Friday, 11 May 2007

AN YA ATIKU ABUBAKAR ZAI GAJI OBASANJO?

Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar a makonnin da suka gabata ya sake jaddada wa Yan Nijeriya cewa tabbas zai fito takarar neman shugabancin kasa a shekarar 2007 . A zangon farko na wa'adin mulkin su da Cif Olusegun Obasanjo Atiku Abbubakar ya shedawa Yan Nijeriya cewa shi da Shugaba Obasanjo sunyi auren zobe kuma shi tamkar jakar hannun Obasanjo ne . Amma sai kwatsam a shekarar bara shi Shugaba Obasanjo ya zargi mataimakin sa Atiku Abubakar da laifin rashin biyayya a gareshi.

A tsarin dimokaradiya na kasashen da suka cigaba bisa al'ada mataimakin shugaban kasa kan samu amincewar shugaban kasa dan ya maye gurbin sa ba dan komai ba dan mataimakin ya cigaba da aiwatar da manufofin da yake kai . Me yasa shi Shugaba Obasanjo yadda ta bayyana karara da jam'iyyar su ta PDP basa son shi Atiku Abubakar ya gaji Obasanjo?

Masu nazarin harkokin siyasa na ganin cewa Shugaba Obasanjo na zargin mataimakin nasa da butulci saboda a takarar 1999 ba zato ba tsammmani Shugaba Obasanjo ya zabi Atiku Abubakar ya zama mataimakin sa alhalin ga fitattun yan siyasa a lokacin kamar su Dakta Abubakar Rimi da Malam Adamu Ciroma da farfesa Jibrin Aminu da sauran su . Kuma a wa'adin su na farko shi Shugaba Obasanjo ya sakar masa ayyukan gwamnati domin kullum yana kan hanyar tafiye-tafiye zuwa kasashen waje . Bai (Obasanjo) fahimci tasirin da mataimakin sa Atiku Abubakar ya samu ba sai da aka zo zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP a shekarar 2003 inda mafi yawa daga cikin gwamnonin jam'iyyar PDP suka tubure cewa su Atiku Abubakar suke so ya zama dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar ta su .Da kyar dai Shugaba Obasanjo ya sami damar shawo kan su suka mara masa baya ya tsaya wa jam'iyyar su takarar shugaban kasa .

Yan Nijeriya da dama suna ganin cewa Shugaba Obasanjo da mataimakin sa Atiku Abubakar Danjuma ne da Danjumai har sai lokacin da ta bayyana sun raba gari a lokacin da shi Atiku Abubakar ya kasance cikin yan sahun gaba a yakin tazarce . Masu nazari kan harkokin siyasa suna ganin cewa rawar dashi Atiku Abubakar ya taka a yakin tazarce ya sake jefa shi cikin tsaka mai wuya ta yadda har aka fito da bayanai da ake zargin sa da amfani da kudaden hukumar PTDF dan arzuta kai . Kuma ana ganin cewa ana son amfani da zargin ne domin in aka same shi da laifi to da wuya yama sami damar tsayawa takara balle ma ya kai ga gadar Shugaba Obasanjo .

Shin mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar zai haye bita da kullin da ake yi masa ? Shin bayanen dashi Atiku Abubakar yake yi na kare kansa bisa zargin da ake yi masa zai gamsar da al'ummar Nijeriya da hukumomin da zasu bincike shi ? Ta wacce hanya zai bi dan cimma burin sa a takaitattcen lokaci domin jam'iyyar sa ta dakatar dashi har tsawon wata uku ? In ya fito takarar zai yi tasirin da zai karbu a ko ina cikin kasar nan ? Sannan ko Atiku Abubakar zai fi Janar Buhari da Janar Babangida karbuwa dama ragowar yan takarar shugaban kasa musamman daga arewa ? Nazarin wadannan tambayoyi na iya haska mana irin rawar da(Atiku Abubakar) zai iya takawa da ko ya kai gaci ko a'a .

Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya fara fice ne a harkokin siyasar Nijeriya lokacin da Marigayi Janar Shehu Yar'aduwa ya tsaida shi takarar fidda gwani na shugaban kasa a karkashin jam'iyyar SDP a inda yazo na uku bayan Marigayi Cif Mashood Abiola Dda Alhaji Babagana Kingibe . Tauraron sa ta sake haskawa a lokacin zaben 1999 a inda ya lashe zaben zama gwamna a jihar Adamawa Cif Obasanjo ya zabe shi ya zama mataimakin sa inda suka lashe zaben shugaban kasa a shekarar 1999. Atiku Abubakar shine ake gani a matsayin shugaban PDM wanda kungiyar ce da ta kunshi dukkan mabiya da magoya bayan Marigayi Janar Shehu Yar'aduwa.

A zangon farko na wa'adin mulkin su da Shugaba Obasanjo Atiku Abubakar yayi bakin jini a jihohi da dama na arewa a inda ake ganin sa a matsayin wanda aka hada kai dashi domin dakusar da arewa . Akwai maganganu marasa dadin ji da dama da ake yawo dasu game dashi mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a arewacin Nijeriya wanda kila saboda kiyayya ko hassada ake yada maganganun domin a sake sashi yayi bakin jini musamman a gun talakawa .

Babbar dama da mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya samu domin wanke kansa da sake samun karbuwa da farin jini gun al'ummar Nijeriya shine rawar da ya taka a lokacin gwagwarmayan yakin tazarce . Ya shiga sahun gaba ya jagoranci rundunar da ta fafata da yan tazarce har suka murkushe ta . Wannan bajinta nasa yasa da dama a Nijeriya suka yafe masa laifuffukan da suke zargin sa da aikatawa musamman rawar da ake zaton ya taka a zaben 2003.

A kowacce jam'iyya Atiku Abubakar zai tsaya zabe ? Masu nazarin harkokin siyasa na ganin cewa jam'iyyar A.C tashi ce domin fitattun magoya bayan sa kamar su Alhaji Lawl Kaita da Cif Audu Ogbeh da Cif Yomi Edu da Uwargida Titi Ajanaku da Alhaji Ghali Umar Na'abba da sauran su su suka kafa jam'iyyar kuma kila karkashin ta zai tsaya takara. Biri dai yayi kama da mutum domin har yanzu jam'iyyar A.C bata da yan takarar shugaban kasa gashi kuma dab da zaben fidda gwani na jam'iyyar sa ta PDP dakatar dashi da akayi zai kare . An ya zai shiga ruguntsumin takarar fidda gwani a jam'iyyar PDP a kuraren lokaci har yayi wani tasiri?

In har da gaske Atiku Abubakar yake na gadar Shugaba Obasanjo to lallai yana shirin daukar dala ba gammo domin na farko Shugaba Obasanjo na yakar sa a siyasan ce inda a yanzu ake ganin cewa shi ya fito da Gwamna Umaru Musa Yar'aduwa takarar shugaban kasa a inda ta nan ya karya kungiyar su ta PDM wanda da ita Atiku Abubakar ke takama. Sauran matsalolin da zai fuskanta shine yawan yan takarar shugaban kasa daga arewa musamman Janar Muhammadu Buhari da Janar Ibrahim Babangida .Lallai zaben 2007 zata nuna cikin su uku waye yafi tasiri da karbuwa a Arewa domin duk wanda ya ja kaso mai yawa to ba shakka shi zai lashe zaben 2007 .

Yan siyasar a Nijeriya suna ganin Atiku Abubakar a matsayin dan siyasa mai tsari da iya kulle-kulle da mabiya a ko ina cikin kasar nan . Ko za suyi tasiri a zaben 2007? Ko Atiku Abubakar zai zama zakaran da Allah ya nufa da cara a zaben 2007 ?Ranar wanka dai ba'a boyen cibi.

Haza Wassalam

Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com

No comments:

Post a Comment