Tun ranar da aka rantsar da Alhaji Umaru Musa Yar’adua a matsayin Shugaban Kasa ya amince da cewa an sami kurakurai a zaben daya kaishi kan kujerar shugaban kasa.Ya kuma nuna sha’awar hada kai da yan’adawa domin ciyar da kasa gaba. Da wannan tayin yan’adawa ke ta kaiwa da komowa kan amincewa ko a’a da gayyatar da Shugaba Yar’adua yayi masu har dai suka amince suka karbi goron gayyata.
Wannan tayin da alamun zai kawo rarrabuwan kai tsakanin yan ‘adawa saboda har an sami sabanin ra’ayuka tsakanin yan’takarar shugaban kasa a jam’iyyun adawa manya wato jam’iyyun ANPP da AC. Jam’iyyar ANPP ce ta fara amsar goron gayyatar, yayin da dan takarar ta na shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari yaki amincewa saboda a cewar sa suna gaban kotu kan rashin amincewar su da sakamakon zaben .Ta bangaren jam’iyyar AC sun bayyana sharadan da in aka amince dasu to zasu amsa goron gayyata ,inda daga bisani da dan takarar ta na shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya dawo gida Nijeriya daga neman magani a kasashen waje ya bayyana matsayin sa na cewa ba zasu amshi ko shiga gwamnatin Yar’adua ba saboda suna gaban kotu.
Da alamun shugaba Yar’adua yayi babban nasara wajen dakushe kaifin yan’adawa saboda an sami banbancin matsaya tsakanin manyan jam’iyyun adawa da yan takarar shugaban kasa a jam’iyyun su .Jam’iyyun na ganin cewa tunda shugaba Yar’adua ya name su kan warware matsalolin da suke addaban Nijeriya to ya zama wajibi su zauna su tattauna domin samin mafita.Su kuma yan’ takarar shugaban kasa a jam’iyyun na ganin cewa tunda suna gaban manta sabo kan ki da amincewar da zaben gaba daya to babu dalilin da zai sa su zauna teburi guda da Yar’adua a matsayin Shugaban Kasa sai in har kotu ta zartar da hukuncin ta.Wannan sabanin ra’ayin na Buhari da Atiku da jam’iyyun su na iya janyo dangantaka mai tsami ko raba gari gabaki daya a tsakanin su.
Shugaba Yar’adua na neman goyon bayan yan’adawa ne duk da yanda daga farko shugaban jam’iyyar sa ta PDP Sanata Ahmadu Ali ya bayyana cewa babu bukatar shigowa da yan’adawa cikin gwamnatin PDP.Amma ganin cewa Shugaba Yar’adua ya kafe kan tafiya tare da yan ‘adawa, jam’iyyar sa ta PDP ta mika wuya.Cikin bukatun abubuwan da yake so su tattauna da yan ‘adawa sun hada da samo hanyar bunkasar tattalin arzikin kasa da warware matsalar yankin Neja Dalta da batun tsaron kasa da sake fasalin kundin tsarin mulkin kasa da kuma kawo gyara a tsarin gudanar da zabe .An kuma ruwaito cewa zai basu kujerun ministoci da jakadu da mashawarta dau wasu mukaman.
An fara zaman farko tsakanin Shugaba Yar’adua da jam’iyyun adawa ranar 26 ga watan Mayu .Cif John Oyegun da Sanata Ahmed Sani Yarima da Sanata Umar Kumo ne suka jagoranci tawagar jam’iyyar ANPP yayin da Cif Audu Ogbeh da Dakta Abubakar Rimi da Alhaji Bashir Dalhatu suka jagoranci tawagar jam’iyyar AC zuwa wajen taron.Inda Mataimakin Shugaban Kasa Dakta Jonatan Goodluck ya shugabanci taron a madadin Shugaban Kasa.Ya kumata mika nasu bukatun ga yan’adawa ,suka kuma yan’adawa suka mika nasu bukatun ga gwamnatin Yar’adua.Inda daga bisani jam’iyyar ANPP ce ta fara amincewa da hada kai da gwamnatin Yar’adua,sai kuma jam’iyyar PPA ,amma jam’iyyar AC na ta kwamgaba gwambaya saboda wasu na so wasu kuma suna tare da ra’ayin Alhaji Atiku Abubakar.
Amma me yasa manyan jam’iyyun adawa suka mika wuya ta hanyar amsar gayyatar shiga gwamnatin hadin kai? Wasu masu fashin bakin siyasa na ganin cewa jam’iyyun na adawa na ganin haka shi yafi dacewa a gare su saboda da alamun cewa gwamnatin Yar’adua ta zauna da gidin ta saboda sunyi kira ga al’ummar kasa da su fito zanga-zangar kin amincewa da gwamnatin Yar’adua a ranar 1 ga watan Mayu amma talakawan kasa basu amsa kiran nasu ba.Sannan kasashen duniyar duk da kiran yan ‘adawa na su kaurace wa gwamnatin Yar’adua sunyi watsi da kiran sun rungumi gwamnatin Yar’adua harma da gayyatar sa taron manyan kasashen duniya na G-8.Haka kuma suma jam’iyyun ‘adawa a jihohin da suka kafa gwamnati jam’iyyar PDP a jihohin sun gurfanar dasu a kotu kan zargin tafka magudi suma inda yanda guguwar canji dake bugawa a bangaren shari’a na iya raba gwamnonin su da kujerun su.Wasu kuma yan’adawar ba zasu iya zama shekaru hudu ba suna adawa saboda sunfi ganewa a dama dasu.Sannan akwai wasu cikin yan adawar da zasu mika wuya ga gwamnatin Yar’adua saboda suma a manta da yanda suka gudanar da mulkin jihohin su.Shugabanin al’umma daga Arewa suma sun kasance cikin sahun gaba na a baiwa gwamnatin Yar’adua cikakken goyon baya.Kungiyar ACF da NU duk sun rungumi Shugaba Yar’adua ,shima Sarkin Musulmi Saad Abubakar ya jagoranci tawagar sarakuna domin yiwa Shugaba Yar’adua mubaya’a, kazalika manyan malaman addini na Musulmi da Kirista duk suna yiwa Shugaba Yar’adua mubaya’a da kungiyoyi daban daban na matasa da yan’kasuwa da sauran su sun je sunyi wa Shugaba Yar’adua mubaya’a .
