Thursday, 6 November 2025

Tinubu da Ayyukan Cigaban Kasa a Jihohin Arewa

Tinubu da ayyukan cigaban Kasa a jihohin Arewa. Daga Shehu Mustapha Chaji A yayin da muke tunkarar zaben shekarar 2027 wasu mutane musamman daga Jam'iyyun adawa suna ta yada farfagandar cewa a karkashin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ana cutar Arewa wajen samar da ayyukan cigaban Kasa. In za'a dubi maganganun masu yada wannan farfagandar da ainihin abinda ke kasa to za'a fahimci cewa zarge zargen su basu da tushe bare makama. Duk mai bibiya zai fahimci cewa ayyukan cigaban Kasa da Tinubu keyi a Arewacin Najeriya sunfi na Kudu yawa. Shugaba Tinubu yana kokarin kwatanta adalci na kokarin ganin cewa kowane yanki a Najeriya na amfana da ayyukan cigaban Kasa. Yayin ziyarar da Maigirma Shugaban Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama'are Engr. Rabiu Suleiman Bichi ya kai jihohin Jigawa da Bauchi ya bayyana wasu daga cikin ayyukan cigaban Kasa da Shugaba Tinubu ya samar a jihohin Kano da Jigawa da Bauchi da suke karkashin Hukumar sa. Rabiu Suleiman Bichi yace an kwashe shekaru ashirin da shida ana wahalar samun ruwan sha a Dutse babban Birnin Jihar Jigawa amma zuwan Shugaba Tinubu ya ware biliyan 60 dan samar da ruwa a Dutse da kewaye. Yace tuni Tinubu ya bada naira biliyan 15 da aka fara da cigaban aikin. Yace (Bichi) karkashin Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama'are kawai Shugaba Tinubu ya sahale a kashe Biliyan 98 domin gyaran Dam din Tiga da Chalawa Gorge Dam da Kalala Dam da Kafin Zaki Dam da ayyukan noman rani na Kafin Ciri da gyara da kula da Hadejia Barrage da samar da sabbin Kadada dubu 6,500 dan inganta noman rani da wasu ayyukan duk a Jihohin Kano da Jigawa da Bauchi. In jami'an Gwamnati zasuyi koyi da Engr. Rabiu Suleiman Bichi wajen bayyana ayyukan dake Hukumomin su da farfagandar yan adawa bai zaiyi wani tasiri ba. Akwai ayyukan cigaban Kasa sabbi da wadannan aka cigaba da aikin su karkashin mulkin Shugaba Tinubu. Wadannan suna kadan daga cikin manyan ayyukan cigaban Kasa da akeyi a Arewacin Najeriya: 1. Baban titin Sokoto zuwa Badagry daya ratsa ta jihohin Sokoto da Kebbi da Neja da Kwara mai tsawon kilomita 1068 inda titin zai hade da jihohin dake Kudancin Najeriya. 2. Aikin dasa bututun gas daga Ajaokuta zuwa Abuja da Kaduna da Kano da akafi sani da AKK. 3. Aikin tagwayen hanyoyi mai nisan kilomita 375 da zai ratsa ta jihohin Sokoto da Zamfara da Katsina da Kaduna. 4. Cigaba da aikin titin Jirgin Kasa daga Kano zuwa Kaduna. 5. Cigaba da aikin titin bypass din Lafiya a Jihar Nasarawa. 6. Gina dubban gidaje a jihohin Sokoto da Kebbi da Neja da Kaduna da Binuwai da Zamfara da Kano. 7. Cigaba da aikin titin Abuja zuwa Kaduna da Kano. 8. Cigaba da aikin bypass a gabashin Kano. 9. Aikin titin Maiduguri zuwa Manguno. 10. Aikin titin Cham zuwa Numan (Gombe zuwa Yola). 11. Aikin titin Mil 9 zuwa Oturkpo da Makurdi. 12. Cigaba da aikin titin Abuja zuwa Lokoja. 13. Cigaba da aikin titin Akwanga zuwa Jos da Bauchi da Gombe mai tsawon kilomita 439. 14. Cigaba da aikin titin Kano zuwa Katsina. 15. Gina sabon titin jirgin kasa da zai rika zirga zirga a cikin Birnin Kano 16. Gina sabbin tashoshin mota na zamani a jihohin Kano da Gombe da Kogi. 17. Samar da Hukumomin raya yankin Arewa maso yamma da Arewa ta tsakiya. 18. Aikin tagwayen titi daga Bauchi zuwa Gombe. 19. Gyara da samar da sabbin tituna guda 135 a Abuja. 20. Samar da ruwa sha a Abuja. 21. Samar da ruwan sha a Garin Dutse Jihar Jigawa. 22. Cigaba da aikin titin daya ratsa ta Sahara mai tsawon kilomita 456. 23. Cigaba da aikin samar da tashar lantarki a Gwagalada da zai samar da megawatts 1350. 24. Cigaba da aikin titin Jirgin Kasa daga Kano zuwa Dutse da Maradi. 25. Ayyukan dakatar da zaizayan kasa a kananan Hukumomi 16 a Jihar Kano. Abubuwan da muka lissafo a sama na daga cikin ayyukan cigaban Kasa da Shugaba Tinubu keyi kusan a koina a Arewacin Najeriya. Wadannan ayyukan cigaban Kasa zasu taimaka wajen bunkasar tattalin arzikin Arewa da Najeriya. Shugaba Tinubu ya cancanci jinjina dan cigaba da ayyukan cigaban Kasa da ba'a Gwamnatin sa aka fara ba sabanin halayyen yan siyasa in suka karbi mulki na kin karasa ayyukan cigaban Kasa da basu suka kirkiro ba. Akwai bukatar Gwamnatin Shugaba Tinubu tayi kokarin dakile farfagandar yan adawa ta hanyar jawo yan siyasa irin su Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso da Mai bawa Shugaba Tinubu shawara kan masarautu Malam Abbas Tijjani Hashim dan sanar da Al'umma ire iren ayyukan cigaban Kasa da Shugaba Tinubu keyi musamman a Arewacin Najeriya. Arewacin Najeriya tabbas na cin moriyar ayyukan cigaban Kasa karkashin mulkin Shugaba Tinubu kuma babu abinda zasu saka masa fiye da sake zaben sa a shekarar 2027. Amb. Shehu Mustapha Chaji

No comments:

Post a Comment