Thursday, 6 November 2025

Shugaba Tinubu mutum ne mai tausayi da Jin - Kai ga yan Najeriya

Shugaba Tinubu mutum ne mai tausayi da jin - kai ga yan Najeriya. Daga Shehu Chaji. Shugaba Bola Ahmad Tinubu, lokacin da aka zaɓe shi ya fuskanci ƙalubale saboda jarumtakar da ya nuna na cire tallafin man fetur, wanda wasu ƙanana ƙungiyoyi ke samun dubban biliyoyin naira, kuɗaɗen da za a iya amfani da su don bunƙasa tattalin arzikinmu da samar da ababen more rayuwa a ko’ina cikin ƙasa. Wannan babban matakin yanzu yana haifar da sakamako mai kyau; tattalin arzikin Najeriya yana dawowa kamar yadda aka saba. Jagorancin tausayi na Tinubu ya bayyana sosai a yadda ya gudanar da jana’izar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari. Bayan sanarwar rasuwar tsohon Shugaba Buhari, Shugaba Tinubu ya umarci Mataimakinsa Kashim Shettima da wasu ministoci su tafi London su kawo gawar. Shugaba Tinubu ya tsaya tare da iyalan Marigayi Buhari a lokacinsu na wahala. Shi kansa ya tafi Daura ya jagoranci jana’izar. Wannan shi ne karo na farko a tarihin Najeriya da aka ba tsohon Shugaban kasa irin wannan girmamawa. Lokacin da tsohon Shugaba Shehu Shagari ya rasu kuma Buhari ne yake mulki, gwamnati bata yi masa girmamawa kamar yadda Tinubu ya yi ba. Mu ɗauka Buhari ne yake mulki yanzu Tinubu ne tsohon Shugaba, shin zai sami irin wannan girmamawa? Shugaba Tinubu ya nuna wa ‘yan Najeriya cewa shi shugaba ne na kowa da kowa. Ya kamata ‘yan Najeriya su canza tunaninsu game da shugabanci. Su daina kallon shugabanni kawai daga yankin su, masu magana da harshen su ko su ne mabiya addinin su kawai ne za su iya bada shugabanci nagari. Yayin da Shugaba Tinubu ke jagorantar ƙasa da tausayi, jinƙai, kirki da kulawa ta gaske ga rayuwar ‘yan Najeriya, ya kamata su sake tunani game da shugabanci. Su daina son kai na kabilanci, yankanci da addini, su kuma lura yadda gwamnatin Tinubu ke gina harsashin ƙasa mai ƙarfi da arziki. Gina ƙasa yana bukatar sadaukarwa, sa’ar ‘yan Najeriya ba su yi asarar rayuka da yawa ba kamar abin da aka samu a China. Nairar mu ta daidaita kuma hauhawar farashin kaya kusan ya tsaya cik. Gwamnatocin Tinubu na biyan albashi a kan lokaci, sabanin wasu ƙasashe kamar Argentina da ba su iya biyan albashin ma’aikatansu. Domin ƙarfafa ci gaban da aka samu da samun nasara wajen gina Najeriya mai arziki, ‘yan Najeriya su zabi Shugaba Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027. Su guji bari ‘yan siyasa waɗanda suka gaza samar da kyakkyawan shugabanci lokacin da suke mulki su yaudarar da su ta hanyar kabilanci, yankanci da addini. Najeriya na bukatar Tinubu, wanda jagora ne mai jarumtaka da tausayi, ya jagorance su zuwa Najeriya mai girma kamar mafarkin su. Amb. Shehu Mustapha Chaji. Daga Kano.

No comments:

Post a Comment