Thursday, 6 November 2025
Shugaba Tinubu mutum ne mai tausayi da Jin - Kai ga yan Najeriya
Shugaba Tinubu mutum ne mai tausayi da jin - kai ga yan Najeriya.
Daga Shehu Chaji.
Shugaba Bola Ahmad Tinubu, lokacin da aka zaɓe shi ya fuskanci ƙalubale saboda jarumtakar da ya nuna na cire tallafin man fetur, wanda wasu ƙanana ƙungiyoyi ke samun dubban biliyoyin naira, kuɗaɗen da za a iya amfani da su don bunƙasa tattalin arzikinmu da samar da ababen more rayuwa a ko’ina cikin ƙasa.
Wannan babban matakin yanzu yana haifar da sakamako mai kyau; tattalin arzikin Najeriya yana dawowa kamar yadda aka saba.
Jagorancin tausayi na Tinubu ya bayyana sosai a yadda ya gudanar da jana’izar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari. Bayan sanarwar rasuwar tsohon Shugaba Buhari, Shugaba Tinubu ya umarci Mataimakinsa Kashim Shettima da wasu ministoci su tafi London su kawo gawar.
Shugaba Tinubu ya tsaya tare da iyalan Marigayi Buhari a lokacinsu na wahala. Shi kansa ya tafi Daura ya jagoranci jana’izar. Wannan shi ne karo na farko a tarihin Najeriya da aka ba tsohon Shugaban kasa irin wannan girmamawa.
Lokacin da tsohon Shugaba Shehu Shagari ya rasu kuma Buhari ne yake mulki, gwamnati bata yi masa girmamawa kamar yadda Tinubu ya yi ba.
Mu ɗauka Buhari ne yake mulki yanzu Tinubu ne tsohon Shugaba, shin zai sami irin wannan girmamawa? Shugaba Tinubu ya nuna wa ‘yan Najeriya cewa shi shugaba ne na kowa da kowa.
Ya kamata ‘yan Najeriya su canza tunaninsu game da shugabanci. Su daina kallon shugabanni kawai daga yankin su, masu magana da harshen su ko su ne mabiya addinin su kawai ne za su iya bada shugabanci nagari.
Yayin da Shugaba Tinubu ke jagorantar ƙasa da tausayi, jinƙai, kirki da kulawa ta gaske ga rayuwar ‘yan Najeriya, ya kamata su sake tunani game da shugabanci. Su daina son kai na kabilanci, yankanci da addini, su kuma lura yadda gwamnatin Tinubu ke gina harsashin ƙasa mai ƙarfi da arziki.
Gina ƙasa yana bukatar sadaukarwa, sa’ar ‘yan Najeriya ba su yi asarar rayuka da yawa ba kamar abin da aka samu a China. Nairar mu ta daidaita kuma hauhawar farashin kaya kusan ya tsaya cik. Gwamnatocin Tinubu na biyan albashi a kan lokaci, sabanin wasu ƙasashe kamar Argentina da ba su iya biyan albashin ma’aikatansu.
Domin ƙarfafa ci gaban da aka samu da samun nasara wajen gina Najeriya mai arziki, ‘yan Najeriya su zabi Shugaba Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Su guji bari ‘yan siyasa waɗanda suka gaza samar da kyakkyawan shugabanci lokacin da suke mulki su yaudarar da su ta hanyar kabilanci, yankanci da addini.
Najeriya na bukatar Tinubu, wanda jagora ne mai jarumtaka da tausayi, ya jagorance su zuwa Najeriya mai girma kamar mafarkin su.
Amb. Shehu Mustapha Chaji.
Daga Kano.
Kanawa na Godiya Shugaba Tinubu
Kanawa na Godiya Shugaba Tinubu
Daga Shehu Mustapha Chaji.
Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya kasance Shugaba dake so da kaunar Al'ummar Jihar Kano. Wannan kaunar yayi ta nunawa a aikace tun rantsar dashi a shekarar 2023 ta hanyoyi da dama.
Yan kwanaki da rantsar da Gwamnatin Kwankwasiyya a Jihar Kano ta kaddamar da Rusau baji ba gani. Shugaba Tinubu ne yabi hanyoyin diplomasiyya ya kawo karshen mafi munin Rusau a tarihin Jihar Kano.
