Thursday, 6 November 2025

Kanawa na Godiya Shugaba Tinubu

Kanawa na Godiya Shugaba Tinubu Daga Shehu Mustapha Chaji. Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya kasance Shugaba dake so da kaunar Al'ummar Jihar Kano. Wannan kaunar yayi ta nunawa a aikace tun rantsar dashi a shekarar 2023 ta hanyoyi da dama. Yan kwanaki da rantsar da Gwamnatin Kwankwasiyya a Jihar Kano ta kaddamar da Rusau baji ba gani. Shugaba Tinubu ne yabi hanyoyin diplomasiyya ya kawo karshen mafi munin Rusau a tarihin Jihar Kano. Bayan nada Tsohon Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje a matsayin Shugaban Jam'iyyar APC na Kasa, Kanawa da dama sun dace da nada su manyan mukaman Gwamnati, saboda yawan wadanda ya nada mukamai daga Jihar Kano sai an zauna an natsu kafin a kawo yawan wadanda suka dace da mukamai a Gwamnatin sa. Ga Triliyoyin kudade da Gwamnatin Tinubu ke kashewa wajen samar da ayyukan cigaba a Jihar Kano. Shugaba Tinubu ya dora daga inda Gwamnatin baya ta tsaya kan ayyukan Titin Kano zuwa Kaduna da layin dogo daga Kano zuwa Abuja. Ga kuma layin dogo daga Kano zuwa Maradi. Akwai ayyukan da ya bayar na by pass da zai kewaye Birnin Kano. Ga titin Kano zuwa Hadejia. Gwamnatin Shugaba Tinubu ta kuma ware biliyoyin naira dan fadada da gyaran Dam din Tiga da sabbin ayyukan da zasu inganta noman rani da zai samarwa dubban Al'umma ayyukan yi da samun kudin shiga. Wadannan kadan ne daga ayyukan cigaban Kasa da Shugaba Tinubu keta kwararowa Jihar Kano. Kamar yanda Engr. Rabiu Suleiman Bichi Shugaban Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama'are ya sha fada , Hukumar mai shelkwata a Kano an ware masu kudi kusan fiye da ninki biyu in aka kwatanta da ragowar Hukumomin raya Koguna dan kulawa da samar da issashen abinci da kulawa da dama damai da mugudanan Ruwa dan ciyar da yankin Arewa ko Kasa gabaki daya. Ba'a zancen ta bangaren samar da manyan makarantu kamar a Kabo da Rano duk a Jihar Kano. Kuma Jihar Kano ta zama shelkwatar Hukumar raya Arewa maso yamma da samar da gudanar da ayyukan cigaba a fannoni daban daban. Sai kwasam Shugaba Tinubu ya ayyana Gwamnatin sa za ta kashe Naira Tiriliyan daya da rabi don gina layin dogo na zamani domin saukaka harkar sufuri a cikin birnin Kano. Ayyuka raya kasa da damarmakin da Jihar Kano ke samu karkashin mulkin Shugaba Tinubu da yan Jam'iyyar APC a Jihar Kano zasuyi koyi dasu Engr. Rabiu Suleiman Bichi da Hon Musa Iliyasu Kwankwaso wajen kwakwazon moriyar da Kanawa ke samu karkashin mulkin Shugaba Tinubu da Kanawa da murya daya zasu cewa Shugaba Tinubu ya zarce domin tunda aka dawo mulkin dimokaradiyya daga shekarar 1999 basu taba cin moriyar dimokaradiyya kamar a wannan lokacin na Mulkin Tinubu ba. Muna fatan Kanawa zasuyi fatali da farfagandar yan adawa na cewa a bar yankin Arewa wajen samar da ayyukan cigaban Kasa. Koda yake saboda ayyukan cigaba da Shugaba Tinubu keyi da kuma yawan Kanawa dake rike da manyan mukamai yan adawa basu da wani tasiri a Jihar Kano. Yanda Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Tsohon Shugaban Jam'iyyar APC na Kasa kuma Jagoran Jam'iyyar APC a Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kawowa Shugaba Tinubu mafi yawan kuri'u a Najeriya har yanzu dakarun sa na siyasa suna nan kuma sun kara yawa da karfi. A kwananan sun sake sake jaddada goyon bayan su ga Shugaba Tinubu. Darakta Janar na kamfen din Tinubu/Shettima wato Engr. Rabiu Suleiman Bichi na nan da Sarkin Yakin Jam'iyyar APC da Shugaba Tinubu Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso na nan da Shugaban Jam'iyyar APC na Jihar Kano Prince Abdullahi Abbas na nan ga kuma jiga jigan yan Jam'iyyar APC a mataikai daban daban. In dai zancen kuri'u ake to Shugaba Tinubu ya kwantar da hankalin sa domin zai sami ninkin kuri'un daya samu a zaben shekarar 2023. Kanawa na kara Godiya Shugaba Tinubu da fatan zai karo ayyukan cigaba masu yawa zuwa Jihar Kano. Amb. Shehu Mustapha Chaji Daga Kano.

No comments:

Post a Comment