Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo a yan kwanakin nan na fuskantar tonon silili da suka iri-iri, tare da kiran da ake tayi na a bincike shi kan yadda ya tafi da kasar a shekaru takwas da yayi yana mulki . Ya kuma kasance tsohon shugaban kasa mafi bakin jini saboda yanda babu kakkautawa ya rika gallazawa yan Nijeriya har zuwa karshen mulkin sa inda ya kara kudin man fetur da haraji bayan shugabantar zabe mafi muni a tarihin zabubbuka a duniya.
Cikin wadanda babu zato babu tsammani suka soki yanda Cif Obasanjo ya tafi da kasar shine mutumin da yaci gajiyar magudin zaben da Obasabjo ya tafka , wato Shugaban Kasa Umaru Musa Yar'adua. Ya zargi gwamnatin Obasanjo da barnata kudi dala biliyan goma kan wutar lantarki amma babu wutar! Koda yake shugaban majalisar wakilai Dimeji Bankole yace kudin dala biliyan sha-shida ne! Haka nan a kullum sai tono abubuwan son zuciya da Obasanjo yayi ake tayi , kamar baiwa kansa lasisin mallakar gidajen rediyo da talebijin da yayi ana sauran yan'kwanaki ya bar mulki. Da gano wasu asusun boye har guda goma sha shida da biliyoyin nairori a dankare.
Mafi muni cikin abubuwan dake ta faruwa game da Obasanjo bayan ya bar mulki shine na zargin da dan'sa na cikin sa Gbenga Obasanjo yake yiwa mahaifin sa cewa yana lalata da matar sa yana bata kwangiloli. Gashi kuma babbar yar'sa Sanata Iyabo Obasanjo-Bello ita ma ana zargin ta da laifin damfara , inda ake zargin cewa ta damfari wani kamfanin kasar Austria mai suna M.Scheider GMBH &Co kudi har naira biliyan uku da rabi ,inda tayi amfani da sunan Uwargida Damilola Akinlawon.
Kafin Cif Obasanjo ya dawo bisa karagar mulki a shekarar 1999,yana cikin mutanen da ake gani da girma da kima a nahiyar Afrika da kasashen duniya.Ya kuma sami girman ne saboda yanda ya mika wa farin hula mulki a shekarar 1979. Sai aka wayi gari Obasanjo ya zubar da mutumcin sa da girman sa a cikin gida Nijeriya da kasashen duniya tun lokacin daya tafka magudin zabe a shekarar 2003, Sannan yaso a canza kundin tsarin mulkin kasan nan domin ya sami wa'adi karo na uku. Yan kasa masu kishi suka tarwatsa mumunan burin na Obasanjo na kasancewa a bisa mulki har mutuwan sa. Abunda ya faru bai ishe shi ishara ba , yayi wani yunkuri na wanke sunan sa , sai gashi bisa taimakon Farfesa Maurice Iwu sun gudanar da zaben da su uku kadai suka yi imanin an gudanar da zabe na gaskiya wato shi kansa Cif Obasanjo da Farfesa Maurice Iwu da Malam Buhari Daure !
A lokacin mulkin Obasanjo yayi ta sayar da kaddarori da kamfanoni da masana'antun gwamnati da zimmar bunkasa yanda suke tafi da al'amurran su, amma sai aka wayi gari yan kasa na zargin cewa an saida wadannan kayayyakin na kasa bisa farashin da bai kai darajar su ba. Sai kuma gashi a kwananan ana neman naira biliyan 146 na kudaden domin basu shiga asusun tarayya na kasa ba. Kazalika majalisar tarayya ta soke wasu daga cikin cinikayyan saboda basa bisa doka.
Yan Nijeriya da dama nata fitowa suna kira ga gwamnatin Umaru Yar'adua data binciki yanda tsohon shugaban kasa Cif Obasanjo ya tafi da kasar nan a shekaru takwas da yayi yana mulki.Kungiyoyi kamar su Afenifere da kungiyar Kiristoci ta kasa da kungiyar hadin gwiwan jam'iyyun adawa da manyan yan siyasa da talakawan kasa nata kira kan lallai Obasanjo nada bayanen da zaiyi wa yan kasa bisa zargin da ake tayi masa na halin fataken dare.