Janar Muhammadu Buhari na fuskantar babbar kalubale a rayuwar sa ta siyasa saboda in ya nace kan cigaba da bin kadin shari’rar sa a kotu sabanin matsayin jam’iyyar sa ta ANPP to zai iya kaiwa jam’iyyar ta dauki mataki a kan sa. Abokanen adawar sa a jam’iyyar AC na iya komawa inda suka fito wato jam’iyyar PDP saboda jam’iyyar har ta kafa kwamitin da zai dawo da ya’yan ta da aka sami sabanin ra’ayi suka bar jam’iyyar da su dawo a cigaba da harkoki dasu a jam’iyyar PDP.In haka ya kasance to Janar Buhari Kadai za’a bari kan shari’a da gwamnatin Shugaba Yar’adua.Amma bayanan dake fitowa daga offishin kamfen din tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar na nuni da cewa zai bi kadin shari’ar da ya shigar gaban kotu.Kuma wasu na ganin cewa dawowar tsohon Shugaban Kasa Obasanjo cikin harkokin jam’iyyar PDP a matsayin shugaban kwamitin dattawa na iya zama dalili na duk wadanda suke da matsala da Obasanjo suki amincewa da batun sulhun dawowar su jam’iyyar.
Wasu jam’iyyun adawa karkashin lemar NUD su kuma sun tubure kan batun kafa gwamnatin wucin gadi,wato suna kan bakan su na cewa Shugaba Yar’adua yayi murabus ya mika mulki ga gwamnatin hadaka ta wucin gadi domin gudanar da sabon zabe.Amma da wuya su iya wani tasiri saboda manyan jam’iyyun adawa guda uku wato ANPP da Ac Da PPA sun nuna sha’awar su ga samar wa Nijeriya mafita sabanin bin hanyoyin da baza su cimma wata nasara ba a tunanin su.
Wasu yan ‘Nijeriya na ganin cewa akwai bukatar yiwa Shugaba Yar’adua uzuri domin ayyukan sa na nuni da cewa da gaske yake wajen samun bakin zaren matsalolin da suka hana Nijeriya cigaba .Suna kuma ganin cewa ya dauki matakan da suka fara nuna cewa shi ba dan amshin shatar tsohon shugaban kasa Obasanjo bane.Suna kawo misalai da yanda ya amshi bukatun kungiyar kwadago harma da daukan alkawarin cewa gwamnatin sa ba zata kara kudin man fetur ba har nan da watanni goma sha biyu da kuma sakin Alhaji Mujahid Asari Dokubo da soke kwangilolin da tsuhuwar gwamnati ta bayar da basu cikin kasafin kudin bana .Ga kuma kira da yake tayi na kowa da kowa yazo ya bada gudunmawarsa ga cigaban Nijeriya.
In da gaske ake kan batun cigaban dimokaradiyya a Nijeriya to babu bukatar jam’iyyun adawa su shiga gwamnatin hadin kan kasa saboda haka na nuni ga kasantuwar Nijeriya mai jam’iyya guda daya .Adawa a dimokaradiyya dole ne! Kuma wannan hadin kan kasa za’ayi yayin da jam’iyyar PDP na da kasa biyu bisa uku a majalisun tarrayya da na dattijai ga jihohi har guda ashirin da bakwai!! Sai dai in jam’iyyun adawa zasu ci amanar magoya bayan ta ne !!! Wadanda aka kashe,aka daure ,aka ci zarafin su ya zama a banza kenan.Kuma a gaskiya jam’iyyun zasu shiga halin da jam’iyyar AD ta sami kanta a yanzu.Dole a yabawa Janar Buhar da Alhaji Atiku Abukakar kan tsahin daka da suke nunawa na ganin cigaban dimokaradiya a Nijeriya ,kuma su sani cewa dukkan masu son cigaban tsarin dimokaradiya ta gaskiya na tare dasu.Su kuma tsaya kan matakin da suka dauka babu gudu babu ja da baya.
Talakawan Nijeriya na kallon yanda al’amurra ke gudana da kuma fatan cewa kowa zai girbi abinda ya shuka ,saboda yan’siyasa da yan’boko a kasar nan bukatun kan su ne a gaba.Sannan suna zuba ido su gan yanda zata kare a gaban shari’a tsakanin gwamnatin Yar’adua da yan takarar shugaban kasa wato Buhari da Atiku domin da alamun jam’iyyun su zasu janye jikin su daga cigaba da bin kadin magoya bayan su a gaban kotu.
Haza Wassalam
Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com
Thursday, 5 July 2007
Subscribe to:
Posts (Atom)