A kwana a tashi ranar 29 ga watan Mayu na wannan shekarar Shugaba Umaru Musa Yar’adua ya cika shekara daya bisa kujerar mulkin Nigeriya. Zaben daya dora shi bisa mulki ya sami suka daga kungiyoyin sa’ido na cikin gida da kasashen waje da jam’iyyun adawa saboda zargin an tafka magudi, wanda ya kaiga shigar da karairaki a gaban kotuna , inda a halin yanzu ana jiran kotun koli ta halasta ko kuma ta soke zaben nasa.
Ya kama aiki a wani yanayi na neman goyon bayan jama’ar kasa , ga kuma yajin aiki na gama gari da kungiyar kwadago ta kasa ta kira saboda neman ya warware wasu manufofin gwamnatin tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo na sayar da matatan man fetur na Kaduna da Fatakwal da Karin kudin man fetur da haraji. Bayan amsa kiran yan Nijeriya ta hanyar biyan bukatun kungiyar kwadago ta kasa ta data nema , ya dauki alkawarin inganta rayuwan yan Nijeriya ta hanyar aiwatar da kudirori guda bakwai.
Ginshikin mulkin Shugaba Yar’adua kamar yadda ya sha fada zai kafu ne bisa kudirori guda bakwai . Kudirorin sune bunkasa wutar lantarki da samar da tsaro da samun yawaitar arziki da samar da ingantattacen ilimi da kawo sauye-sauye a dokar filaye da kyakyawan tsarin sufuri da warware matsalar yakin Neja Dalta . Amma abin lura da tambaya shine ko Shugaba Yar’adua ya kama hanyar cimma burin sa na kudirorin guda bakwai ? Kuma cikin kudirorin guda bakwai wannene ya warware matsalar ? Sannan shin yana kan hanyar aiwatar da kudirorin guda bakwai? Kuma shin talakawan Nijeriya zasu shedi banbanci a gudanar da yanayin mulkin sa dana tsohon shugaban kasa Obasanjo?
A zancen gaskiya har yanzu yan Nijeriya basu fara amfana da kudirorin bakwai na shugaba Yar’adua ba. In mun dauki wutar lantarki, a kullum lamarin sai kara tabarbarewa yake tayi inda yanzu wutar da ake samu ya gaza awa biyar a rana. Kuma har yanzu yan Nijeriya na sa’ido domin ganin ya saka dokar tabaci a kan wutar lantarki kamar yadda yayi alkawari. Sannan in muka dauki fannin samar da tsaro har yanzu yan kasa na fuskantar barazanar masu aikata muggan laifuka. Kazalika matsalar yankin Neja Dalta na nan inda tsagerun matasa masu dauke da makamai nata cigaba da kawo cikas a harkokin hakan man fetur inda ake hako kasa da ganga miliyan 2 a rana maimakon ganga miliyan 2.4. Fatara da talauci da rashin aikin yi da kuma hauhawan farashin kayayyaki ya tasa talakawa a gaba duk da makudan kudade da gwamnatin ke samu .
Tun hawan sa bisa mulki masana harkokin siyasa ke zargin cewa Shugaba Yar’adua na mulki da sanyin jiki wanda ya janyo harkokin gudanar da mulkin kasa keta tafiyar hawainiya. Suna kuma ganin cewa har yanzu kamar ya kasa gano kan zaren matsalolin dake damun kasar , ga kuma ayi gaba ayi baya kan manufofin gwamnatin sa. Akwai masu ganin cewa mulkin sa cigaban mulkin tsohon shugaban kasa ne Cif Olusegun Obasanjo . Wannan shi yasa ma wasu suke ganin cewa babu wani cigaba da aka samu a shekara daya da yayi yana mulki.
Amma wani abin lura game da gwamnatin Shugaba Umaru Yar’adua shine na kokarin bin doka da oda, inda yake ta kokarin ganin cewa ana bin dokokin tsarin mulkin kasa da bin umarnin kotu sabanin gwamnatin da ta shude. A shekara daya na mulkin sa, Shugaba Yar’adua na bin hukuncin kotuna da suka yanke musamman gwamnonin jam’iyyar sa da kotuna suka soke zaben su, shima kansa yayi alkawarin cewa in kotun koli ta soke zaben sa zai sauka a take ya kuma mika mulki ga wanda kotu tace a mika masa mulki. Koda yake yan adawa na zargin cewa ta bayan gida ana tsoma baki a harkokin shari’a inda suke zargin sa hannun Uwargidan sa Hajiya Turai Yar’adua da hannu a shari’ar data tabbatar da kujerar gwamnan jihar Kebbi Alhaji Sa’idu Usman Nasamu Dakin Gari domin surikin sune. Duk da haka babu zargi kai tsaye na cewa shi Shugaba Yar’adua da kansa ne ya tsoma baki a batun shari’ar.
Kuma tun hawan sa mulki babu zargin cewa yana sama da fadi da dukiyar al’umma kamar a gwamnatocin baya. Sannan ba’a zargin sa da yada cin hanci da rashawa ko kuma bada cin hanci ga yan majalisun kasa dan cimma manufofin sa. Haka kuma ba’a zargin sa da dakile ko kuma kawo cikas ga aiyukan majalisun tarrayya da kawo cikas a aiyukan sashin shari’a.
Yan Nijeriya nada bukatar ganin cewa gwamnatin Shugaba Yar’adua na gudanar da aiyuka na zahiri da zai inganta rayuwar su, kamar samar masu da aiyukan yi da gaggauta kawo karshen matsalar wutan lantarki da rashin sa ke kawo cibaya ga bunkasar tattalin arzikin su da bunkasa aikin gona ko kuma a takaice ya aiwatar da kudirorin sa guda bakwai kamar yadda yayi masu alkawari. Sannan kuma a aikace ya tabbatar da ana zabe na gaskiya kamar yadda yayi alkawari domin baiwa yan kasa kwarin gwiwa kan cewa lallai Nijeriya na bin tsarin dimokaradiya.
Har yanzu mafi yawan yan Nijeriya nayi wa Shugaba Umaru Yar’adua kyakkyawan zato na cewa kila abinda kesa yake jan kafa wajen gudanar da mulkin sa shine na karar dake gaban kotun koli . Ya wajaba a gare shi ya kasance tare da yan Nijeriya ba wai wani ko wasu mutane ba saboda sun tsaya masa ya zama shugaban kasan Nijeriya ba. Lokaci dai baya jira a inda a yanzu har ya shafe shekara daya yana mulki.
Inda za’a gudanar da kuri’ar jin ra’ayin mutanen Nijeriya da mafi yawan su zasu ce su har yanzu basu gani a kasa ba. Rayuwar su babu banbanci da shekaru takwas da Obasanjo yayi yana mulki, kuma sun fara fidda rai kan cewa mulkin Shugaba Yar’adua zai kawo canji a rayuwar su. A watanni masu zuwa yan Nijeriya zasu iya tabbatar da cewa zasu sami canjin da suke tsammani ko kuma cigaba da rayuwa kamar yanda suka shafe shekaru takwas na mulkin Obasanjo cikin matsi da kuncin rayuwa duk da arzikin da kasar ke samu albarkacin hauhawan farashin man fetur a kasuwan duniya.
Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com
Thursday, 29 May 2008
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment