Thursday, 20 March 2014
Majalisar Siyasa ta intanet ta karrama ’ya’yanta
Bashir Yahuza Malumfashi,
a Kaduna
A ranar Asabar ta makon jiya ce majalisar nan da ake kira da suna Dandalin Siyasa, wacce ke tattauna al’amuran siyasa a intanet ta gudanar da taronta na shekara-shekara, inda ta karrama hudu daga cikin membobinta.
Taron, wanda ya gudana a zauren taro na Gamji Gate da ke Kaduna, ya faro ne da gabatar da membobin dandalin, wadanda suka samu halartar taron, inda daga bisani, Shugaban Dandalin na Jihar Kaduna, Alhaji Yakubu Rigasa ya gabatar da jawabin maraba.
A jawabinsa, mai gudanar da dandalin, wanda kuma shi ne ya kirkiro shi, Malam Shehu Mustafa Chaji, ya fadi cewa ya kirkiro dandalin ne a ranar 19 ga March na shekarar 2008, domin fadakarwa gami da wayar da kan al’umma game da al’amuran siyasa a kasar nan.
Sauran wadanda suka gabatar da jawabi a wurin, sun hada da Shugaban Kwamitin Gudanarwa na dandalin, Alhaji Hashimu Ubale Yusuf da Malam Umaru Sa’idu Tudun Wada da kuma Malam Yakubu Jos. Dukkansu dai sun nuna bukatar samun canji a zamantakewar al’ummar Najeriya, inda za a rika gudanar da al’amuran mulki da zamantakewa cikin dacewa, mutunta juna, da niyyar kawo ci gaba a Najeriya.
Wadanda aka karrama a wurin taron sun hada da Alhaji Umaru Dembo, da John danfulani da Hajiya Binta Zakari da kuma Hajiya A’isha Zakari.
Da yake nuna bukatarsa ta daukar dawainiyar taron dandalin na badi a Sakkwato, dan jarida mai zaman kansa, Alhaji Yusuf Abubakar Dingyadi, ya tabbatar wa membobin dandalin cewa, za su ga abin mamaki a taron na Sakkwato, inda ya sha alwashin halartar gwamnoni biyu a taron. Haka kuma ya jaddada cewa membobin dandalin na Jihar Sakkwato, za su yi wa mahalarta taron gagarumar tarba, tare da zagayawa da su wuraren tarihi a Jihar Sakkwato, domin buda ido. An dai tashi taron lafiya.
http://www.aminiya.com/kano/AMINIYA/051110%20Aminiya/page%2027.pdf
Wednesday, 12 February 2014
Dandalin Siyasa : UPDATE
Its been long that the Management Committee of dandalinsiyasa@yahoogroups.com has its meeting due to political activities of 2011 elections in the country. All the same, on behalf of the Management I wish to congratulate our members that in one way or the other participated in the 2011 elections either as observers or in the wining or loosing side as they all contributed their quota to the growth of democratic governance in our country.
I will also use this opportunity to welcome new members on board , and I believe many have enjoyed their stay which is manifested by rate of participation of members in discussions , and the zeal many have showed in advising ways to make dandalin siyasa more greater to make positive contributions to development of our country.
Dandalin Siyasa forum is open to all Nigerians in respective of political , social, economic and religious affiliations of members, we are all partners in the business of strengthening our democratic norms and providing suggestions for our country’s development in all aspects.
The forum started as initiative of a single individual which is the first of its kind in Northern part of Nigeria and has today been able to provide us with a platform of a unique innovation in discussion forums in Nigeria. We have been able to achieve a lot in the last three years of Dandalin Siyasa existence. The forum had it first year anniversary in Kano (2009), Second anniversary in Kaduna (2010) and hopefully its third year anniversary to hold in Sokoto later in the year.
It has become a norm that during every anniversary event , some of our members are honoured with awards for their outstanding performance in the forum , so far six of our members received the awards in the past two years.
We are also able to register an NGO (DANDALI FOUNDATION) with CAC to enable us perform our functions in the larger society according to the laws of the land. Plans are in top gear to launch DANDALI FOUNDATION as soon as possible.