Bayan nada Tsohon Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje a matsayin Shugaban Jam'iyyar APC na Kasa, Kanawa da dama sun dace da nada su manyan mukaman Gwamnati, saboda yawan wadanda ya nada mukamai daga Jihar Kano sai an zauna an natsu kafin a kawo yawan wadanda suka dace da mukamai a Gwamnatin sa.
Ga Triliyoyin kudade da Gwamnatin Tinubu ke kashewa wajen samar da ayyukan cigaba a Jihar Kano.
Shugaba Tinubu ya dora daga inda Gwamnatin baya ta tsaya kan ayyukan Titin Kano zuwa Kaduna da layin dogo daga Kano zuwa Abuja. Ga kuma layin dogo daga Kano zuwa Maradi.
Akwai ayyukan da ya bayar na by pass da zai kewaye Birnin Kano. Ga titin Kano zuwa Hadejia.
Gwamnatin Shugaba Tinubu ta kuma ware biliyoyin naira dan fadada da gyaran Dam din Tiga da sabbin ayyukan da zasu inganta noman rani da zai samarwa dubban Al'umma ayyukan yi da samun kudin shiga.
Wadannan kadan ne daga ayyukan cigaban Kasa da Shugaba Tinubu keta kwararowa Jihar Kano.
Kamar yanda Engr. Rabiu Suleiman Bichi Shugaban Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama'are ya sha fada , Hukumar mai shelkwata a Kano an ware masu kudi kusan fiye da ninki biyu in aka kwatanta da ragowar Hukumomin raya Koguna dan kulawa da samar da issashen abinci da kulawa da dama damai da mugudanan Ruwa dan ciyar da yankin Arewa ko Kasa gabaki daya.
Ba'a zancen ta bangaren samar da manyan makarantu kamar a Kabo da Rano duk a Jihar Kano.
Kuma Jihar Kano ta zama shelkwatar Hukumar raya Arewa maso yamma da samar da gudanar da ayyukan cigaba a fannoni daban daban.
Sai kwasam Shugaba Tinubu ya ayyana Gwamnatin sa za ta kashe Naira Tiriliyan daya da rabi don gina layin dogo na zamani domin saukaka harkar sufuri a cikin birnin Kano.
Ayyuka raya kasa da damarmakin da Jihar Kano ke samu karkashin mulkin Shugaba Tinubu da yan Jam'iyyar APC a Jihar Kano zasuyi koyi dasu Engr. Rabiu Suleiman Bichi da Hon Musa Iliyasu Kwankwaso wajen kwakwazon moriyar da Kanawa ke samu karkashin mulkin Shugaba Tinubu da Kanawa da murya daya zasu cewa Shugaba Tinubu ya zarce domin tunda aka dawo mulkin dimokaradiyya daga shekarar 1999 basu taba cin moriyar dimokaradiyya kamar a wannan lokacin na Mulkin Tinubu ba.
Muna fatan Kanawa zasuyi fatali da farfagandar yan adawa na cewa a bar yankin Arewa wajen samar da ayyukan cigaban Kasa.
Koda yake saboda ayyukan cigaba da Shugaba Tinubu keyi da kuma yawan Kanawa dake rike da manyan mukamai yan adawa basu da wani tasiri a Jihar Kano.
Yanda Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Tsohon Shugaban Jam'iyyar APC na Kasa kuma Jagoran Jam'iyyar APC a Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje
ya kawowa Shugaba Tinubu mafi yawan kuri'u a Najeriya har yanzu dakarun sa na siyasa suna nan kuma sun kara yawa da karfi. A kwananan sun sake sake jaddada goyon bayan su ga Shugaba Tinubu.
Darakta Janar na kamfen din Tinubu/Shettima wato Engr. Rabiu Suleiman Bichi na nan da Sarkin Yakin Jam'iyyar APC da Shugaba Tinubu Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso na nan da Shugaban Jam'iyyar APC na Jihar Kano Prince Abdullahi Abbas na nan ga kuma jiga jigan yan Jam'iyyar APC a mataikai daban daban. In dai zancen kuri'u ake to Shugaba Tinubu ya kwantar da hankalin sa domin zai sami ninkin kuri'un daya samu a zaben shekarar 2023.
Kanawa na kara Godiya Shugaba Tinubu da fatan zai karo ayyukan cigaba masu yawa zuwa Jihar Kano.
