Thursday, 6 November 2025
Bichi HJRBDA da kudirin Tinubu na samar da abinci
Bichi, HJRBDA da kudirin Tinubu na samar da abinci.
Daga Shehu Mustapha Chaji
Yau kusan watanni bakwai da Engr. Rabiu Suleiman Bichi ya kama aiki a matsayin Shugaban Hukumar Kogunan Hadejia da Jama'are. Sun kama aiki tare da Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso a matsayin Daraktan Kudi sai Alhaji Tijjani Isa a matsayin Daraktan tsare tsare sai Engr. Baffa Datti Abdulkadir a matsayin Daraktan Injiya sai Hajiya Zainab Gamawa a matsayin Daraktan harkokin noma. Ana rantsar dasu suka kama aiki a take dan aiwatar da kudirorin Hukumar daya hada da kula da albarkatun ruwa dake doran kasa dana karkashin kasa a jihohin Kano da Jigawa da Bauchi.
Babban nasarar da suka fara samu shine na yin abinda ya dace dan dakile hambaliyar ruwa dake janyo asarar rayuka da albarkatun gona da dukiyoyi na miliyoyin naira kusan kowane shekara.
Bisa jagorancin Engr Rabiu Suleiman Bichi gwarzon da baya gajiya da aiki ko dare ko rana. Ko a kwananan Gwamna Bala Muhammad na Jihar Bauchi yace " munyi aiki tare da Rabiu lokacin da nake Ministan Abuja kuma yana cikin gwarazan Daraktoci a Hukumar FCDA a lokacin". Duk yayin da aka zo wa Bichi da rahoton akwai matsala a magudanan ruwa ko Kogunan dake karkashin Hukumar Hadejia Jama'are a take yake bada umarnin aje a gyara. Ana kuma fara gyaran zaije wajen duk da irin yanayin wahalar zuwa ire iren wadannan wuraren musamman da damina. Engr Rabiu Suleiman Bichi da kansa ya kan hau babur ko kwale kwale da shiga chabi da tabo dan ya tabbatar anyi aikin. Wannan sadaukarwan ne dalilin dakile hambaliyar ruwa a jihohin Kano da Jigawa da Bauchi a wannan shekarar. Kuma kasancewar kofar sa kullum a bude yasa ma'aikatar Hukumar duk yayin da suka hango matsala zasu kira shi kai tsaye dan sanar dashi. Shi kuma a take ya umarci injiniyoyi suka garzaya wajen dan gyara.
Kudirorin Shugaba Tinubu na samar da abinci yayiwa Engr Bichi tasiri sosai. Hakan yasa yana cikin aiki ba dare ba rana domin wannan kudiri na Shugaba Tinubu ya zama ya tabbata domin ragargazan yunwa da samar da dubbin arziki.
Shugaba Tinubu ya bada umarnin gyara da kara girman Dama Damai har Sha shida a Jihar Kano ciki har da Dam din Tiga da Dam din Challawa Gorge da Dam din Kafin Chiri. Gyaran wadannan Dama Damai zai taimakawa Manoma fiye da dubu talatin su da iyalan su. Sannan za'a sami sabbin karin heka dubu hamsin dan noman rani. Manoma kuma zasu rinka noma sau uku a shekara. Kuma wannan gyaran da kara girman Dama Damai zai samar da sabbin ayyukan yi har dubu dari uku.
Bichi da tawagar sa a kullum suna aiki tukuru tsakanin jihohin Kano da Jigawa da Bauchi domin tabbatar da Manoma suna samun isashen ruwa dan bunkasa noman damina dana rani. Kuma sun kaddamar da yaki kan Ciyawar Kachala dake taimakawa wajen jawo ambaliya da hana Manoma samun isashen ruwa dan kulawa da shukokin su.
Wasu daga cikin ayyukan cigaba da Hukumar Hadejia Jama'are ta samu karkashin jagorancin Engr Rabiu Suleiman:
1) Bunkasa noman zamani da jawo Al'umma musamman Matasa su shiga harkan noma dan tabbatar da nasarar Shugaba Tinubu na samar da abinci.
2) Tsari da shirin baiwa Matasa dubu biyar horo a fannonin noman zamani musamman a fannin noman rani da kiwon zuma da noman a dakunan zamani. Burin Engr. Bichi ana samar da matasa da zasu zama hamshakan attajirai dubu biyar a jihohin Kano da Jigawa da Bauchi kusan kowane shekara.
3). Bunkasa noman rani ta hanyar kara heka da ake noma a yanzu daga heka dubu hamsin da hudu zuwa heka dubu dari biyu da arbain. Hakan zai kara bunkasa noman shinkafa daga tan dubu dari biyu da sha shida zuwa tan miliyan daya.
4). Samar da hanyoyin da za'a sami karin ruwa da kashi ashirin dan bunkasa noman rani.
5) Engr Rabiu Suleiman Bichi ya kasance ya aminta da da'awar Matar Shugaban Kasa Sanata Oluremi Tinubu na noma a kowane gida. Wannan kudirin nata zai taimaka wajen samar da abinci.
6) Manoma su rika noma har sau uku ko fiye a shekara a jihohin Kano da Jigawa da Bauchi.
7) Yanke Ciyawar Kachala ko wane lokaci a shekara da saka masana su kirkiro hanyar da za'a rika amfani da Ciyawar a matsayin makamashi a gidaje.
8) Kulawa da gyaran mugudanan Ruwa.
9) Daukan mataikai dan dakile hambaliyar ruwa da zaizayan kasa.
Hukumar Hadejia Jama'are karkashin jagorancin Engr Rabiu Suleiman Bichi sun dau alwashin gyara wuraren na musamman da aka tanade su dan tara ruwa domin noman rani. Wasu wuraren tara ruwa sunyi shekaru masu yawa a lalace ko ba'a amfani dasu. Ma'aikatar Hukumar Hadejia Jama'are suma suna cikin annashuwa domin sun sami Shugaba da zai farfado da inda suka kwashe shekaru suna aiki .
Muna amfani da wannan damar dan kira ga Engr. Rabiu Suleiman Bichi ya nemi mika rokon Kanawa ga Shugaba Tinubu ya sahale a samarwa Kano gidan ruwa na zamani kamar wanda akeyi a yanzu a Dutsen Jihar Jigawa da Abuja dan kawo karshen matsalar rashin ruwan amfanin yau da kullum a gidaje.
Saboda amincewa da girma da kima da Al'umma ke gani na Engr. Rabiu Suleiman Bichi mutane da dama sun zama Manoma a jihohin Kano da Jigawa da Bauchi wanda hakan zai bunkasa harkan noma.
Kudirin Shugaba Tinubu na samar da abinci zai zama gaske bisa jagorancin Engr Rabiu Suleiman Bichi a jihohin Kano da Jigawa da Bauchi.
Amb. Shehu Mustapha Chaji
Subscribe to:
Post Comments (Atom)

No comments:
Post a Comment