I will suggest to the house (forum) on the need for us to have an extra –ordinary meeting or get-together so that old and new members can come together face to face to strengthen friendship and exchange ideas as we do daily in the forum.
Once again , we welcome all new members to our great forum and hope they will contribute positively in whatever way for the growth of dandalin-siyasa@yahoogroups.com and Dandali Foundation.
Thank you all.
Pharm Hashim Ubale Yusufu,
Chairman, Management Committee,
Dandalin Siyasa Social Get Together
Dandalin Siyasa Online Discussion Forum held a Social Get Together at Tiga Dam on 25th June 2011. According to Chairman of the forum Pharm Hashim Ubale Yusufu, the get together is for new and old members of the forum to socialize, interract and to falicitate with members that are are appointed into political offices and those that won elections. Among prominent members that the forum rejoice with are Alhaji Ibrahim Wakkala elected as Deputy Governor of Zamfara state and Alhaji Umar Said Tudun Wada appointed as Director of Press to Kano State Governor.
Dandalin Siyasa Online forum was founded by Shehu Mustapha Chaji on March 19, 2009. The forum held it first ever anniversary in Kano and the second annioversary in Kaduna State. Hopefully before the end of the year the third anniversary event will take place in Sokoto state.
Members of the forum allover the country and abroad attended the event.
THE RISE OF DANDALIN SIYASA ONLINE FORUM (1)
Dandalin siyasa is an online discussion forum that was established and moderated by my close friend, Mustapha Shehu Chaji. Chaji was our former secretary general of Bayero University Kano, Students union government to match theory with practical as he read Bsc in political science. Chaji is a committed writer, activist and young revolutionaries. Dandalin siyasa is a forum for gavel-to-gavel discussions on political developments in Nigeria, Africa’s largest democracy.
Recently some of the active members of the dandali were opportune to accomplish success in their areas, hence the need to write and congratulate them and to graciously give kudos to the dandali and its members. The corner stone of our online forum is the mutual respect for people’s views, though freedom of expression is inherent in our dandali, views and opposition views expressed in the forum are the rights of individual contributors. The active members of dandali are to many to mention, but a few, like my humble self, then the moderator or simply ‘madugun dandali’’, shehu chaji, who got a job recently after he completed his masters degree program in Developmental studies at his Alma Mata. Congratulations to the General John Danfulani, for successfully becoming a Phd holder. Danfulani was the former president students union, A.B.U. Zaria, a prolific scholar and analyst. Ghali Rogo is another active member worthy of mention. He would be going to England to pursue a course on security detectives’ equipment course at Stafford University London.
The newly elected governor of Kano state, Rabi’u Kwankwaso made some appointments recently. Luckily for our dandali, about three of our active members were among. Dr. Inusa Dangwani is one of us, and he was the new chief of staff to Kano government house. Then the director press in person of Mallam Umar Said Tudunwada, popularly known as UST. He was the former General Manager Freedom radio Kano and deputy director press to Kwankwaso’s first tenure. Therefore his appointment did not come to many of us as a surprise; his track record is exceptional and highly impressive. I am wishing them a very meritorious tenure of service to their beloved state. I am very proud of dandalin siyasa online forum, and that is why I don’t mind if my views were not published in our dailies in as much as it was posted in dandali. Aliyu Tilde, Admiral Tsakuwa, Rigasa, Alhazai, Muazu Magaji, ……your views are respected by all and sundry. Long live Dandali and its members.
Ahmed Rasheed Makarfi.
Published in Muryar Talaka on 12/11/2011
Origin Of Dandalin Siyasa Online Forum
Dandalin Siyasa was created on March 19, 2008 by Shehu Mustapha Chaji, with the aim of providing a forum that mostly Nigerians from Northern part of the country can discuss and debate on issues relating to politics. And to also provide them with a forum that they can express their views and opiniions in matters relating to promotion of democracy in Nigeria, Africa and the world over. Dandalin Siyasa online discussion forum is established to be a forum for gavel-to-gavel discussion of political development in Nigeria, Africa’s largest democracy.
Culled from : Dandalin Siyasa (An online discussion forum) in promotion of democracy and good governance in Nigeriafrom 2008 to 2010
Monday, 16 December 2013
Rahoto: Yadda Taron Dandalin Siyasa Ya Gudana A Zamfara
Al’ummar yankin Arewacin tarayyar Nijeriyar yau sun baje kolin hajar ra’ayoyinsu kan mabanbantan matsaloli, kalubale da kwan-gaba-kwan baya da ke addabar yankin wanda kai tsaye za a kwatanta da ukubobin mulki irin na gashin ragon layya da talakawa da al’ummar kasa ke fuskanta karkashin mulkin jam’iyyar PDP.
Wannan ya biyo baya ne a babban taron Dandalin Siyasa na kasa karo na biyar da aka gudanar a Gusau birnin jihar Zamfara a makon da ya gabata a karkashin daukar nauyin Gwamnatin Abdul-aziz Yari Abubakar.
A karshen taron bayan musayar ra’ayi, tattaunawa da gabatar da mukalu Dandalin Siyasa ya fitar da takardar bayan taro wadda ta yi bayani dalla-dalla kan matsayar da manbobin Dandalin suka cimma bakidaya.
Taron tattunawa kan makomar kasa da Gwamnatin Tarayya ta kudiri aniyar gabatarwa ba zai samar da wata mafita ko wani gyara ga matsalolin da Nijeriya da ‘yan Nijeriya ke fuskanta ba. Dandalin ya ce taron ba ya da kowane irin alfanun da zai magance dimbin matsalolin da kasa ke fuskanta don haka suka yi kiran da a soke taron bakidaya.
Bugu da kari Dandalin ya kuma yi magana kan manyan matsaloli da kalubalen da ke addabar yankin Arewa da suka had da; fatara da koma baya a fannin ilimi da tabarbarewar sha’anin tsaro da rashin cikakkiyar dama a lamurran siyasa.
Haka ma wasu abubuwan da Dandalin ya cimma matsaya a kansu su ne; babu sadaukar da kai a siyasar Nijeriya, haka ma siyasar tana cikin mawuyacin halin da ke bukatar a sake daidaita lamurra. A kan wannan bayanin ya nuna bukatar da ke akwai ta zaben shugabanni nagari wadanda za su tafiyar da mulkin gaskiya a tafarkin gaskiya.
Dakta Usman Muhammad, Malami a jami’ar Abuja shine ya karanta takardar bayan taron wadda a ciki kuma ta yi kira ga majalisar tarayy da ta yi fatali da batun dokar hukuntan wadanda ke suka da caccaka a dandalin sadarwa na zamani. A kan wannan bayanin ya yi kira ga masu shata dokoki daga yankin Arewa da kada su aminta a tabbatar da dokar.
Baya ga wannan Dandalin ya bayyana cewar babu wani kwakkwaran amintaccen dan siyasa daya da ya samu karbuwa, goyon baya da amincewar jimlatan din al’ummar Arewa, wanda akan wannan bayanin ya nuna bisa ga bayyanar Dandalin Siyasa akwai kyakkyawan tsammanin Arewa da ‘yan Arewa za su samu ingantaccen dan takarar da zai samu karbuwa a yankin bakidaya.
A jawabin da ya gabatar a matsayinsa na mai masaukin baki, Gwamna Yari ya bayyana cewar a bisa ga gazawar Gwamnatin tarayya wajen magance satar man fetur, da rabon tattalin arzikin kasa da ake yi yadda aka ga dama don haka taron tattaunawa na kasa da za a gudanar ba zai haifar da da mai ido ba ga siyasar Nijeriya. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ta bakin mataimakisa Ibrahim Wakkala.
A nasa jawabin Gwamna Kwankwaso na jihar Kano shi kansa ya yi kakkausan kira ga al’ummar Arewa da su kauracewa Babban Taron na Kasa yana mai cewa “Ko kadan taron ba ya da wani amfani a garemu don haka muke kira da a kaurace masa.
Baya ga wannan jagoran na Kwankwasiyya wanda Sakataren Gwamnatin jihar Kano, Rabi’u Sulaiman Bichi ya wakilta ya yabawa hobbasar kwazon Dandalin Siyasa na fadakar da shugabanni da jagororin siyasar yau kan halin ha’ula’in da al’ummar kasa suke ciki.
Shugaban Dandalin Siyasa Hashimu Ubale Yusuf bai yi kasa a guiwa ba wajen bayyana yadda Dandalin ya kafu a 2008 da ‘yan manbobi kalilan, amma a yau bisa ga gamsuwa da abubuwan da ake tattaunawa an wayi gari akwai dubban manbobin Dandali na yahoogroups da nashafin Facebook.
A taron an kuma aminta da karin wasu Manbobin Kwamitin Amintattu na Dandali ba ya ga wadanda ake da su. Wadanda aka tabbatar sune: Mataimakin Gwamnan Zamfara, Ibrahim Wakkala da Sakataren Gwamnatin jihar Kano, Rabi’u Bichi, da biyu daga cikin masu kula da Dandalin, Urwatu Bashir-Saleh da Uba Dan Zainab da Ahmad Sajo, daraktan yada labarai ga Gwamna Murtala Nyako na jihar Adamawa.
Tun da fari gabanin ranar babban taron sai da aka fara kai ziyara a ranar jumu’a a gidan Kurkuku da gidan Marayu ta yadda Dandalin ya bayar da tallafin tufafi da kayan amfanin yau da kullum ga wadanda abin ya shafa domin tausaya masu ga halin da suke ciki tare karfafa masu guiwar samun kyakkyawar makoma a gaba. Kazalika domin neman albarkar masu albarka, haka ma an kai gaisuwar girma a gidan Mai Martaba Sarkin Katsinan Gusau.
Baya ga wannan kuma a daren ranar babban taron, Gwamna Yari ya jagoranci cin liyafar musamman a fadar Gwamnatinsa a inda aka ci a ka kuma sha abincin alfarma a gidan alfarma a bisa ga bakuntar bakin mai alfarma.
Baya ga wannan haka ma a ranar lahadi Kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara Ibrahim Muhammad Birnin-Magaji ya jagoranci shugabannin Dandalin a ziyarar gani da idanu kan muhimman ayyukan raya kasa da ci gaban al’umma da Gwamnatin Shehi ta gudanar a Zamfara daga 2011 da ta fara jan zaren mulk zuwa yau.
Wakilinmu ya ba mu labarin Dandalin Siyasa wani fitaccen Dandali ne da a farko aka asasa a yahoogroups a duniyar gizo inda jama’a da dama ke baje kolin hajar ra’ayoyinsu kan mabanbantan al’amurran da suka jibanci siyasa, zamantakewa da tattalin arziki, da sauran batutuwa da dama da suka shafi cigaban kasa da matsalolinta da ma hanyoyin magance su.
Daga baya ne aka fadada shi ta hanyar buda shafin Facebook na Dandalin Siyasa. A haka ya zuwa lokacin hada wannan rahoton akwai manbobin Dandalin Siyasa na yahoogroups 1, 964 da kuma wasu manbobi 6, 733 da ke a shafin Facebook wadanda duka sun fito ne daga ko wane lungu da sakon Nijeriya, haka ma akwai manbobin da ke a sauran sassan kasashen duniya.
Bugu da kari Dandali ya hada jama’a da dama daga jam’iyyun siyasa daban-daban, wadanda duka ke musayar ra’ayi tare da muhawarori masu ma’ana ba tare da amfani da zafafan kalamai kan wani ko wasu ba, kamar yadda dokar Dandali ta shata, a daya gefen tare da bin dokar kasa ta ‘yancin fadin albarkacin baki.
A cikin Dandalin akwai zaratan shugabannin siyasa, ‘yan siyar akida, ‘yan siyasar zaure da ‘yan siyasar da ke iya azata ta zauna, baya ga manya, matsakaita, da kananan ma’aikatan Gwamnati, da ‘yan kasuwa, da masu mulki da masu iko da ‘yan Rabbana ka wadata mu, da dalibai da Malamansu da sauran mabanbanta al’umma maza da mata.
Fassarar Sharafaddeen Sidi Umar da Hussaini Ibrahim, Gusau.
Culled from Leadership Hausa
Bakuncin Gizago a Jihar Zamfara
Rabona da shiga cikin birnin Gusau na Jihar Zamfara tun mulkin Yariman Bakura na farko, kodayake na sha zuwa, amma dai shigar shantun kadangare nake mata, domin kuwa nakan wuce in je Sakkwato, ba tare da na shiga kwaryar garin ba.
A wannan karon, na niki gari a ranar Juma’ar da ta gabata, na tunkari birnin. Babban makasudin zuwa Gusau kuwa shi ne, domin halartar taron ‘Dandalin Siyasa A Intanet’ karo na biyar, wanda Gwamnatin Jihar Zamfara ta dauki bakuncinsa.
A matsayina na wanda ya dade bai rakade birnin Gusau ba, sai na samu kaina a matsayin bako, wanda haka ya sanya al’amura da yawa suka zame mani abin al’ajabi. Na farko dai, na samu garin ya canza matuka daga yadda na san shi a baya. Na ga yadda aka shimfide shi da manyan tituna masu gida biyu da magudanun ruwa a kowane bangare. Haka kuma, na ga yadda sababbi kuma manyan gine-gine suka cika birnin, kamar kuma yadda na ga an dandashe mahada titunan da fitulun ba da hannu.
Game da hanyoyin nan kuwa, masu ababen hawa, musamman ma ’yan baburan Acaba, har ma da wasu masu motocin tasi, na ga yadda suke karya dokokin hanya kai tsaye. Na ga yadda suke yin tukin ganganci da wauta. Akwai lokacin da na zo shataletalen kusa da Gidan Gwamnati, fitilun bayar da hannu sun ba hanyarmu izinin tafiya amma sai ga shi ’yan Acaba da wasu kalilan din motoci sun shiga titi daga hannun da ke daura da namu (wanda kamata ya yi su tsaya). Bisa ga haka, saura kadan in kade wani mai babur amma Allah Ya kiyaye, na dauke kan motata da sauri. Da baicin taimako da agajin Allah, da yanzu labari ya cika gari, cewa Gizago ya kade dan Acaba, (Allah Ya kiyaye)!
Wani abu kuma da ya daukar mani hankali game da Jihar Zamfara shi ne, yadda na rika jin mutane suna yaba wa gwamnatinsu mai ci a yanzu, a karkashin Gwamna Alhaji Abdul’aziz Yari Abubakar, musamman suna cewa yana yi masu ayyukan raya kasa. Da nake magana game da titunan da na ga sun kayata birnin, shi ne wani ma’aikacin otel din da na sauka ya shaida mani cewa ai duk aikin gwamnan ne mai ci yanzu.
Al’amari na gaba da ya kara daukar mani hankali shi ne, abin da na tsinkaya a daren Lahadi, lokacin da aka gudanar da liyafar cin abincin dare tare da Gwamna Abdul’aziz Yari. An gudanar da liyafar ce a Gidan Gwamnatin Jihar Zamfara. Bayan an kammala cin abinci da abin sha, sai aka gayyaci gwamnan domin ya gabatar da jawabinsa. Jawabin nan nasa ne ya zama abu na gaba da ya doki zuciyata, ya daukar mani hankali matuka.
Gwamnan ya bayyana yadda yake tafiyar da al’amuransa, sannan ya yi bayani dalla-dalla game da hakkin da ke kansa, kamar kuma yadda ya tunatar da al’umma cewa su ma suna da hakki. Ya ta’allaka yadda ake samun matsaloli da yawa daga shugabanni a Najeriya da rashin sanin makamar aikin da ke kansu. Ya ce a wannan zamani da muke ciki, mafi yawan masu rike da madafun iko, suna samun kansu ne kawai a mulki, ba tare da sun shirya masa ba.
Game da haka, ya shawarci al’umma da cewa, duk wani abu da za su aikata, to su samu iliminsa tukunna. Mai mulki, ya yi kokarin sanin makamar aikin da ke gabansa.
Wani kalamin da gwamnan ya yi, wanda kuma ya dauki hankalina, shi ne inda ya ce dole ne mai mulki ya yi taka-tsan-tsan da mabiyansa, wadanda a mafi yawan lokaci sukan wuce makadi da rawa wajen zuga shugaba, su nuna masa cewa shi ne shugaban kowa kuma ya fi kowa. Gwamnan ya ce, a lokacin da shugaba ya biye masu, ya dauki wannan zuga da ingiza-mai-kantu-ruwa, to zai kasance mai girman kai. Idan ya yi haka, to barna za ta biyo baya.