Amb. Shehu Mustapha Chaji
Daga Kano.
Tinubu da Ayyukan Cigaban Kasa a Jihohin Arewa
Tinubu da ayyukan cigaban Kasa a jihohin Arewa.
Daga Shehu Mustapha Chaji
A yayin da muke tunkarar zaben shekarar 2027 wasu mutane musamman daga Jam'iyyun adawa suna ta yada farfagandar cewa a karkashin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ana cutar Arewa wajen samar da ayyukan cigaban Kasa.
In za'a dubi maganganun masu yada wannan farfagandar da ainihin abinda ke kasa to za'a fahimci cewa zarge zargen su basu da tushe bare makama. Duk mai bibiya zai fahimci cewa ayyukan cigaban Kasa da Tinubu keyi a Arewacin Najeriya sunfi na Kudu yawa.
Shugaba Tinubu yana kokarin kwatanta adalci na kokarin ganin cewa kowane yanki a Najeriya na amfana da ayyukan cigaban Kasa.
Yayin ziyarar da Maigirma Shugaban Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama'are Engr. Rabiu Suleiman Bichi ya kai jihohin Jigawa da Bauchi ya bayyana wasu daga cikin ayyukan cigaban Kasa da Shugaba Tinubu ya samar a jihohin Kano da Jigawa da Bauchi da suke karkashin Hukumar sa. Rabiu Suleiman Bichi yace an kwashe shekaru ashirin da shida ana wahalar samun ruwan sha a Dutse babban Birnin Jihar Jigawa amma zuwan Shugaba Tinubu ya ware biliyan 60 dan samar da ruwa a Dutse da kewaye. Yace tuni Tinubu ya bada naira biliyan 15 da aka fara da cigaban aikin. Yace (Bichi) karkashin Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama'are kawai Shugaba Tinubu ya sahale a kashe Biliyan 98 domin gyaran Dam din Tiga da Chalawa Gorge Dam da Kalala Dam da Kafin Zaki Dam da ayyukan noman rani na Kafin Ciri da gyara da kula da Hadejia Barrage da samar da sabbin Kadada dubu 6,500 dan inganta noman rani da wasu ayyukan duk a Jihohin Kano da Jigawa da Bauchi.
In jami'an Gwamnati zasuyi koyi da Engr. Rabiu Suleiman Bichi wajen bayyana ayyukan dake Hukumomin su da farfagandar yan adawa bai zaiyi wani tasiri ba.
Akwai ayyukan cigaban Kasa sabbi da wadannan aka cigaba da aikin su karkashin mulkin Shugaba Tinubu. Wadannan suna kadan daga cikin manyan ayyukan cigaban Kasa da akeyi a Arewacin Najeriya:
1. Baban titin Sokoto zuwa Badagry daya ratsa ta jihohin Sokoto da Kebbi da Neja da Kwara mai tsawon kilomita 1068 inda titin zai hade da jihohin dake Kudancin Najeriya.
