Tuesday, 10 June 2008

Kano 2011: Da sassafe ake kama fara

Ba’a bori da sanyin jiki, da alamun wannan Karin Magana ke sa yan siyasar jihar Kano dake da burin gadar gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau bayan ya kamala wa’adin mulkin sa a zango na biyu keta shirye-shiryen ganin ko zasu dace. Wasu cikin masu kokarin ganin cewa sun gaji Gwamna Shekarau tuni suka fara nuna kansu ta hanyar kaddamar da kamfen ta bayan gida ta hanyoyin da suke ganin yafi dacewa a gare su dan samun goyon bayan al’ummar jihar Kano.
Cikin sahun gaba na masu son shige gidan gwamnatin jihar bayan Gwamna Shekarau ya nade kayan sa a shekarar 2011, sune yan jam’iyyarsa ta ANPP . Sannan yan jam’iyyun adawa musamman yan jam’iyyar PDP , sai kuma yan jiran ganin yadda guguwar siyasar zata kada kafin nan da shekarar 2010.
Mafi yawan yan takarar gwamnan jihar Kano dake nuna kansu ko kuma suke da niyyar tsayawa takara a shekarar 2011 in Allah ya kaimu sune manyan jami’an gwamnati da gaggan yan jam’iyyar ANPP me mulki a jihar. A sahun gaba na masu neman mukamin gwamnan a jihar sune Aljaji Sani Lawan Kofarmata, limamin Allah ya maimaita, Darakta Janar na Hukumar alhazai na jiha da Injiniya Abdullahi Muhammad Gwarzo mataimakin gwamna da Alhaji Garba Yusuf na hannun daman Gwamna Shekarau kuma kwamishina a gwamnatin sa da Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso kwamishinan raya karkara kuma kakakin jam’iyyar ANPP na jihar Kano da Injiniya Sarki Labaran kwaminishan aiyuka da Alhaji Abdullahi Sani Rogo .
Kazalika Sanatocin jihar a majalisar dattijai na kasa wato Sanata Kabiru Gaya da Sanata Muhammad Bello da Sanata Aminu Sule Garo ba’a barsu a baya ba wajen ganin cewa ko zasu dace su gaji Gwamna Shekarau ba. Tun dawowar tsarin dimokaradiya a shekarar 1999 tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Kabiru Gaya keta hankoran ya sake komawa gidan gwamnatin jihar amma hakar sa bata cimma ruwa ba. In da rai da rabo, ba shakka kila ya sake jarraba sa’ar sa a zaben 2011. Shi kuma Sanata Muhammad Bello tun shekarar 2003 yake ta kokarin ganin cewa ya shige gidan gwamnatin jihar, kuma tun dawowar sa jam’iyyar ANPP yake ta kokarin ganin cewa ya sami gindin zama kuma hakan yasa yayi taka tsan-tsan wajen kaucewa karo da Gwamna Shekarau duk da radi-radin da ake tayi na cewa yana da sha’awar kujerar gwamnan jihar kafin zaben 2007.Shima ana ganin cewa tunda gwamna Shekarau zai bar mulki a shekarar 2011 to shima zai jarraba farin jinin sa ga al’ummar jihar Kano ganin yadda ya shafe shekaru yana yi da dukiyar sa wajen karfafa jam’iyyar ANPP a jihar da taimakawa jama’a da kungiyoyi a jihar. Shi kuma Sanata Aminu Sule Garo tun kafin zaben 2003 yake da sha’awar fitowa takarar gwamnan jihar Kano amma a lokacin abokin sa Alhaji Ibrahim Amin Little ya sha gaban sa a lokacin .Shima da alamun wannan karon zai sake yinkurawa ko zai dace a wannan karon. Sai dan majalisar tarrayya Alhaji Danlami Hamza wanda a yanzu yana zango na uku a majalisar yana cikin wadanda suke da sha’awar zama gwamna a 2011.
Suma wadanda suka canza sheka daga wasu jam’iyyun zuwa jam’iyyar ANPP ba za’a bar su a baya ba wajen neman takarar gwamna a karkashin jam’iyyar ANPP ba a shekarar 2011. Cikin su akwai Alhaji Barau Jibrin tsohon dan majalisar tarayya kuma na hannun dama a daga tsohon kakakin majalisar tarayya Alhaji Ghali Umar Na’abba da tsohon gwamnan jihar Kano Dakta Muhammadu Abubakar Rimi, sai Alhaji Shehu Yusuf Kura wanda yayi takarar gwamna karkashin jam’iyyar PDP da Dakta Bala Salisu Kosawa shima dan takarar gwamna karkashin jam’iyyar NDP.
