YAR'ADUA ZAI ZAMA MAGAJIN OBASANJO KUWA ?
Alhaji Umaru Musa Yar'adua Gwamnan Jihar Katsina kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP shine mutumin da ake ganin cewa in so samu ne ga Shugaba Obasanjo zai so ya lashe zaben watan Mayu na wannan shekarar ya kuma gaje shi bayan ya kwashe shekaru takwas a fadar Aso Rock a matsayin Shugaban Kasar Nijeriya.
Shi dai Gwamna Yar'adua sabanin harsashen masana harkokin siyasa bisa harsashen su kafin zaben fidda gwani na jam'iyyar sa ta PDP baya cikin jerin wadanda ake ganin zasu taka rawa ta musamman a zaben 2007. Daya daga cikin dalilan da ake ganin cewa Shugaba Obasanjo ya natsu da ganin cewa Gwamna Yar'adua ya tsaya takara shine na nakasa kungiyar PDM da mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar ke takama da gadara da ita a matsayin kungiyar da tafi tasiri a jam'iyyar PDP wanda ta samo asali daga rawar da marigayi Janar Shehu Musa Yar'adua ya taka a siyasun baya.Sanmnan masana harkokin siyasa na ganin cewa shi Gwamna Yar'adua zaifi saukin juyawa gashi Shugaba Obasanjo yayin da ya koma gonar sa ta Ota bayan ya mika mulki.
Gwamna Umaru Yar'adua ya kasance cikin gwamnonin da ake ganin cewa sunyi wa jama'arsu aiyukan cigaba tare da rikon amana . Ba'a zargin sa da halin bera da babakere da handama da dukiyar al'umma tsawon shekarun da yayi yana mulkin jihar Katsina . Kuma gashi da tattali har ya adana biliyoyin nairori a asusun ajiyar jihar bayan aikace aikace kamar ya gina makarantu da asibitoci da hanyoyi da samar da abubuwan more rayuwa ga al'ummar jihar sa .
Tarihin siyasar sa ta faro ne a jamhuriyya ta biyu inda ya kasance cikakken dan sahun gaba a jam'iyyar PRP ta marigayi Malam Aminu Kano duk da cewa wansa na goyon bayan wata jam'iyyar daban. Ga wadanda suka kusanci Gwamna Yar'adua sun shede shi a matsayin mutumnin da bai dau rayuwa da zafi ba kuma abun duniya bai dame shi ba wanda ga alamu irin tarbiyar daya samu ne a kokarin sa na koyi da gwarzon sa a siyasan ce wato marigayi Malam Aminu Kano.
Shin kamannin Gwamna Yar'adua da muryar sa na iya sa a kalle shi a matsayin wanda za'a iya juyawa? Shin Gwamna Yar'adua zai aminta da akidun jari hujja kan irin akidojin sa na da? Kan tambaya na ta farko muna iya samun amsoshin daga su Alhaji Lawal Kaita da Alhaji Iro DanMusa da Alhaji Musa Musawa da Alhaji Bello Masari da Jakada Magaji Muhammad da sauran jiga-jigan Katsinawa ko a jam'iyyar PDP ko a wasu fannonin . Al'ummar jihar Katsina kuma na iya bamu amsar mu kan irin akidun da Gwamna Yar'adua ke kai a yanzu.
Da ace siyasar wanda zai gaji Shugaba Obasanjo bata zo da tsarkakiya ba to da lallai Gwamna Yar'adua yana da cikakken kamala da sanin makaman aikin da jama'ar Nijeriya zasu mara masa baya domin zama Shugaban Kasa. Amma ya sami kansa a wani yanayi mai gargada da wuyan sha'ani domin na farko jama'a na ganin sa a matsayin dan amshin shatar Shugaba Obasanjo .A na yi masa ganin cewa Shugaba Obasanjo nason amfani dashi ne domin in ya gaje shi to duk abubuwan da suka faru a lokacin mulkin sa na ba daidai ba to ruwa tasha gajab. Sannan kuma shi zai ta juya shi a matsayin uban gidan sa.
Cikin yanayin gargadan da Gwamna Yar'adua ya sami kansa shine na cewa biyu daga cikin wadanda yake takara dasu yayu ne a gareshi wato Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar da Janar Muhammadu Buhari. Kamar yadda kowa ya sani Atiku Abubakar shine magajin marigayi Janar Shehu Yar'adua a siyasan ce kuma alakar Janar Buhari da marigayi Janar Yar'adua na tsawon shekaru ne tun suna yara wanda dangantakar ta juye ta zama yan'uwan taka .Gashi a yau Gwamna Yar'adua na gwagwarmayar neman mulki dasu .