2. Aikin dasa bututun gas daga Ajaokuta zuwa Abuja da Kaduna da Kano da akafi sani da AKK.
3. Aikin tagwayen hanyoyi mai nisan kilomita 375 da zai ratsa ta jihohin Sokoto da Zamfara da Katsina da Kaduna.
4. Cigaba da aikin titin Jirgin Kasa daga Kano zuwa Kaduna.
5. Cigaba da aikin titin bypass din Lafiya a Jihar Nasarawa.
6. Gina dubban gidaje a jihohin Sokoto da Kebbi da Neja da Kaduna da Binuwai da Zamfara da Kano.
7. Cigaba da aikin titin Abuja zuwa Kaduna da Kano.
8. Cigaba da aikin bypass a gabashin Kano.
9. Aikin titin Maiduguri zuwa Manguno.
10. Aikin titin Cham zuwa Numan (Gombe zuwa Yola).
11. Aikin titin Mil 9 zuwa Oturkpo da Makurdi.
12. Cigaba da aikin titin Abuja zuwa Lokoja.
13. Cigaba da aikin titin Akwanga zuwa Jos da Bauchi da Gombe mai tsawon kilomita 439.
14. Cigaba da aikin titin Kano zuwa Katsina.
15. Gina sabon titin jirgin kasa da zai rika zirga zirga a cikin Birnin Kano
16. Gina sabbin tashoshin mota na zamani a jihohin Kano da Gombe da Kogi.
17. Samar da Hukumomin raya yankin Arewa maso yamma da Arewa ta tsakiya.
18. Aikin tagwayen titi daga Bauchi zuwa Gombe.
19. Gyara da samar da sabbin tituna guda 135 a Abuja.
20. Samar da ruwa sha a Abuja.
21. Samar da ruwan sha a Garin Dutse Jihar Jigawa.
22. Cigaba da aikin titin daya ratsa ta Sahara mai tsawon kilomita 456.
23. Cigaba da aikin samar da tashar lantarki a Gwagalada da zai samar da megawatts 1350.
24. Cigaba da aikin titin Jirgin Kasa daga Kano zuwa Dutse da Maradi.
25. Ayyukan dakatar da zaizayan kasa a kananan Hukumomi 16 a Jihar Kano.
Abubuwan da muka lissafo a sama na daga cikin ayyukan cigaban Kasa da Shugaba Tinubu keyi kusan a koina a Arewacin Najeriya. Wadannan ayyukan cigaban Kasa zasu taimaka wajen bunkasar tattalin arzikin Arewa da Najeriya.
Shugaba Tinubu ya cancanci jinjina dan cigaba da ayyukan cigaban Kasa da ba'a Gwamnatin sa aka fara ba sabanin halayyen yan siyasa in suka karbi mulki na kin karasa ayyukan cigaban Kasa da basu suka kirkiro ba.
Akwai bukatar Gwamnatin Shugaba Tinubu tayi kokarin dakile farfagandar yan adawa ta hanyar jawo yan siyasa irin su Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso da Mai bawa Shugaba Tinubu shawara kan masarautu Malam Abbas Tijjani Hashim dan sanar da Al'umma ire iren ayyukan cigaban Kasa da Shugaba Tinubu keyi musamman a Arewacin Najeriya.
Arewacin Najeriya tabbas na cin moriyar ayyukan cigaban Kasa karkashin mulkin Shugaba Tinubu kuma babu abinda zasu saka masa fiye da sake zaben sa a shekarar 2027.
Amb. Shehu Mustapha Chaji
Tinubu da Ayyukan Cigaban Kasa a Jihar Kano
Tinubu da ayyukan cigaban Kasa a Jihar Kano
Daga Shehu Mustapha Chaji
Kasancewar Jihar Kano cibiyar Kasuwanci da dimokaradiyya a Arewacin Najeriya na daga cikin dalilan daya sa Shugaban Kasa Alhaji Bola Ahmed Tinubu ke cigaba da baiwa Jihar kulawa ta musamman. Cikin ayyukan cigaban Kasa da Shugaba Tinubu ya sahale ayiwa Jihar Kano a wannan makon sun hada da ware Naira Biliyan 12 dan samar da wutar solar a Asibitin Malam Aminu Kano da zai samar da megawatt bakwai da hakan zai sanya asibitin sauka daga layin lantarki ta kasa.
Ana kuma cigaba da aikin gina bene mai hawa biyar na sashin bayar da kulawar gaggawa (Emergency) a Asibitin. A wannan shekarar kawai Shugaba Tinubu ya sahale a kashe Naira Biliyan 26 a Asibitin Malam Aminu Kano domin maida Asibitin sahun manyan Asibitoci a Afrika.
Karin cibiyoyin da suka amfana da ayyukan cigaban Kasa a Jihar Kano a wannan makon suna hada da :
Jami'ar Bayero da za'a sanya wutar solar megawatt biyar zuwa shida.
Jami'ar Aliko Dangote dake Wudil da za'a sanya wutar solar megawatt hudu.
Asibitin Murtala da za'a sanya wutar solar megawatt uku
Asibitin Nasarawa da za'a sanya wutar solar megawatt uku.
Samar da wutar solar ga wadannan cibiyoyi zai rage musu yawan kudaden da suke kashewa kan lantarki da dizel da kula da Janeretoci da sauran su.
Wasu yan adawa a kullum suna kokarin yada farfagandar cewa babu abinda Shugaba Tinubu yayiwa Jihar Kano na cigaba. Zancen gaskiya akwai ayyukan cigaban Kasa da dama da aka fara ko aka cigaba da aikin su karkashin mulkin Shugaba Tinubu. Kadan daga cikin su sun hada da :
1). Cigaba da aikin gina layin dogo daga Kano zuwa Kaduna.
