Thursday, 6 November 2025

Tinubu da Ayyukan Cigaban Kasa a Jihar Kano

Tinubu da ayyukan cigaban Kasa a Jihar Kano Daga Shehu Mustapha Chaji Kasancewar Jihar Kano cibiyar Kasuwanci da dimokaradiyya a Arewacin Najeriya na daga cikin dalilan daya sa Shugaban Kasa Alhaji Bola Ahmed Tinubu ke cigaba da baiwa Jihar kulawa ta musamman. Cikin ayyukan cigaban Kasa da Shugaba Tinubu ya sahale ayiwa Jihar Kano a wannan makon sun hada da ware Naira Biliyan 12 dan samar da wutar solar a Asibitin Malam Aminu Kano da zai samar da megawatt bakwai da hakan zai sanya asibitin sauka daga layin lantarki ta kasa. Ana kuma cigaba da aikin gina bene mai hawa biyar na sashin bayar da kulawar gaggawa (Emergency) a Asibitin. A wannan shekarar kawai Shugaba Tinubu ya sahale a kashe Naira Biliyan 26 a Asibitin Malam Aminu Kano domin maida Asibitin sahun manyan Asibitoci a Afrika. Karin cibiyoyin da suka amfana da ayyukan cigaban Kasa a Jihar Kano a wannan makon suna hada da : Jami'ar Bayero da za'a sanya wutar solar megawatt biyar zuwa shida. Jami'ar Aliko Dangote dake Wudil da za'a sanya wutar solar megawatt hudu. Asibitin Murtala da za'a sanya wutar solar megawatt uku Asibitin Nasarawa da za'a sanya wutar solar megawatt uku. Samar da wutar solar ga wadannan cibiyoyi zai rage musu yawan kudaden da suke kashewa kan lantarki da dizel da kula da Janeretoci da sauran su. Wasu yan adawa a kullum suna kokarin yada farfagandar cewa babu abinda Shugaba Tinubu yayiwa Jihar Kano na cigaba. Zancen gaskiya akwai ayyukan cigaban Kasa da dama da aka fara ko aka cigaba da aikin su karkashin mulkin Shugaba Tinubu. Kadan daga cikin su sun hada da : 1). Cigaba da aikin gina layin dogo daga Kano zuwa Kaduna. 2). Cigaba da aikin gina dubban gidaje masu sauki a wasu kananan Hukumomin Jihar Kano. 3). Ayyukan gyara dan maida Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano kamar na Kasashen da suka cigaba a duniya. 4). Cigaba da aikin tagwayen titi daga Kano zuwa Kaduna zuwa Abuja. 5). Cigaba da aikin titin Bypass a gabashin Kano. 6). Cigaba da aikin tagwayen titi daga Kano zuwa Katsina. 7). Cigaba da aikin titin Kano zuwa Hadejia. 8). Cigaba da aikin bututun gas (AKK). 9). Aikin Jirgin Kasa na zamani da zai ratsa Birnin Kano. 10) Cigaba da aikin titin jirgin kasa daga Kano zuwa Dutse zuwa Maradi. 11). Kulawa ta musamman kan tsayar da zaizayan kasa a kananan Hukumomi 16 a Jihar Kano. 12). Aikin gina sabbin mugudanan Ruwa daga Dam din Tiga da Dam din Karaye da Dam din Kafin Chiri zuwa Kano ta Kudu dan bunkasa noman rani. 13). Cigaba da aikin tagwayen titi daga Kano zuwa Maiduguri. 14). Cigaba da aikin titin Bypass mai tsawon kilomita 38 a arewacin Kano. 15). Gyara da kara girman Dam din Tiga. 16). Daga matsayin makarantar gaba da sakandare dake Kabo zuwa Jami'ar kimiya da fasaha. 17). Sahalewa a gina Makarantar gaba da sakandare a Rano. 18). Gyara dama damai goma sha shida a Jihar Kano. 19). Aikin gina cibiyar taron kasa da kasa a Yar Gaya. Saboda takaita bayanai kan ayyukan cigaban Kasa da Shugaba Tinubu keyi a Jihar Kano zamu tsaya a haka. Kanawa suna ta godiya da jinjina ga Shugaba Tinubu kan yanda yake ta kwararo ayyukan cigaban Kasa a Jihar Kano. Tunda aka dawo mulkin dimokaradiyya a shekarar 1999 Jihar Kano a karon farko ta san ana mulkin dimokaradiyya. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kwantar da hankalin sa kan batun zaben shekarar 2027 domin zasu bashi kuri'u kusan miliyan biyu. Amb. Shehu Mustapha Chaji

No comments:

Post a Comment