Masu nazari kan harkokin siyasa na ganin cewa Gwamna Yar'adua baya taka wata muhimmiyar rawa a kamfen din neman shugaban kasa domin baya bayyana manufofin da zai aiwatar in aka zabe shi da ya wuce zancen zai cigaba da manufofin sauye sauye na shugaba Obasanjo in aka zabe shi .Mafi yawan yan Nijeriya na ganin cewa shekaru takwas na tsarin dimokaradiya karkashin jagorancin Shugaba Obasanjo bai kara masu komai ba face talauci da rashin tsaro da rasa ayyukan su a kullum da sunan sauye sauyen tattalin arziki . Ga matsalar rashin wutan lantarki da hanyoyin duk da biliyoyin nairorin da ake cewa an kashe domin ingantasu .Uwa uba karin kudin man fetur a koda yaushe wanda kesa hauhawan farashin kayyayaki da sufuri.
Kuma duk inda suka je kamfen Shugaba Obasanjo na babakere kai kace shine ke neman takarar sake zama shugaban kasa domin yana hana shi Gwamna Yar'adua sakewa ya wala ya mike kafa a matsayin sa na mai neman jama'ar Nijeriya su zabe shi a matsayin shugaban kasa . Amma wasu masu fashin bakin siyasa na ganin cewa kawaici da alkunya Gwamna Yar'adua yake yi kuma ba haka zai kasan ce ba in Allah ya kai damo ga harawa domin a tarihin siyasar Nijeriya ba'a faye wanyewa lafiya ba tsakanin ubangida da wanda ya mara wa baya ba. Suna kawo misali dashi Shugaba Obasanjo wanda wasu suka dauko shi daga kurkuku suka tsaya masa da kudi da mulki da jama'a amma yaya suka kare a yanzu?
Wasu suna ganin cewa a tsarin da jam'iyyar PDP ta shirya in Gwamna Yar'adua ya lashe zaben fidda gwani sun shirya duk yanda za'ayi a gan cewa Janar Muhammadu Buhari bai lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar sa ta ANPP ba inda suke zaton cewa ko Gwamna Ahmed Sani ko Gwamna Bukar Abba Ibrahim ne zai lashe zaben ganin cewa Janar Buhari bashi da goyon bayan gwamnonin jam'iyyar sa da shugabancin jam'iyyar amma sai abubuwa suka juye Janar Buhari yama lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar ANPP ba tare da wata hamaiya ba. Wannan nasarar ta Janar Buhari har ya janyo radi-radin cewa jam'iyyar PDP zata musanya Gwamna Yar'adua domin suna ganin cewa ba zai iya tinkarar Janar Buhari ba a zabe. Yayin da wani sashen masu tsage bakin siyasa na ganin cewa in har jam'iyyar PDP tayi halin data saba a zabe to dole Janar Buhari da Atiku Abubakar su hakura domin Gwamna Yar'adua kanin su ne.
Koma dame wasu na ganin cewa mafi muhimmmanci shine a raba Kuturu da Goraba ko a yarda mangoro a huta da kuda wato Shugaba Obasanjo ya bar mulki a ranar 29 ga watan Mayu na wannan shekarar ta 2007 kuma suna ganin cewa a'i mulki ya komo Arewa . Kuma har ila yau wasu na ganin cewa in har Gwamna Yar'adua zai kwatanta irin mulkin da yayi a jihar Katsina na cigaban al'umma to lallai za'a sami cigaba fiye da yadda Shugaba Obasanjo yayi a nashi mulkin.
Fatan talakawan Nijeriya shine na a gudanar da zabe na gaskiya ba tare da magudi ba domin cigaba da dorewar zaman lafiya da cigaba da bunkasar tsarin dimokaradiya. Shugabanci nagari ta samr wa talaka sauki a rayuwar sa na yau da kullum shine fatan sa.
Kira na ga Gwamna Umaru Musa Yar'adua kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP itace ya rage zancen cigaba da sauye sauyen tattalin arzikin shugaba Obasanjo ya bayyana wa yan Nijeriya nashi manufofin ko jama'a zasu aminta dashi su sake shawarar su inda basu yi niyar zaben sa ba su zabe shi tare da fatan cewa in shine mafi alheri ga talakawa da cigaban dorewar Nijeriya a kasa daya to Allah ya bashi sa'a.
Haza Wassalam
Shehu Mustapha Chaji
Thursday, 10 May 2007
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment