Monday, 16 June 2008

YUNKURIN JANAR JANAR NA WANKE ABACHA: IHU BAYAN HARI!

Ranar 8 ga watan Yuni, tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha ya cika shekaru goma da rasuwa. Kamar kowane shekara iyalan marigayi Janar Sani Abacha kan gabatar da addu’oi a irin wannan ranar . Amma abinda yafi jan hankali a addu’ar na bana shine haduwar tsofin shugabanin kasa na soja wato Janar Muhammadu Buhari da Janar Ibrahim Babangida da Janar Abdulsalam Abubakar, inda kowanen su ya fito karara ya karyata zargin da akeyi na cewa marigayi Janar Sani Abacha yayi rub da ciki da dukiyar al’umma yayin da yake mulki.

Kafofin watsa labarai sun ruwaito Janar Muhammadu Buhari na fadin cewa “dukkan zargin da akewa Janar Sani Abacha zai kasance zargi ne kawai”. Shi kuma Janar Ibrahim Babangida na cewa “ zargin da akewa Abacha basu da tushe balle makama…kuma babu kanshin gaskiya na cewa yayi almudahana da dukiyar al’umma”. A inda shi kuma Janar Abdulsalam Abubakar ke cewa “ abin takaici ne da rashin adalci a zargi iyalan marigayi Sani Abacha da satar dukiyar al’umma”.

Wannan yunkurin na Janar Buhari da Babangida da Abubakar na wanke marigayi Janar Sani Abacha daga zargin wawushe baitul malin gwamnati ya baiwa jama’ar kasa mamaki saboda basu fito sunyi wannan jawabin ba sai bayan shekaru goma da rasuwar sa. Duk da suna raye , suna ji , suna gani a lokacin gwamnatin baya da take ta shela tana sanar da duniya irin magudan kudaden da take karbowa a matsayin boyayyun kudade daga bankunan cikin gida da kasashen waje da marigayi Abacha ya boye.

Jaridar Thisday ta ranar 5 ga watan Yuni 2008 , ta larabto cewa kasar Switzerland ta fadi cewa ta maido wa gwamnatin Nijeriya dukkan kudaden sata da marigayi tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha ya boye a bankunan kasar ta , ba tare da wani sharadi na yanda za’a kashe kudaden ba. Jaridar ta ruwaito Ma’aikacin ofishin jakadacin na kasar Switzerland a Nijeriya , Mista Fabio Baiardi na cewa , sun maido wa Nijeriya kudade a kashi-kashi , yace a kashin farko sun bada dala miliyan 290 ranar 1 ga watan Satumba na 2005, sannan kashi na biyu sun bada dala miliyan 168 a ranar 19 ga watan Disamba na 2005, sai kashin karshe, dala miliyan 40 a karshen watan Janairu na 2006.

Bayanai na nuni da cewa Nijeriya tayi nasarar karbo dala miliyan 505.5 daga gwamnatin kasar Switzerland cikin kudaden da ake zargin Janar Sani Abacha ya sace tare da boye su a kasar kamar yanda bayanan da Ofishin majalisar dinkin duniya mai yaki da miyagun kwayoyi da laifuffuka da kuma bankin duniya suka bayar karkashin sabon yunkuri da ake kira da Stolen Asset Recovery (STAR ). Sannan ta bangaren gwamnatin Nijeriya anyi bayanin cewa an karbi kudi har dala miliyan 800 daga cibiyoyin hada-hadan kudi na cikin gida, cikin dala biliyan 3 zuwa 5 da ake zargin marigayi Janar Sani Abacha ya wawure, an kuma bada kiyasin cewa an karbi jimalar kudi dala biliyan 1.3 cikin kudaden.

In har zancen Janarori ya kasance gaskiya to ina kasar Switzerland ta sami miliyoyin dalolin data maidowa Nijeriya a matsayin kudaden da marigayi Janar Sani Abacha ya boye a bankunan kasar ta? Sannan ofishin majalisar dinkin duniya da bankin duniya ina suka sami bayanan da suka bayar kan kudaden da aka karbo na marigayi Janar Abacha? Su kuma (Janarori) ina suka sami nasu bayanan na cewa Janar Sani Abacha bai wawuri dukiyar Nijeriya ba?

Abin tambaya a nan shine me suke so su cimma da wannan furucin nasu na wanke Janar Abacha bayan shekaru goma ? In har tsofin shugabanni uku sun isa su bada sheda na wanke wanda ake zargi, to lallai sai yan Nijeriya su amince da shedan da tsofin shugabannin kasa uku wato Janar Yakubu Gowon da Alhaji Shehu Shagari da Cif Earnest Shonekan zasu bayar kan tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo kan yanda ya tafiyar da dukiyar Nijeriya daga 1999 zuwa 2007.

Yan Nijeriya na bukatar sanin gaskiyar lamari game da zargin satan dukiyar kasa da gwamnatin baya ke zargin marigayi Janar Sani Abacha dayi. Tunda har Janarorin sun fito a yanzu su shedi cewa Janar Abacha bai saci dukiyar al’umma ba, sai su kara wa yan kasa haske dan suyi watsi da bayanan da suka fito daga kasar Switzerland a matsayin kazafi ga marigayi Janar Sani Abacha.



Shehu Mustapha Chaji

shehuchaji@yahoo.com

No comments:

Post a Comment