Saturday, 26 July 2008

Rayuwan yan siyasa da talakawa na kara tazara!

Irin makudan kudaden da ake samu a harkar siyasa a yau ya sanya siyasa kan gaba wajen harkar da tafi kawo kudi a yau a Najeriya. Manoma da yan kasuwa da ma’ikatan gwamnati a yau ko kusa basa samun kudin shiga kamar yan siyasa. Makudan kudaden da yan siyasa ke samu daga albashin su da alawus-alawus zuwa maikon dake tattare da kujerar da suke kai ya sanya su a sahun masu hannu da shuni. A yau babu dan siyasa daga Kansila zuwa sama da bai bawa miliyoyi baya ba !



Shi kuma talakan Najeriya a kullum sai kara talaucewa yake yi. Hauhawan farashin kayayyaki da rashin aikin yi da rashin tabbas kan aiki da sana’oi da kuma karancin albashi ya sanya talaka na rayuwa cikin matsi duk da dinbin arzikin kasa daga ma’adinai da kudin shiga da gwamnati ke samu a kullum.



Banbancin rayuwa tsakanin yan siyasa da talakawa na kara nisa a kullum. Duk da cewa Malaman makarantu sun shiga yajin aiki kan batun Karin albashi da gwamnati har yanzu taki sauraron su saboda wasu dalilai da hankali ba zai kama ba. Su kuma yan siyasa an kara masu albashi da alawus-alawus na miliyoyin nairori.



Ya’yan talakawa a yau nata garanramba da tallace-tallace da aikin leburanci da bara sakamakon yajin aikin malaman makaranta. Su kuma ya’yan yan siyasa daga Shugaban Kasa zuwa Kansila suna karatun su a makarantu masu zaman kansu masu tsada. Daga Shugaban kasa zuwa Mataimakin sa da ministocin da yan majalisar tarayya da shugabannin su da gwamnonin jihohi da kwamishinonin su , waye a cikin su da ya’yan sa ke zuwa makarantun gwamnati kuma wannan yajin aikin ya shafe su? In an sami daya cikin wadanda na lissafa a baya ya’yan sa na zuwa makarantun gwamnati , to a shirye nake ayi mani bulala guda goma.



In har yan siyasa zasu sami Karin albashi da alawus-alawus har sau biyar daga 1999 zuwa yau, su kuma talakawan kasa fa? Ko su basa bukatar Karin albashi ne? Nawa ne mafi karancin albashi? Kuma nawa ne kudin buhun shinkafa a yau? Sannan ga kudin cefane na yau da kullum da kudin haya da sufuri da asibiti da makaranta da wutan lantarki da ruwa da sauran su.



A yaushe zamu daina munafunci da yaudara a kasar mu? Kowa ya san cewa albashin da ake baiwa ma’aikata a Najeriya baya isar su biyan muhimman bukatun rayuwan yau da kullum. Su yan siyasa sun fi zama yan Najeriya ne kan talakawa? Sannan su yan siyasa wasu mutane ne na musamman? Wasu sun fi wasu muhimmanci ne a bada gudunmawar gina kasa?



In banda zalama da son kai irin na yan siyasar Najeriya me zai hana su yin amfani da mukaman su wajen aiwatar da ayyukan da zai rage ko kawo karshen wahaloli da kuncin rayuwa daya dabaibaye talakawan su da kuma bada kyakyawan misali? Romon dake tattare da mukaman da suke kai nada yawan gaske, inda suke more gidan kwana da motoci da kiwon lafiya da abinci da sutura da duk kayayyakin more rayuwa a kyauta. Amma saboda son kai dan bukatun da talakawa ke bukata dan tallafa masu a rayuwar yau da kullum an hana su. Bukatun talaka kadai ke gamuwa da rashin kudin da tsuke bakin aljihun gwamnati. In kuma suka dage kan neman biyan bukatun su sai ayi masu barazana da rage ko korar su daga aiki.