Ko a jam'iyyar sa ta PDP inda yake rike da kujerar shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar wato BOT,yana fama da suka da adawa inda wasu manyan yan jam'iyyar ta PDP ke neman yayi murabus. Cif Solomon Lar da Alhaji Abubakar Rimi na ganin cewa zargin abin kunya na lalata da matan dan'sa kadai ya isa hujja Obasanjo yayi murabus. Shi kuma tsohon shugaban majalisar dattijai Sanata Ken Nnamani na ganin cewa kujerar da Obasanjo ke kai na shugaban kwamitin amintattu kujerace ta Arewacin Nijeriya. Sannan shi da tawagar sa ta G21 na neman jam'iyyar ta koma kan kundin tsarin mulkin ta na shekarar 1998, wato a fakaice suna son a datse fukafukan Obasanjo a jam'iyyar .
Kuma da lamu yan siyasar Nijeriya na neman maida Obasanjo saniyar ware domin a yau duk tonon sililin da Obasanjo ke fuskanta daga cikin gidan sa zuwa kasa gabaki daya babu mai fitowa ya kare shi. Yau yan gani kashenin Obasanjo irin su Sanata Nasiru Mantu da Malam Nasiru el-Rufa'i da Cif Femi-Fani Kayode da Malam Nuhu Ribadu da Gwamna Sule Lamido da sauran su , babu wanda ya fito dan kare mutumci da martaban Obasanjo kamar yadda aka san su a baya suna yi.
Sannan Obasanjo ya zama saniyar ware a siyasar kasashen duniya da nahiyar Afrika saboda yanda ya gudanar da zaben 2007 a Nijeriya. A yau Mista Kofi Annan duk da cewa bai taba zama shugaban kasa a wata kasa ta Afrika ba ,bayan Mista Nelson Mandela babu wani dan nahiyar Afrika mai martaba da kiman sa domin ko rikicin magudin zabe dake faruwa a kasar Kenya shi ke kaiwa da komowa dan samin zaman lafiya a kasar.Girma da martaban da Obasanjo zai samu a Afika da duniya da suna dayawa daya kare mutumcin sa , amma sai gashi yayi karkon kifi daga shahararre a siyasar duniya da Afrika zuwa almajirin Lamidi Adedibu a fagen siyasa da siyasar yankin yarbaawa.
Yau kusan shekara guda kenn da Umaru Yar'adua yake bisa mulki amma ga dukkan alamu yanda Obasanjo ya kudundune kasar ya mika masa ya kasa gano zaren matsalolin dake damun kasar .Har yau babu wani cigaba da aka samu daya wuce soke ko kuma aiwatar da wasu manufofin gwamnatin Obasanjo. Rashin aikin yi da talauci da rashin tsaro da hauhawan farashin kayayyaki da sauran su sai karuwa suke tayi inda rayuwan talaka sai kara munana yake tayi.
Ko Shugaba Yar'adua zai amsa kiraye-kirayen da ake tayi masa na binciken gwamnatin Obasanjo? Haka ma suma majalisun tarayya shin zasu iya tuhuman Cif Obasanjo kamar yadda suke ta tada kuran zasu yi?Hadin gwiwan jam'iyyun adawa shin zasu iya tursasa gwamnatin Yar'adua ta binciki Obasanjo?
Ta bangaren yan Nijeriya suna da bukatar sanin yanda aka gudanar da dukiyar su a lokacin mulkin Obasanjo. Suna fatan cewa Shugaba Yar'adua zai nuna wa duniya cewa shi ba dan amshin shatar Cif Obasanjo bane ta hanyar kafa kwamitin bincike kan yadda Obasanjo ya tafi da arzikin kasar nan, in kuma aka same shi da laifi to lallai a hukumta shi,yin haka zai sa jama'ar kasa suyi ma Yar'adua kyakyawan zato. Tsakani Obasanjo da yan Nijeriya sai muce rana dai bata karya sai dai uwar ya taji kunya.
Hazawassalam
Shehu Mustapha Chaji
shehuchaji@yahoo.com
Sunday, 10 February 2008
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
is your blog only for Hausa speakers?
ReplyDelete