2). Cigaba da aikin gina dubban gidaje masu sauki a wasu kananan Hukumomin Jihar Kano.
3). Ayyukan gyara dan maida Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano kamar na Kasashen da suka cigaba a duniya.
4). Cigaba da aikin tagwayen titi daga Kano zuwa Kaduna zuwa Abuja.
5). Cigaba da aikin titin Bypass a gabashin Kano.
6). Cigaba da aikin tagwayen titi daga Kano zuwa Katsina.
7). Cigaba da aikin titin Kano zuwa Hadejia.
8). Cigaba da aikin bututun gas (AKK).
9). Aikin Jirgin Kasa na zamani da zai ratsa Birnin Kano.
10) Cigaba da aikin titin jirgin kasa daga Kano zuwa Dutse zuwa Maradi.
11). Kulawa ta musamman kan tsayar da zaizayan kasa a kananan Hukumomi 16 a Jihar Kano.
12). Aikin gina sabbin mugudanan Ruwa daga Dam din Tiga da Dam din Karaye da Dam din Kafin Chiri zuwa Kano ta Kudu dan bunkasa noman rani.
13). Cigaba da aikin tagwayen titi daga Kano zuwa Maiduguri.
14). Cigaba da aikin titin Bypass mai tsawon kilomita 38 a arewacin Kano.
15). Gyara da kara girman Dam din Tiga.
16). Daga matsayin makarantar gaba da sakandare dake Kabo zuwa Jami'ar kimiya da fasaha.
17). Sahalewa a gina Makarantar gaba da sakandare a Rano.
18). Gyara dama damai goma sha shida a Jihar Kano.
19). Aikin gina cibiyar taron kasa da kasa a Yar Gaya.
Saboda takaita bayanai kan ayyukan cigaban Kasa da Shugaba Tinubu keyi a Jihar Kano zamu tsaya a haka.
Kanawa suna ta godiya da jinjina ga Shugaba Tinubu kan yanda yake ta kwararo ayyukan cigaban Kasa a Jihar Kano. Tunda aka dawo mulkin dimokaradiyya a shekarar 1999 Jihar Kano a karon farko ta san ana mulkin dimokaradiyya.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kwantar da hankalin sa kan batun zaben shekarar 2027 domin zasu bashi kuri'u kusan miliyan biyu.
Amb. Shehu Mustapha Chaji
Nigeria, Tinubu and Compassionate Leadership
Nigeria, Tinubu and Compassionate leadership
By Shehu Chaji
President Bola Ahmad Tinubu thought when elected into office faced challenges due to his courageous decision to remove fuel subsidy that some few cartels are making hundreds of billions of naira, monies that can be used for growth of our economy and providing infrastructures all-over the country.
This bold decision is now yielding positive results Nigeria’s economy is returning to normal.
Tinubu’s compassionate leadership was fully exhibited on how he handled the burial of former President Muhammadu Buhari. After the announcement of the death of former President Buhari, President Tinubu directed his Vice President Kashim Shettima and some Ministers to head to London and bring back his corpse.
President Tinubu stood by the family of Late Buhari at their trying period. He personally traveled to Daura to led the funeral rites. This is the first time in Nigeria’s history that a former President was so honored.
When former President Shehu Shagari died and now late Buhari was in charge, his government didn’t honor him near what President Tinubu did.
Let’s assume that Buhari is in charge and Tinubu is the former President, will he receive such honor? President Tinubu proves to Nigerians he’s a leader for all Nigerians.
The Nigerian people should try to change their mindset about leadership. They should stop thinking of only the leaders they speak the same language, came from the same region, practice the same religion etc can provide purposeful leadership.
As President Tinubu is leading the country with compassion, empathy, kindness and a genuine concern for wellbeing of Nigerians, Nigerians should have a second thought on leadership. Let them drop sentiment of tribalism, regionalism, and religious sentiment and access how Tinubu administration is laying down the foundation of a great and prosperous Nigeria.
Nation building requires sacrifices and luckily for Nigerians it didn’t take long and no loss of millions of lives as the case of China. Our Naira is now stable and inflation almost stopped. Governments under Tinubu are paying salaries on due unlike countries that faced challenges similar to Nigeria like Argentina that can’t pay salaries to workers in the country.