Abu na gaba da ya daukar mani hankali a Jihar Zamfara, shi ne ganawarmu da Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Zamfara, zakakurin mutum mai himma, Alhaji Ibrahim Muhammad (dan Madamin Birnin Magaji). A matsayinsa na daya daga cikin jami’an gwamnati da suka kasance masu masaukin baki a taron nan, bai nuna gazawa ba ko kadan. Duk inda ake wata hidima a taron nan sai ka gan shi tsamo-tsamo, ana tafiyar da al’amura da shi.
Saboda azamarsa, shi ya jagoranci membobin dandali da suka zo taron nan daga sassan kasar nan zuwa ziyarar gani da ido zuwa wasu muhimman ma’aikatu, domin shaida ingantattun ayyukan raya kasa da gwamnatinsu ta gudanar.
Kwamishinan da kansa ya jagorance mu zuwa Gidan Rediyon Jihar Zamfara, wanda ake kira da sunan Gidan Injiniya Mamman Maru. Mun ga sababbin na’urori na zamani, wadanda aka shaida mana cewa su ne ake yayi a duk fadin duniya. A takaice, ya shaida mana cewa, gwamnatin Abdul’aziz Yari ce ta kashe kudi har Naira biliyan daya, wajen kammala ginin gidan rediyon da kuma inganta shi da wadannan na’urori na zamani.
Ziyayar tamu ta dauke mu har zuwa Asibitin kwararru na Yariman Bakura, wanda shi ma aka inganta shi da na’urori na musamman, wadanda suka hada da na’urar gwajin yanayin sassan jiki, wadda da ita ake gwajin gano ciwon koda, ciwon suga da sauransu. Mun ga na’urar gwajin haihuwa ta zamani, mai aiki da hasken lantarki, wacce idan aka haska za a iya tantance yanayin ciki da sauran lalurorinsa. Mun ga na’urarori daban-daban, wadanda ya ce irinsu ne ake samu a manyan asibitocin zamani na kasashen duniya.
Kamar yadda ya ce, duk wani awo da ake gudanarwa a asibitin, Naira dari biyar suke amsa, domin saukaka wa talakawa. Ya ce gwamnatin tasu, ta kashe sama da Naira biliyan biyu wajen kammala ginin asibitin da kuma inganta shi da na’urori.
Daga nan ne kuma muka rankaya zuwa gadar boko, wadda kamar yadda Kwamishinan Watsa Labarai ya ce ake ginawa a halin yanzu. Wannan gada, hade da hanya mai nisan kilomita 75, za ta hada kananan hukumomin Talatar Mafara da Bakura da Maradun da Zurmi. Ya ce an bayar da kwangilar gina ta a kan Naira biliyan 7.1 kuma za a kammala ta cikin shekara uku, saboda muhimmancinta ga al’umma, musamman wajen bunkasa kasuwanci da noma da kiwo.
Mun yi wa Kwamishina dan Madamin Birnin Magaji Tambayar cewa, ta yaya ake samun dinbin kudin da ake aiwatar da wadannan muhimman ayyuka? Shi ne ya amsa da cewa: “Gwamnanmu ya dakile duk wasu hanyoyi na almubazzaranci da dukiyar al’umma, yana ririta dan abin da ake samu daga Gwamnatin Tarayya.”
Babu shakka na ji dadin bakunci na a Jihar Zamfara, musamman ma yadda na gana da Gizagawan Jihar Zamfara da na Jihar Sakkwato, su Yusuf Zamfara da su Kassim Lema da su M. A. Faruk da Nata’ala Babi da su Jamila Abubakar da Hussaina Abdullahi. Haka kuma, na hadu da zaratan Gizagawan Jihar Kaduna, irinsu Muntaka Abdul Hadi Dabo da Idris Barden Kubau da sauransu. Babu abin da zan ce, sai Allah Ya bar zumunci!
Culled from Aminiya
http://aminiya.com.ng/index.php/gizago/4053-bakuncin-gizago-a-jihar-zamfara
Subscribe to:
Posts (Atom)