Ta bangaren jam’iyyar PDP me adawa a jihar Kano wadanda ake ganin zasu shiga sahun gaba a takarar sun hada da Alhaji Ibrahim Amin Little da Alhaji Ahmed Garba Bichi ministan kasuwanci da Alhaji Ghali Umar Na’abba tsohon kakakin majalisar tarayya da Dakta Shamsudeen Usman ministan kudi da Alhaji Faruk Lawan dan majalisar tarayya da Alhaji Aminu Dabo da Alhaji Usaman Sule Ruruwai dan takarar jam’iyyar A.C a zaben 2007.
Ta bangaren magoya bayan Janar Muhammadu Buhari a jihar Kano suma zasu fito da karfin su saboda da zarar abinda suke jira ya tabbata na matsayin da Buhari zai dauka bayan hukuncin kotun koli zasu kara kaimi wajen ganin cewa dantakarar gwamnan jihar Kano da zasu mara wa baya mai goyon bayan Janar Buhari ne.Burin magoya bayan Janar Buhari a jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Haruna Ahmadu Dan Zago shine na samin gwamna me goyon bayan Janar Buhari a jihar Kano a shekarar 2011.
Sai dai da alamun cewa takarar na gwamnan Kano a shekarar 2011 zai iya zuwa da sarkakiya in har ta tabbata Gwamna Ibrahim Shekarau ya canza sheka zuwa jam’iyyar PDP kafin zaben 2011 , inda ko yayi nasara wajen tsaida magoya bayan sa a takara har dana gwamna yanda tsohon gwamnan jihar Kebbi SSanata Adamu Aliero ya sami nasarar yi bayan ya koma jam’iyyar PDP ko kuma ya sami nakasu kamar yanda tsohon gwamnan jihar Jigawa Sanata Saminu Turaki ya samu inda yan jam’iyyar PDP na asali karkashin jagorancin Gwamna Sule Lamido suka mamaye takarar da mukamai masu tsoka suka sha gaban Sanata Saminu Turaki . In har ta tabbata Gwamna Shekarau ya koma jam’iyyar PDP jam’iyyar zata kwashi ruguntsumin banbancin ra’ayi tsakanin gaggan jam’iyyar inda zai sami Tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso da tsohon gwamna Abubakar Rimi wanda kowannen su zai yi kokarin ganin cewa dan takarar sa na gwamna ne ya sami tikitin tsayawa takarar gwamna. Sannan akwai yan takara masu jinni a jika kamar su Alhaji Ibrahim Amin Little da Alhaji Ghali Umar Na’abba da zasu yi kokarin tabbatar da ikon su saboda kada ayi masu sakiyar da babu ruwa kamar yanda akayi masu a zaben fidda gwani na shekarar 2007.
Yanda Gwamna Shekarau ya tafiyar da gwamnatain sa a shekaru biyu masu zuwa zai iya bashi damar ko rashin damar tsaida tsaida wanda yake so ya gaje shi a shekarar 2011. Jam'iyyar sa ta ANPP a kasa na fuskantar durkushewa gaba daya saboda rigingimun cikin gida ga kuma barazanar mamayar PDP data tinkaro yankin Arewa maso Yamma yankin da Shugaba Yar'adua ya fito inda jam'iyyar keso ta tabbatar da ikon ta saboda Shugaba Yar'adua.
Al'ummar jihar Kano na lura da bibiyar yanayin siyasar dake gudana, in kuma Allah ya kaimu lokacin zasu duba su darge su dauki wanda suke ganin yafi dacewa ya jagoranci jihar a shekarar 2011. Ko su amince da duk wanda gwamna Shekarau ya nuna masu ko kuma su zabi wani daban albarkacin Shugaba Umaru Yar'adua ko kuma su sake amincewa da wanda Janar Muhammadu Buhari zai nuna masu kamar yanda yayi a shekarar 2003. Amma kuma ko su a kan kansu zasu duba wani daban a kan kansa da suke ganin shi yafi dacewa da cancanta dan samun romon dimokaradiya da ake ta tababa ko tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso da Gwamna Ibrahim Shekarau basu baiwa al'ummar jihar ba a lokacin mulkin su lokaci ne kadai zai bayyana.

Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com

No comments:

Post a Comment