To consolidate progress made so far and achieve success in building a prosperous Nigeria, Nigerians should vote for President Tinubu come 2027 Presidential election?
They should not allow politicians that failed to provide good governance when they are in charge deceive them with tribal, regional and religious sentiments.
Nigeria needs Tinubu who is courageous and compassionate leader to led them to the great Nigeria of their dreams.
Amb. Shehu Mustapha Chaji
writes from Kano.
Tinubu, Kano and Dividends of Democracy
Tinubu, Kano and Dividends of Democracy.
By Shehu Mustapha Chaji
Since the assumption of office the people of Kano state have continue to enjoy special care , regard and concern from President Bola Ahmad Tinubu.
Just few days after Kwankwasiyya led administration was sworn in to power in Kano state their first policy was massive demolitions that the state never witnessed in its history. As tension raised through using diplomatic means President Tinubu ended it and normalcy returned to the ancient city.
After former Governor Dr. Abdullahi Umar Ganduje assumed office as APC National Chairman many indigenes of Kano state were appointed into President Tinubu's government. Due to large numbers of those appointed from Kano state one cannot easily count their numbers.
Tinubu's administration have been spending Trillions of naira to build infrastructures across the state that will led to development and growth of the state.
President Tinubu administration also didn't abandon, cancel or stopped infrastructures works started by previous administrations as it's the tradition with many past governments. Tinubu's administration continues with those works which includes Kano to Kaduna Highway, Kano to Katsina road, Kano to Maiduguri road, Railway from Kano to Abuja and Railway from Kano to Maradi .
The Tinubu administration also ended the long standing dispute delaying the construction of 38 kilometer Kano Northern Bypass and works continues. Also the work from Kano to Hadejia in Jigawa state.
President Tinubu also awarded new contract for rehabilitation and expansion of Tiga Dam to boost Irrigation farming that will provide more jobs and increase income to people of Kano while at the same time providing food security.
These are mentioned some works on infrastructures going on in Kano state.
In areas of providing food security as Engr. Rabiu Suleiman Bichi MD Hadejia Jama'are River Basin Development Authority, Kano have been saying, the River Basin with its headquarter in Kano was allocated the highest amount to help it boost Irrigation farming, protecting of Dams, water channels and opening thousands of Hectres of lands for all season farming that will led to increase of food that can feed the country and even exported.
In area of education, new higher institutions were upgraded to University i.e Kabo and new to be build in Rano. Thousands of students also benefitted from NELFUND to help them study in ease.
Kano state also host the headquarter of North West Development Commission which will help to facilitate development in many areas.
And suddenly Tinubu administration awarded contract for light railway that will cost about 1.5 Trillion naira to turn Kano to world class city.
Kano state under Tinubu administration, the state enjoys building of infrastructures and people from the state appointed into many positions of power. If APC stewards are trumpeting dividends of democracy the state is enjoying like Engr. Rabiu Suleiman Bichi and Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso then by now President Tinubu should not even bother to come to Kano for his re election campaign.
Kano state presently enjoys dividends of democracy under Tinubu administration that the state never witnessed from 1999 after return of democracy.
The people of Kano are aware of propaganda by the opposition that the North is been short changed. But they know it's pure propaganda and that's the reason why the opposition is totally weak in the state. Many infrastructures works are on going and large numbers of those appointed from the state also help in crippling the opposition in Kano state.
Former Governor of Kano state and Chairman of APC Dr. Abdullahi Umar Ganduje got the highest votes in Nigeria to President Tinubu during the 2023 presidential election. His team is still intact and even received main leaders of the opposition NNPP Kwankwasiyya during 2023 election into APC. And just recently the Kano APC endorsed President Tinubu for second term due to great work to make Nigeria great again.
Kano APC is more stronger than APC of 2023 with Dr. Abdullahi Umar Ganduje the leader, the Director General Tinubu/Shettima Campaign Council is on ground, Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso feared by the opposition is on ground, the Kano APC Chairman Prince Abdullahi Abbas and many strong stalwarts of the party are all on ground. The votes President Tinubu will receive from Kano come 2027 will be more than double of votes he received during 2023 presidential election.