Talakawan Najeriya sun kasance masu hakuri da dogaro ga Allah wanda hakan ya sanya su basa daukan rayuwa da zafi. Buri da bukatar talaka bai wuce samun abinci sau uku a rana ba da samun halin biyan kudin haya da samun kyakyawan yanayin da zasu gudanar da harkokin neman halaliyar su na yau da kullum. Su kuma iya biyan kudin makarantan ya'yan su da magungunan da akan rubuta masu su saya a asibitoci da sauran su. In talaka zai iya biyan bukatun dake gaban sa , to yan siyasa suje suyi duk abinda suka gan dama da dukiyar kasa. Me yasa yan siyasa suka zama mugaye marasa tausayi da imani? Me zai sa mutum daya shi kadai ya saci biliyoyi da bazai iya amfani dasu ba ya kaisu bankunan kasashen waje ya boye? Yan siyasar Najeriya su kwan da sanin cewa zalunci da yaudara ba zai dore ba , saboda wata rana talaka da ake zalunta zai fahimci banbanci tsakanin hannun hagun sa da dama.



Rashin yarda da zargi da kiyayya nata yaduwa a ko'ina cikin kasar nan kan yan siyasa. Talakawa sun kasa fahimtar me ake da biliyoyin dalolin da kasar ke samu albarkacin hauhawan farashin man fetur a kasuwar duniya. Wasu kasashe cikin wadanda suke cin gajiyar hauhawan kudin man fetur har su kaddamar da gina sababbin birane guda biyar , yayin da wasu suke amfani da nasu wajen gina masana'antar nukiliya dan samar da makamashi. Mu kuma a nan talakawa na cigaba da rayuwa cikin yunwa da rashin abubuwan more rayuwa. Ya kama yan siyasa su gaggauta kaddamar da aiyuka da manufofin da talaka zai shedi cewa yana da shugabanin masu tausayi da sanin ya kamata.



Yan siyasar dake tafiyar da al'amurran mulki daga gwamnatin tarayya da jihohi zuwa kananan hukumomi duk sun gaza wajen aiwatar da ayyukan cigaba kwatan-kwacin makudan kudaden da suke rabawa a tsakanin su. Babu kyawawa da ingantattun hanyoyi da ruwan sha da ilimi da kiwon lafiya da wutan lantarki da sauran su. Kuma sun gaza warware matsalar rashin aikin yi da ya maida matasa majiya karfi almajirai da masu aikata laifuka da karuwai da kuncin rayuwa. Matsalar rashin aikin yi ya dauki sabon salo inda ake tatsan su kudade dama iya rasa rayukan su a wajen neman aiki.



Sauran yan Najeriya kamar yan siyasa na bukatar a basu damar su da hakkokin su da cika aiki maimakon dogon turanci da kyautata niyya maimakon yaudara da mulkin adalci da zabe na gaskiya. Abin takaici ne ace yan siyasa suki cika alkawarukkan da suka yiwa talakawa yayin neman kuri'ar su . Yan siyasa masu ci a yanzu basu da wata hujja na kasa yin aiyukan cigaba saboda makudan kudaden da suke samu a yanzu.



Duk kasar da take son taci gaba ya wajabta ta kashe kudade masu yawa wajen bunkasa harkan ilimi , da wannan nake kira ga Shugaban Kasa Alhaji Umaru Musa Yar'adua inda gaske yake kan aiwatar da kudirorin sa guda bakwai da ilimi ke da matukar muhimmanci daya gaggauta nuna misali ta fitar da ya'yan sa daga makarantu masu zaman kansu ya maida su na gwamnati, sannan ya umarci jami'an gwamnatin sa da yan jam'iar sa suma suyi hakan, kuma ya biya dukkan bukatun malaman makaranta . In yayi haka cikin lokaci kadan zamu gan canji me yawa a fannin ilimi.



Yan siyasan Najeriya in basu sani ba , to su sani talakawa na kallon yadda suke rayuwar su cikin jindadi da kwanciyar hankali yayin da su suke rayuwa cikin duhu da rashin tsaro da rashin sanin makomar su a rayuwa. Suma talakawa kamar yan siyasa na bukatar rayuwan jin dadi dan su more romon dimokaradiyya a kalla kashi daya cikin goma na irin jin dadin da yan siyasa ke fantamawa a cikin sa.



Hazawassalam



Shehu Mustapha Chaji

shehuchaji@yahoo.com
08038222575

1 comment:

  1. Loved your site, Lee! Thanks for sharing Kami menyediakan berbagai macam obat seperti Obat kondiloma , Kencing Nanah , Wasir , Sipilis , Herpes , Diabetes

    ReplyDelete