma gashi da son Mangwaro. A take sai ya yanke shawarar ya arcen da Mangoron. Zomo na ganin haka ya kwada masa kira yana "tsaya! tsaya! dawo! Ina zaka da Mangoro na? Bushiya na jin haka sai ya samu waje ya tsaya, yace ma Zomo "Mangoron nan a baya na ya fado saboda haka Mangwaron nan nawa ne" . Kurciya na kallon su sai tace "kai, ku daina gardama a zancen gaskiya Mangoro dai nawa ne dan ni na tsinko shi daga kan bishiya". Haka dai suka rinka gardama da rants-rantse kan cewa ko wannen su na da'awar cewa Mangoro nasa ne.

Suna cikin wannan yamutsin sai ga Kare yazo wuce wa .Sai ya tsaya yana kallon hayaniya da tada jijiyoyin wuya da suke yi. Sai yace masu"wai kan me kuke wannan daga murya? Sai duk suka taho wajen sa , sai dayan su ya kada baki yace"Kare ka kasance mai hikima da kwarewa sakamakon zaman ka da mutane, saboda haka muna son kayi mana shari'a bisa adalci kan wanda yafi cancanta ya tafi da wannan Mangoro". Sai ko wannen su ya bashi labarin dalilin sa na cewa Mangoro nasa ne. Kare yayi tunani ,sai ya tambaya "wa ya fara ganin Mangoron ? Sai Zomo ya kada baki yace "ni ne! ni ne ! Sai kare ya sake tambaya "wa ya tsinko Mangoro? Sai Kurciya tayi tsalle ta ce "ni ce! ni ce na tsinko! Sai kare ya sake tambaya " wa ya dauki Mangoro bayan an tsinko? Sai Bushiya ya ce "ni ne! ni ne domin a baya na ya fado! Sai Kare ya yanke masu hukunci kan cewa "matsalar da kuke fuskanta shine ko wannan ku nada iko akan Mangoro, amma Mangoro guda daya ne , saboda haka na yanke hukuncin cewa za'a raba maku Mangoro ku daidai gida uku".

Mamaki da murna ya kama dabbobin gaba daya kan hukuncin da Kare ya yanke masu. A take Bushiya ya dauko Mangoro daga bayan sa ,ya raba gida hudu. Ya fara mika wa Zomo "ga rabon ka saboda fara ganin Mangoro". Sai ya mika wa kurciya yana cewa "ga naki rabon dan tsinko mangoron da kika yi". Sai ya baiwa kansa wani bangaren yace "saboda ya fado a baya na". Sannan ya baiwa Kare wani bangaren yace "ga naka " Kare yayi mamakin gaske cike da farin ciki sai ya ce "me yasa nima kuka bani wani bangaren a matsayin rabo na?" Sai Bushiya ya ce "saboda ka bamu shawaran da muka ji dadi ". Ta wannan hanyar dukkan su suka sami rabon shan Mangoro mai dadi cikin jin dadi da annashuwa.

Darasin da wannan labarin ke koyar wa ita ce raba dai dai aiki ne mai kyau domin yana kawo farin ciki da warware matsaloli da dama.

Haza wassalam

Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com