The great people of Kano appreciates President Tinubu and hope more infrastructures will be site in the state.
Amb. Shehu Mustapha Chaji
writes from Kano
Tinubu and Development of Northern Nigeria
Tinubu and Development of Northern Nigeria.
By Shehu Mustapha Chaji
As we approach 2027 election some people especially from the opposition are spreading a lot of propaganda that the administration of President Bola Ahmed Tinubu is sidelining the North in areas of infrastructure and development.
If one cross check and make own research it will reveal that the opposition are lying and surprisingly the North gets more infrastructures compared to the South!
President Tinubu's administration is distributing dividends of democracy to all parts of the country.
During the courtesy visit by Engr Rabiu Suleiman Bichi MD Hadejia Jama'are River Basin Development Authority, Kano to Governors of Bauchi and Jigawa states he enumerated projects approved by President Bola Ahmed Tinubu in those states under his agency. Bichi said, Dutse the capital of Jigawa state after suffering for 26 years lacking portable drinking water, President Tinubu voted N60 billion for Greater Dutse Water Supply Scheme and have so far released more than N15 billion for the on going work. And Just under Hadejia Jama'are River Basin Development Authority, Kano there are projects of about N98 billion for rehabilitation and repairs of Tiga Dam, Challawa Gorge Dam, Kalala Dam, Kafin Zaki Dam, Kafin Ciri Irrigation Project, repairs and maintenance of Hadejia Barrage, creation of 6,500 Hectres for irrigation and so many other projects in Kano, Jigawa and Bauchi States.
If many government officials will inform the public about President Tinubu's projects under their ministries/agencies etc the opposition cannot easily mislead the public.
There are many projects new and on going by President Tinubu's administration. Among this projects in Northern Nigeria are :
1. Sokoto - Badagry Highway that will link Northern and Southern regions from Sokoto, Kebbi, Niger , and Kwara states a 1068 kilometers project.
2. Sokoto - Zamfara - Katsina - Kaduna dual carriageway of 375 kilometers project.
3. On going Ajaokuta - Abuja - Kaduna - Kano (AKK) Gas pipeline.
4. On going Kano - Kaduna Rail line project.
5. On going construction of Lafia Bypass in Nasarawa state.
6. Construction of thousands of Houses in Sokoto, Kebbi , Katsina, Zamfara, Kaduna, Niger, Benue and Kano States.
7. On going construction of Abuja - Kaduna - Kano Expressway.
8. On going construction of Eastern Bypass in Kano state.
9. Maiduguri - Manguno Road.
10. Cham - Numan Road ( Gombe - Yola).
11. 9 Mile - Oturkpo - Makurdi road.
12. On going construction of Abuja - Lokoja Highway.
13. On going 439 kilometers Akwanga - Jos - Bauchi - Gombe Road .
14. On going Kano - Katsina road.
15. Light Railway Kano city.
16. Construction of Bus terminals in Kano, Lokoja and Gombe.
17. Establishment of Development Commissions for Northwest and North Central.
18. Dualization of Bauchi - Gombe Road.
19. About 135 roads constructed or re construction in FCT .
20. Greater Abuja Water Supply Project.
21. Greater Dutse Water Supply Scheme.
22. On going construction of 456 kilometers Trans - Sahara Road .
23. On going construction of Gwagalada Independent power plant that will generate 1350 megawatts.
24. On going construction of Kano - Dutse - Maradi Rail line project.
25. Ecological protection in 16 Local Government Areas of Kano state.
The above are just some of the on projects approved by President Tinubu's administration allover Northern Nigeria. And this projects will led to development of Northern Nigeria is all aspects.
And the North is lucky for having someone as President Tinubu as President of Nigeria! He continues projects not started or initiated by him unlike many of our politicians !
To tackle the opposition misleading the public the government should bring on board vocal politicians like Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso to enlighten the public. And the office of Malam Abbas Tijjani Hashim the President's Senior Special Assistant on Chieftaincy Matters should also be in contacts with our traditional rulers from bottom to top a create awareness ongoing works by President Bola Ahmed Tinubu allover the North.
As the North continues to benefits dividends of democracy under Tinubu's administration the North should reciprocate by massively voting him again come 2027 presidential election.
Amb. Shehu Mustapha Chaji
writes from Kano.
Subscribe to:
Comments (Atom)
